Fadar shugaban Najeriya ta nesanta kanta daga allunan yaƙin neman zaɓen 2027

Tinubu

Asalin hoton, Bayo Onanuga/Facebook

Lokacin karatu: Minti 2

Fadar gwamnatin Najeriya ta nesanta kanta daga allunan da ake yaɗawa a wasu biranen ƙasar na neman sake zaɓen Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a shekarar 2027.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce ba su da hannu a fitar da allunan, domin a cewarsa lokaci bai yi ba.

"Fadar shugaban ƙasar tana takaicin yadda ake ta yaɗa allunan neman zake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima na zaɓen 2027 musamman a titunan Abuja da Kano."

Sanarwar ta ce duk da cewa Tinubu da Shettima suna godiya da ƙaunar da magoya bayansu suke nuna musu a faɗin ƙasar, amma "ba sa tare da duk wani yaƙin zaɓe da ya saɓa doka. Dokokin zaɓen Najeriya ba su amince a fara yaƙin zaɓen 2027 tun a yanzu ba. Fara yaƙin zaɓe tun a yanzu zai yin naƙasu ga sahihancin zaɓen," kamar yadda sanarwar ta nuna.

Ya ƙara da cewa Tinubu da Shettima mutane ne masu amfani da doka da oda, wanda a cewarsa hakan ne ma ya sa ba za su aminta da duk wani mataki da zai zubar da ƙimar hukumomin ƙasar, da ɓata tsarin zaɓe ba.

Ya kuma yi kira ga waɗanda suke yaɗa allunan da masu ɗaukar nauyinsu da dakata, inda ya ce a jira lokacin da Hukumar INEC za ta fitar da jadawain zaɓe, "amma kafin nan shugaban ƙasa da mataimakinsa ba su ba kowa izinin fara yaɗa allunan neman zabensu na 2027 ta kowace kafa ba."

A ƙarshe sanarwar ta ce Tinubu da mataimakinsa sun fi mayar da hankali ne kan sauke da ke kansu na ciyar da Najeriya gaba, wanda sanarwar ta ce an fara "samun nasarori wajen inganta tattalin arzikin ƙasar da samar da ababen more rayuwa da inganta jin daɗi da walwalar ƴan ƙasar."

Sai dai ya ce da zarar INEC ta sanar da lokacin fara shirye-shiryen zaben, Tinubu zai sanar da ƴan Najeriya tsare-tsarensa.

Yanzu dai Bola Tinubu na gab ne da cika shekara biyu a wa'adinsa na farko na mulkin ƙasar, wanda ya fara bayan ya lashe babban zaɓen ƙasar na shekarar 2023.

Sai dai kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi damar sake tsayawa takara a zaɓen da za a yi a shekarar 2027 domin shugabantar ƙasar a wa'adi na biyu.