Shin dokar samar da daidaito tsakanin ƙabilun Najeriya na fuskantar barazana?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
Wasu 'yan Najeriya na nuna damuwa game da yadda shugaban ƙasar ke ƙin martaba ƙabilun ƙasar daban-daban wajen raba muƙaman gwamnati.
Da jimawa dai aka wargaza tsarin zamantakewar al'ummun Najeriya mafi ɗimbin jama'a a Afirka.
Yayin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba kowane yanki sararin a dama da shi wajen rabon manyan mukaman gwamnati, wanda hakan shi ne abin da aka sani tun asali domin ƙara samar da haɗin kan ƙasa.
A yanzu dai ana ci gaba da samun damuwar yadda ba bin hakan, har ma akwai masu sukar yadda gwamnatin shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da ke cika shekaru biyu akan mulki - da fifita 'yan ƙabilarsa ta Yarbawa wajen rabon muƙamai.
Fadar shugaban ƙasar ta musanta wannan zargi da ƙaƙƙarfar murya.
An daɗe ana fargabar cewa 'yan wasu ƙabila za su yi baba-kere wajen mamaye manyan muƙaman wannan gwamnatin, wanda hakan ke nufin ana bibiye da dukan muƙaman da shugaban ƙasar ya bayar da zarar an bayar da sanarwar hakan.
Najeriya na da fiye da ƙabilu 250 da suka haɗa da Hausawa da Fulani da Yarbawa da Ibo - da ke zaune shiyoyin arewa da kudu maso gabas da kudu maso yamma - waɗanda kuma su ne manyan ƙabilun da ƙasar uku.
Masu sharhi na cewa shugaba Tinubu wanda musulmi ne daga yankin kudancin ƙasar, ya kauce hanya wajen zaɓar mataimakinsa a zaɓen da ya gabata, wanda addininsu ɗaya (duk da yake ya fito daga arewa).
Tun bayan komawa tsarin mulkin dimukuraɗiyya a 1999, manyan jam'iyyu na da tsarin haɗa shugaba da mataimakinsa musulmi da kirista a matsayin 'yan takara, saboda ƙasar ta riga ta rarrabu a bisa a dalilan bambancin addinan guda biyu da ake da su.
Sai dai gwamnatinTinubu ce ta fi jan hankali mutane kan haka daga tun lokacin da ya zama shugaban ƙasa a watan Mayun 2023.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk ana da gurabun muƙamai da da dama da shugaban ƙasa zai iya cikewa, amma a cewar barista Lawal Lawal akwai manyan ayukka takwas da ke da "matuƙar muhimman ga kowace gwamnati".
Waɗannan muƙaman su ne:
- Babban Banki
- Kamfanin Man fetur na ƙasa, NNPC
- Rundunar 'Yan sanda
- Rundunar Sojoji
- Hukumar Yaƙi Da Fasa Ƙwauri
- Hukumar Tattara Bayanan Sirri
- Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa, da
- Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga
Babu dai wata doka a kundin tsarin mulkin ƙasar da ta tsara raba mukamai, amma waɗannan gurabu su ne muhimmai a ɓangarorin kuɗi da tsaron ƙasar.
Kowane shugaban ƙasa kan gaji wasu muƙamai da shugaban da ya gabace shi ya tsara, amma dai shi ne mai wukasa da nama wajen maye gurbinsu.
Daga watan Afirilu, shugaba Tinubu ya naɗa 'yan ƙabilarsa na Yarbawa ne akan duka waɗannan muƙamman takwas.
Na baya-bayan nan shi ne naɗa tsohon shugaban kamfanin Shell Bayo Ojulari ya jagoranci kamfanin haƙar mai na NNPC wanda ya maye gurbin ɗan arewa, ya haifar da muhawarar cewa a zahiri ana fifita wata ƙabila ne wajen raba muhimman muƙaman a ƙasar.
Kuma ana ganin cewa shugabannin ƙasa biyu da Tinubu ya gada ba su yi irin wannan rabonna kura baa lokacin da suke mulki.
Tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan - wanda ya yi shugabanci daga 2010 zuwa 2015 - ya yi nuna daidaito wajen bayar da muƙaman inda ya ba Fulani biyu, Hausawa sun samu biyu, kabilat Atyab sun samu ɗaya, Ibo sun samu ɗaya Yarbawa ɗaya sai kuma muƙami guda da ya fito daga ƙabilar Kalaba.
Hka shi ma Muhammadu Buhari - da ya zama shugaban ƙasa daga 2015 zuwa 2023, ba a samu irin haka ba.
Ya ba Hausawa manyan muƙamai uku, Kanuri muƙamai biyu da ƙabilar Ibo muƙami ɗaya sai Yarbawa masu ɗaya yayin da aka ba ƙabilar Nufawa muƙami ɗaya.
Amma a tunanin 'yan Najeriya da dama, Hausawa da Kanuri da Nufawa ana ganin dukan su a matsayin 'yan arewa, inda nan ma akwai masu zargin a lokacin gwamnatin Buhari an ɗan nuna irin wannan alfarma, saboda shi kansa daga shiyar ta arewa ya fito.
Wasu na cewa gwamnatin Tinubu ta ɗora ne bisa ga abin da ya tarar, amma dai yadda Yarbawa suka yi kane-kane ɗari bisa ɗari, ga waɗannan manyan muƙamai guda takwas abu ne da ba a saba gani ba.
Masani tarihi a Najeriya, Farfesa Tijjani Naniya ya shaidawa BBC cewa, " A tsarin gwamnatin shugaban ƙasa da aka zaɓa ta hanyar dimukuraɗiyya, ba zan taɓa iya tuna a tarihin Najeriya inda aka samu 'yan ƙabila daya sun mamaye manyan muƙamai ba kamar wannan gwamnati".
Farfesan ya ce illar hakan ta fi shafar makomar haɗin kan ƙasar fiye da abubuwan da suka faru a can baya.
"A ganina, fargabar ita ce kada wani shugaba na gaba ya ce shi ma zai bi irin wannan tsri ya ɗaquki muƙamai masu muhimmanci ya ba 'yan ƙabilarsa, inda hakan kan dusashe fatan da sauran al'umar ƙasar ke da na ganin an dama da su, kuma zai rage karsashin son mulkin dimukuraɗiyya," in ji shi.
Shekaru biyu da suka gabata, wasu 'yan arewa, waɗanda galibinsu Hausawa da Fulanin ne, sun yi wa wannan tsari kallon wanda ba za ta saɓu ba.
Waɗannan mukaman na maza (da babu mace ko ɗaya) a shugabancin NNPC da 'yan sanda da Kastam da Hukumur yaƙi da cin hanci duk an maye gurbin 'yan arewa ne.
Bayan an cire Abdulrasheed Bawa, wanda Bahaushe ne a matsayin shugaban EFCC a shekarar 2023 shekaru biyu kawai bayan naɗa shi akan muƙamin abu ne da ya jima yana daure kan jama'a.
Wasu daga yankin na arewa na da ra'ayin cewa ba a yi wa Bawa adalci ba, kawai mataki ne da aka ɗauka domin sharewa Misata Olukoyode hanya.
"Akwai buƙatar shugaban ƙasa fa ya san da cewa Yarbawa mutane ne daga wani ɓangare na kasa, kuma ya kamata a raba dukan muƙamai ga dukan kabilun sassan ƙasar," kamar yadda Isah Habibu wani mai sharhi akan lamurran yau da kullum a Najeriya ya sanar da BBC.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Mai ba shugaban Najeriya shawara kan kafafen watsa labari Sunday Dare ya yi ƙoƙarin bayanin cewa Tinubu ya ba 'yan arewa 71 da 'yan kudu 63 mukamai sai dai sai ya goge bayanin wanda ya wallafa a ranar 9 ga watan Afirilun a shafinsa na X bayan ya fafata da ɗimbin jama'a da suka nuna kurakurai a cikin maganarsa.
Ya kuma yi alƙalin sabunta jerin sunayen amma har kawo yanzu fiye da sati shida bai sake wallafa kome ba.
Tinubu na fuskantar suka daga 'yan ƙasarsa
Sanata Ali Ndume wanda ya fito faga arewa - shi ma dai kamar Tinubu - jam'iyarsu ɗaya ta APC. A wata hira da ya yi da wani gidan talabijin ya ce ya fito ne a sarari don ya sanar da muƙaman da Tinubu ya naɗa "na ba daidai ba".
Ndume ya ya kaɗu da ya ji haka, inda ya kwatanta su da "na wariya da ba su tafi daidai da ajandar shugaban ƙasar ta sabuwar fatar tafiya da kowa ta 'Renewed Hope' .
Wani mai ba shugaban kasar shawara Daiel Bwala, ya yi musun hakan, inda ya ce wasu muƙaman ai sun ɗara wasu muhimmanci.
"Abin da na sani shugaban ƙasa ya kiyaye dokokin kundin tsarin mulki [da suka shafi raba muƙamai] ga jama'a - babu wani sashe a kundin tsarin mulkin [ina yake] da aka bayyana manya biyar ko manyan mukamai 10 da sauran su," ya Shaidawa BBC.
Mai ba shugaban kasa shawara akan lamaurran tsaro ya fitao ne daga yankin arewa maso gabasa, babban hafan tsaro ya fito ne daga arewa maso yamma sai kuma sakataren gwamnatin tarayya da ya fito daga arewa ta tsakiya."
Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda ke bayyana manufofin fadar shugaban ƙasa ya fitar da wani bayani a ranar 12 ga watan Afirilu cewa Tinubu na kwatanta gaskiya a cikin wannan rabon muƙaman.
A cewar sa, "Wannan gwamnati na kokarin tabbatar da kowane yanki na ƙasar ya samu wakilci a dukan hukumomi da sasan gwamnati".
Lawal wanda masanin lamurran siyasa ne ya ce ya kamata shugaban kasa ya naɗa mutumin da ya fi cancanta ne kawai ba tare da la'akari da ƙabila ko yankin da ya fito ba - inda ya ce hakan shi ne abin da Tinubu ke yi a yanzu.
"A Najeriya an kai matsayin da ya kamata a ce an wuce irin wannan yanayi na magana akan kabilanci," in ji shi.
Ana iya samun lokacin da 'yan Najeriya za su gaji da batutuwan da suka shafi asalin ƙabilar waɗanda ke riƙe da madafun iko. Amma a cewamasani tarihi a Najeriya Farfesa Naniya, wannan wani dogon batu da ba na yanzu ba.
Ya yi imanin cewa hakan na iya faruwa ne kawai idan aka samu aƙalla shugabannin ƙasa har huɗu a jere da da suka samar da daidaito a rabon muƙamai da ayukan raya ƙasa.
"Ina jin kome na iya faruwa amma hakan na buƙatar shuagabanni na gari".











