'Tashin hankalin da na gani ya fi na yaƙin Maitatsine'

Malama Rahama a cikin gidanta da ke unguwar Ƙofar Mata da ke Kano
Bayanan hoto, Rahama ta shiga ruɗu lokacin da ta ji ana saran ɗanta maras lafiya da adda amma ba za ta iya ceton shi ba
    • Marubuci, Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Abuja, Nigeria
  • Lokacin karatu: Minti 6

Gargaɗi: Wannan labari na ƙunshe da bayanai waɗanda za su iya tayar da hankali.

A unguwar ƙofar Mata, ɗaya daga cikin daɗaɗɗun unguwanni masu tsohon tarihi a birnin Kano, kusan kowane gida na da wata alama da ke nuni da faruwar hare-haren ƴan daba.

A jikin ƙofofi da dama za ka iya ganin alamar sarar adda ko kuma gatari, kasancewar idan ƴan daba suka kawo farmaki, baya ga mutane, hatta ƙofofin gidaje da kantunan da ake yi da langa-langa ko ƙarfe ba su tsira ba.

Faɗa ne tsakanin gungun matasa masu adawa da juna, inda abu kaɗan zai iya haifar da karon-batta a tsakaninsu, wanda ke haifar da kisa da kuma barin waɗanda suka tsira da munanan raunuka.

Matsalar daba ta zamo ruwan dare a wasu daga cikin sanannun unguwannin a Kano, jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya kuma cibiyar kasuwanci.

Lamarin da ya tilasta wa gwamnatin jihar Kano samar da wani kwamitin da ta yi wa laƙabi da 'Anti Daba', wanda ya haɗa da jami'ai daga hukumomin tsaro na Najeriya daban-daban.

Sai dai duk da haka matsalar ba ta ƙare ba.

A irin haka ne, wata ranar Asabar ta farkon watan Agusta ƴan daba suka shigo unguwar suka sassari mutane tare da kashe wani baƙo.

'Ina ji ana saran ɗana amma ba zan iya ceton shi ba'

Iliya a cikin ɗakin da ƴan daba suka sassare shi
Bayanan hoto, Iliya na fama da lalurar da ke hana shi kuzari da magana
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahama, dattijuwa ce mai ƴaƴa shida, kuma an haife ta ne a unguwar ta Ƙofar Mata, sannan a nan ta yi aure tun tana budurwa.

Yanzu haka tana jinyar ɗanta Iliya, mai kimanin shekara 21 wanda ke fama da rashin lafiyar da ke hana shi kuzari, kuma ba ya iya magana sosai, wanda ƴan daba suka yi wa mummunan sara a kusan dukkanin sassan jikinsa.

Sanye da farar riga ƴar shara da wando iya gwiwa, Iliya - wanda fuskarsa ke cike da bandeji sanadiyyar saran da ƴan daba suka yi masa da adda - ya zauna kusa da mahaifiyarsa yayin da take tattaunawa da BBC.

Ta shaida wa BBC cewa ba ta taɓa ganin tashin hankali kamar irin wanda ta gani a wannan karo ba.

"Na ga masifa iri-iri amma ban taɓa ganin irin wannan ba, ko yaƙin Maitatsine bai kai min bala'in da na gani a wannan karon ba," in ji Rahama.

Tana daga cikin waɗanda ƴan daba suka kutsa cikin gidanta da sanyin asuba, sa'ilin da mutane ke sallar asubahi.

Duk da cewa sauran ƴaƴanta maza sun yi nasarar tsallakewa ta katanga domin tsere wa maharan, Iliya, ya kasance a kwance cikin ɗaki kuma ba zai iya ƙwatar kansa ba.

A kansa ne ƴan dabar suka sauke fushinsu.

"Suka banko ƙofa suka shigo, muka tashi, wasu suka haura ta katanga, mu kuma muka shiga ɗaki muka kulle," a cewar Rahama.

"Har sun zo (ƴan daba) za su fita sai suka gan shi a cikin ɗaki, sai suka dawo, suka shiga suka riƙa saran shi.

"Ina jin ana saran ɗana kamar yadda ake saran itace amma babu dama na cece shi saboda ina gudun kada su dawo kaina.

"Su na ta saran shi har sai da ya yi ƙara, ya ce aaargh aaargh!! sau biyu, daga nan sai ya yi ɗif, sai suka ce ya mutu, ku zo mu tafi," Kamar yadda Rahama ta bayyana wa BBC.

Bayan kammala saran Iliya, ƴan dabar sun bankade ƙofar ɗakin da Rahama ke ciki, inda suka buƙace ta da ta miƙa masu wayarta ta hannu.

"Na ce musu ni tsohuwa ce ba na da waya, amma suƙa ƙi, sai da na ba su haƙuri, sai suka tafi."

'Babu wanda ya tsira'

Alamar sara da adda kan wani shago na langa-langa a unguwar Kofar Mata
Bayanan hoto, Alamar sara da adda kan wani shago na langa-langa a unguwar Kofar Mata

Ɗaya daga cikin abin da ya fi tayar da hankali a ranar shi ne yadda ƴan dabar suka kashe wani baƙo mai suna Imrana Isa, wanda ya je ziyara wurin kawunsa Malam Lawal Mai hijabi.

"Ɗa ne a wurina, saboda ɗan yayana ne, matarsa tana da juna-biyu shi ne ya taho nan Kano domin yin sayayya, a lokacin ba na nan," kamar yadda Malam Lawal ya shaida wa BBC.

"Ya fito domin yin alwalar sallar asuba kawai sai ya hadu da su, daga nan suka kama sarar shi.

"Lokacin da aka kira ni a awaya aka fada min sai na ce a kai shi asibitin Malam Aminu Kano, a lokacin da aka kai shi, sai malaman asibiti suka ce ya rasu."

Wani mutum na daban da lamarin ya rutsa da shi, shi ne Malam Iliyasu, wanda ladani ne na ɗaya daga cikin masallatan da ke unguwar.

"Na fito daga masallaci, ina zaune a zaure ina karatu kawai sai na ji an banko ƙofa da ƙarfi, lokacin da na juya kawai sai na ga mutum tsaye da adda, sai na ji kaf, ya sare ni a kai, sai na faɗi, ɗaya daga cikinsu ya ce a kashe ni kawai, Allah ne ya tseratar da ni," in ji Malam Iliya.

Abideen ya zama mai guntulallun yatsu

Abideen zaune a ƙafar gida
Bayanan hoto, Abideen na zaune a ƙofar gida lokacin da ƴan dabar suka shigo unguwar Ƙofar Mata

Abideen ya rasa yatsunsa ne a lokacin da ya yi yunƙurin kare sara da adda da wani ɗan daba ya riƙa yi masa.

Matashin na zaune ne a ƙofar gida lokacin da ƴan daban suka kawo harin na baya-bayan nan.

"Ɗaya daga cikin su (ƴan daba) da ya tsaya a ƙofar gidanmu ne ya rufe ni da sara, ya yi min sara biyu a kaina, lokacin da na sa hannu domin na kare sai ya ƙara kawo sara, kawai sai na ga ƴan yatsuna guda biyu sun fita ɗayan kuma na rawa, fata ce kawai ta riƙe shi," in ji Abideen.

A lokacin da aka je asibiti, likitoci sun ce ba za a iya mayar wa Abideen yatsunsa ba.

Baya ga sare masa yatsu, ƴan dabar sun kuma sari Abideen a gadon bayansa da kuma gefen cikinsa.

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton Haruna Kakangi kan matsalar daba a Kano

Yaran ƴan siyasa, shaye-shaye

Akwai abubuwa uku da suke haifar da ƙazancewar matsalar daba a Kano: ayyukan siyasa, shaye-shaye da kuma taɓarɓarewar tarbiyya.

Ana zargin akasarin ƴan siyasa a Kano da tallafa wa ƴan daba.

Hakan na fitowa ƙarara a lokutan yaƙin neman zaɓe.

Ko a lokacin zaɓen cike gurbi na ƴan majalisa da aka gudanar a watan nan na Agusta, rundunar ƴansanda a jihar Kano ta sanar da cewa ta kama ƴan daba ɗauke da makamai iri-iri.

Ana zargin cewa ƴan siyasa ne ke tallafa wa irin wadannan ƴan daba da kuɗi da kuma miyagun ƙwayoyin da suke sha kafin aikata ta'asa.

Wani ɗan siyasa a jihar, Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce ƴan daba "matasa ne waɗanda aka yi amfani da su a lokacin siyasa amma aka manta da su daga baya."

Sai dai jami'an tsaro ba su da ƙarfin halin kama irin wadannan ƴan siyasa, hasali ma su ne ke ba su tsaro.

Sai kuma shaye-shaye, wanda ake ganin abu ne da ke bayar da gagarumar gudumawa wajen ƙazancewar matsalar ayyukan daba a jihar.

Zainab Nasir, wata matashiya mai yaki da matsalolin matasa a Kano ta ce "babu wani ɗan daba da zai aikata ɓarna sai ya yi shaye-shaye".

'Muna yin bakin ƙoƙarinmu'

A tsakanin bakin titin da ya raba unguwanni Ƙofar Mata da Zango, akwai wasu motocin ƴansanda da aka girke, yayin da jami'an ƴansanda ke zaune a gefe suna lura da abubuwan da ke gudana.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan Najeriya a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa BBC cewa an ajiye ƴansandan ne domin su hana ɓarkewar irin waɗannan rikice-rikice na daba kasancewar "rikici ne tsakanin matasan unguwar Zango da kuma matasan unguwar Ƙofar Mata."

Kiyawa ya ce babbar matsalar ita ce "maimakon kowane manyan unguwar kowane ɓangaren su ja kunnen matsanasu, sai suna ganin laifin ɗaya ɓangare."

Ya ƙara da cewa yanzu sun ɗauki matakin ganawa da shugabannin al'umma a wadannan unguwanni domin fadakar da su kan illar hakan domin ganin an kawar da matsalar.