Liverpool na zawarcin Isak,Wolves na son Jota, Man U ta kara farashin Rashford

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta tuntubi makusantan dan wasa mai kai hari na Newcastle da Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, kafin komawarsa a lokacin bazara. (Fabrizio Romano)
Manchester United ta kara farashin da ta nema kan dan wasa mai kai farmaki, Marcus Rashford mai shekara 27, wanda aka bayar da shi aro ga Aston Villa wanda wannan ne ya sa Ingila ta yi masa kiranye . (Football Insider), external
Wolves na bibiyar halin da Diogo Jota ke ciki a Liverpool kuma sun fara kokarin ganin cewa dan wasan gaban Portugal mai shekara 28 ya koma Molineux wannan bazara. (Teamtalk), external
Ita ma Manchester United na sa ido kan dan wasan gaba na Eintracht Frankfurt da Faransa Hugo Ekitike mai shekara 22, da kuma dan wasan gaba na RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko mai shekara 21. (Florian Plettenberg), external
Bournemouth na da kwarin gwiwar yin nasara a kan golan Jamhuriyar Ireland Caoimhin Kelleher, mai shekara 26, daga Liverpool a bazarar nan. (Sun), external
AC Milan za ta dauko dan wasan bayan Manchester City da Ingila Kyle Walker, mai shekara 34, a bazara, amma ba za ta nemi ci gaba da rike dan wasan Portugal Joao Felix, mai shekara 25, aro daga Chelsea ba. (Gazzetta dello Sport - in Italian), external
Liverpool na shirin kashe sama da fam miliyan 250 a wannan bazarar don siyan dan wasan gaban Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, mai shekara 25, da dan wasa tsakiya na RB Leipzig da Netherlands Xavi Simons, mai shekara 21, da dan wasan bayan Inter Milan da Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 25. . (Fichajes - in Spanish), external
Liverpool na daya daga cikin kungiyoyin da ke sanya ido kan dan wasan baya na Bayer Leverkusen Jeremie Frimpong, yayin da suke ganin dan wasan baya na Netherlands mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin Trent Alexander-Arnold. (Caught Offside), external
Tsohon dan wasan tsakiya na Manchester City Kalvin Phillips, mai shekara 29, yana neman komawa Leeds United bayan da aka bada shi aro ga Ipswich Town a kakar wasa ta bana.(Football Insider), external
Watakila Aston Villa ta siyar da dan wasan tsakiyar Argentina Enzo Barrenechea, mai shekara 23, ga Valencia a bazara sakamakon tagomashin da ta samu bayan ta bada shi aro ga kulob din na Sfaniya,(Athletic - subscription required), external
Manchester City da Liverpool da Chelsea da kuma Arsenal na zawarcin dan wasa gefe na River Plate mai shekara 17, Franco Mastantuono wanda kungiyar za ta iya sakinsa akan fam miliyan 35m. (Teamtalk), external
Tottenham ta bayyana kocin Fulham Marco Silva da kocin Bournemouth Andoni Iraola a matsayin wadanda take zawarcinsu domin maye gurbin Ange Postecoglou. (Telegraph - subscription required), external











