Yadda ƴan majalisar Kenya suka kaɗa kuri'ar tsige mataimakin shugaban ƙasa

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Wycliffe Muia
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi
- Marubuci, Will Ross
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa regional editor
- Lokacin karatu: Minti 3
Ƴan majalisar Kenya sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da tsige mataimakin shugaban ƙasar bisa zarge-zargen rashawa da cin hanci.
Ƴan majalisar sun kuma zargi mista Rigathi Gachagua da yin siyasar ƙabilaci da kuma yi wa gwamnati zagon ƙasa.
A ranar Talata ne dai kakakin majalisar Moses Wetangula ya sanar da cewa ƴan majalisar 281 sun amince da ƙudirin tsige mataimakin shugaban mai ɗauke da tuhuma guda 11, inda kuma ƴan majalisar 44 suka ƙi amince wa da ƙudirin sannan mutum ɗaya ya kasance ɗan baruwanmu.
Yanzu abin da hakan yake nufi shi ne mista Gachagua ya zama mataimakin shugaban ƙasar na farko da majalisar wakilan ta tsige duk da cewa majalisar dattawa za ta fitar da matsayar ko ya tsigu ko kuma a a.
Ana dai tuhumar sa da mallakar kadarori ba bisa ƙa'ida ba. Mataimakain shugaban ƙasar wanda attajirin ɗan kasuwa ne, ya ce mafi yawancin gidanjensa da filaye mallakar ɗan uwansa ne wanda ya rasu.
Sai dai kuma ƴan majalisar Kenyan da dama sun yi maganganun da suka zubar masa da ƙima - inda suka nuna a fili cewa suna tare da shugaba Ruto.

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin shugaban na Kenya mai shekaru 59 wanda aka fi sani da "Riggy G" ya bayyana zarge-zargen da "na bazata" sannan kuma "na ɓata suna".
Tun dai watan Yuni ne rikicin siyasar ke ruruwa tsakanin shugaba Ruto da mataimakin nasa bayan zanga-zangar da ta ɓarke a ƙasar kan haraji.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ruto ya kori mafi yawancin ƴan majalisarsa sannan ya kawo ƴan jam'iyyar adawa cikin gwamnatin tun bayan zanga-zangar.
Ƴansanda sun gayyaci ƴan majalisar dokoki da dama da ke biyayya ga mataimakin shugaban a watan da ya gabata - duk da cewa ba a tuhume su da laifin komai ba.
Kafin dai a fara kaɗa ƙuri'ar neman amincewar tsige mataimakin shugaban, an tsaurara tsaro a Nairobi, babban birnin na Kenya, inda ƴansanda suka rinƙa sinitiri a kan manyan titunan da ke tafiya zuwa majalisar dokoki.
Kafafen watsa labaran cikin gida na Kenya sun rawaito cewa an ɗauki lauyoyi kimanin 20 domin daƙile ƙuri'ar da majalisar za ta kaɗa ta tsige mr Gachagua.
Ƴan majalisar 281 ne suka rattaɓa hannu kan ƙudirin tsegewar, fiye da mutum 117 da tsarin dokar ƙasar ya tanada domin tabbatar da tsigewar a makon da ya gabata.
Gachagua dai ya gaza samun nasarar daƙile ƙudirin a kotuna da dama.
Yayin wani jawabi a gidan talbijin ranar Litinin, Gachagua ya soki Mwengi mutuse, wani ɗan majalisa wanda shi ne ya rubuta kudurin, inda ya bayyana abin da ya yi da "abin kunya da son tayar da hankali."
ƙudurin dai ya lissafa wasu tuhume-tuhume guda 11 da ya ce ya kamata a tsige mataimakin shugaban da suka haɗa da zargin cewa Gachagua ya tara dukiya da kadarori da suka kai ƙimar shilling biliyan 5.2 kwatankwacin dala miliyan 31 a shekaru biyu ta hanyar da ba a sani ba.
"Ni ban aikata dukkan waɗannan tuhume-tuhumen ba," in ji Gachagua.
"Ba ni da niyyar yin murabus daga aikin nan. Zan bi haƙƙina har zuwa ƙarshe."
Ya kuma ƙara haske dangane da batun yi wa gidansa da gwamnati ta ba shi kwaskwarima.
Bisa ƙa'ida dai duk wani babban batu da za a yanke irin wannan, tsarin ƙasa ya ce sai an tuntuɓi al'umma ƙasa kafin aiwatar da shi.
Wani rahoto daga majalisar dokokin ƙasar dai ya nuna cewa an tuntuɓi ƴan ƙasar kuma fiye da mutane 200,000 ne suka bayar da martaninsu, inda kuma kaso 65 suka goyi bayan tsige mista Gachagua sannan kaso 34 suka soki ƙudirin.
A ranar Lahadi ne Gachagua ya roƙi Ruta da ƴan majalisar to yi masa gafara dangane da duk wani laifin da ya yi a zamanin mulkinsa. Daga baya kuma ya yi ƙarin haske kan neman afuwar da ya yi cewa ba wai ya amsa laifinsa ba ne.
Har yanzu dai shugaba Ruto bai ce uffan ba kan al'amarin duk da dai an san matsayarsa tun ma farkon shekarun yaƙin neman zaɓe yana cewa ba zai taɓa tsinka mutumcin mataimakinsa ba a fili.











