Da gaske babu giɓin shugabanci a Najeriya duk da bulaguron Tinubu da Shettima?

Tinubu da Shettima

Asalin hoton, Social Media

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Bulaguron da shugaban Najeriya da mataimakinsa suka yi zuwa ƙasashen waje na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar, inda mutane da dama ke ganin cewa an bar su babu shugabanci.

Shugaba Tinubu dai ya fice daga Najeriya ne a ranar 3 ga watan Octoban da muke cikin domin tafiya hutun mako biyu da ya tsara gudanarwa a Birtaniya. To amma daga baya fadar shugaban ƙasar ta ce ya tafi birnin Paris na ƙasar Faransa domin halartar wasu al’aumara da ba ta bayyana ba.

Shi kuwa mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima a ranar Laraba ya yi tafiya zuwa ƙasar Sweden domin halartar wasu tarukan ƙulla alaƙar ci gaban kasuwaci da wasu yarjejeniyoyi a tsakanin ƙasashen biyu.

Bulaguron jagororin biyu ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin ƴan ƙasar, inda wasu ke ganin bai kamata su bar ƙasar su biyu duka a lokaci guda ba.

To sai dai fadar shugaban ƙasar ta ce babu wani giɓi da tafiyar shugaban da mataimakinsa suka haifar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugababn ƙasar Bayo Onanuga ya fitar ranar Laraba, ya ce bulaguron shugabannin biyu ba ta haifar da wani giɓin shugabanci ba kasancewar akwai shugaban majalisar dattawa da sakataren gwamnatin tarayya, da sauran ministoci, kuma kowa na gudanar da aikinsa.

'Shugabanci ba gadi ba ne da za a ce koyaushe sai mutum yana nan'

Malam Abdulaziz Abdulaziz, ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban ƙasar ya shaida wa BBC cewa bulaguron jagororin ƙasar biyu ba wata matsala ba ce.

''Shi fa shugabanci ba gadi ba ne da za a ce koyaushe sai mutum yana nan, babban abin da ake buƙata shi ne jan ragama da jagoranci da kuma ɗaukar matakan da suka dace na shugabanci da ke tasowa daga lokaci zuwa lokaci'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa wannan kuwa shugaban ko mataimakinsa za su iya yinsa ba tare da suna zaune a ofishinsu ba.

Ya kuma ce dama ita gwamnati tana da muƙarrabai da suke gudanar da al'amuranta na yau da kullum.

''Shi shugaba daga duk inda yake zai iya bayar da umarni ko doka kuma su waɗannan muƙarraban su aiwatar da ita, ba sai lallai shugaban na cikin ƙasar ba'', kamar yadda Abdulaziz Abdulaziz ya bayyana.

Ya ƙara da cewa daga cikin muƙarraban gwamnatin da ke aiwatar da al'umuran gwamnati na yau da kullum akwai sakataren gwamnati da shugabar ma'aikatan fadar gwammnati da shugabannin ma'aikatu da sauran manyan sakatarori.

''Kuma da ma yawanci su waɗannan su ke aiwatar da al'amuran gwamnati ko da shugabvan ƙasar yana cikin ƙasar'', in ji shi.

Wannan ne farko da Tinubu da Shettima suka yi bulaguro lokaci guda?

Lokaci na farko da shugaban ƙasa da mataimakinsa suka fice daga Najeriya a lokaci guda shi ne a farkon watan Mayun 2024, lokacin da Shugaba Tinubu ya halarci taron musamman kan kasuwanci da aka gudanar a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

Kafin komawar Tinubu ƙasar ne kuma mataimakinsa, Kashim Shettima ya yi bulaguro zuwa ƙasar Amurka domin halartar taron kasuwanci tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka.

Me ake nufi da giɓin shugabanci (Leadership vacuum)?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barista Alƙali Sidi Bello, shugaban ofishin lauyoyi na 'Sidi Bello And Co' da ke Sokoto, ya ce abin da ake nufi da giɓin shugabanci, shi ne a samu yanayin da shugaba ko mai riƙe da madafun iko ya rasu ko ya kasance cikin wani yanayi ko rashin lafiyar da ba zai iya gudanar da aikinsa ba.

Ya ci gaba da cewa idan shugaba ko mai riƙe da madafar iko ba ya nan, ya yi tafiya hutu ko wani aiki a wajen ƙasa, to wannan ba giɓin shugabanci ba ne, ''Sai dai a ce shugaba ba ya nan''.

''Don haka ne ma doka ta yi tanadin cewa idan shugaban ƙasa zai tafi hutun da ya kai aƙalla mako biyu, to zai miƙa ragamar jagorancin ƙasa ga mataimakinsa, don haka ne ma ake kiransa da muƙaddashin shugaban ƙasa'', in ji lauyan.

''Don haka abin da ke faruwa yanzu a Najeriya ba giɓin shugabanci ba ne, sai da mu ce shugaban ƙasa da mataimakisa duka ba sa ƙasa'', in ji Barista Sidi Bello.

Ya ce a irin wannan yanayi duk abin da muƙaddashin ya zartar ana kallonsa a matsayin hukuncin shugaban ƙasa, ba na mataimaki ba.

'Abubuwan da Tinubu da Shettima ne kawai za su iya yinsu'

Saɓanin abin da fadar shugaban ƙasar ta bayyana da cewa akwai wasu ƙusoshin gwamnatin da ke gudanar da al'amuran yau da kullum, Barista Sidi Bello ya ce akwai wasu batutuwan da shugaban ƙasa ne kawai ko mataimakinsa za su iya gudanar da su idan buƙatarsu ta taso.

''Kamar jagorantar majalisar zastarwar ƙasa, da majalisar tsaron ƙasa, shugaban ƙasa ko mataimakinsa ne kawai za su iya jagorantar waɗannan majalisu'', in ji lauyan.

Ya ce sakataren gwamnati ko wani minista ba shi da hurumin da zai jagorancin waɗannan majalisu biyu.

Amma ga haka lauyan ya ce ministoci da sakataren gwamnati za su iya jagorantar sauran ayyukan gwamnati ko da kuwa shugaban ƙasa ko mataimakinsa ba sa nan.