Shin matsalar dabanci ta gagari hukumomi ne a Kano?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
- Lokacin karatu: Minti 5
Matsalar daba da kwacen waya, sun zama ruwan dare a Kano, jiha mafi yawan al’umma a Najeriya.
Mutane da dama na ci gaba da rasa rayukansu sanadiyyar wadannan matsaloli, yayin da masu nisan kwana cikin wadanda kan yi ido hudu da irin wadannan mutane a mafi yawan lokuta kan tsira ne da wani mummunan raunin da za su tafi lahira da tabonsa.
A wannan makon ne birnin Kano ya sake amo a kafofin sadarwa, sannan ƴan birnin suka shiga mummunan tashin hankali bayan wasu matasa da ake zargin 'yan daba ne sun kashe wani jami'in gwamnatin jihar mai suna Sadiq Gentle.
Sadiq, wanda shi n mai ɗaukowa gwamnan Kano rahoto na musamman a hukumar kula tarihi da al'adu ta jihar ya rasu ne kwanaki kaɗan bayan an kai masa hari har gida, inda aka caccaka masa wuƙa, lamarin da ya jefa shi mawuyacin hali kafin hali ya yi.
Kisan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu da ake zargi ƴan daba ne sun kashe wani ɗalibin Jami'ar Bayero wato BUK da ke Kano mai suna Umar Abdullahi Hafizi a gidansu da ke yankin Ɗorayi a birnin jihar.
Harkar daba wata matsala ce da ta daɗe tana ci wa mutanen jihar tuwo a ƙwarya tun shekaru aru-aru a jihar, duk da akan samu sauƙi, sannan a koma gidan jiya, duk da cewa ba a jihar ba ne kaɗai lamarin ke ajalin mutane.
Wannan ya sa wasu mazauna birnin ke cewa ayyukan ƴandaba sun fara zama ruwan dare gama gari, inda wasu ke tambayar ko dai lamarin ya gagari gwamnati ne?
Ko me ya sa gwamnati ke fuskantar kalubale wajen dakile wannan barazana? Kuma shin akwai makoma mai kyau ga matasa da ke tsunduma cikin dabi'ar daba?
Yawaitar lamarin
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ganin yadda lamarin ke ta'azzara ne gwamnatin Kano ta kafa kwamitin yaƙi da harkar daba da ƙwacen waya da gyara hali a ƙarƙashin kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar, Dokta Yusuf Ƙofar Mata, wanda ya bayyana wa BBC cewa suna samun nasarori sosai.
A game da harkar na raguwa ne a jihar, Ƙofar Mata ya ce, "tun bayan aka kafa kwamitinmu na murƙushe daba a Kano, za a ce abubuwa sun yi baya sosai. Za mu a iya cewa an murƙushe su. A lokacin duk wani wanda yake taƙama da daba, sai da aka kama shi, ko kuma ya gudu ya bar garin nan."
Ya ce kwamitin sai da ya kama aƙalla mutum 1,500 waɗanda ya ce yawancin sun fuskanci.
"A lokacin muna da kotun tafi da gidanka. Da mun kama mutum, za mu gabatar da shi, sai kotu ta yanke masa hukunci," in ji shi.
Ƙofar Mata ya ce bayan kama waɗanda suke zargi da aikata laifin, sun kuma nasarar tattara sunan wasu matasa kusan 700, waɗanda ya ce, "mun fahimci suna da alamar gyaruwa. Wannan ne ma ya sa a lokacin gwamna ya sanar da ɗaukar matasa 1,400 a makarantar koyon sana'a domin su shiryu har ma su amfani al'umma."
Dawo da hannun agogo baya
Ganin yadda lamarin ke tafiyar hawainiya ne ya sa wasu suke cewa akwai sakacin masu riƙe da madafun iko.
Sai dai a game da wannan, Ƙofar Mata ya ce sake ta'azzarar lamarin ba zai rasa nasaba da ɗan takawa da kwamitin ya yi ba.
"Bayan wannan nasarar da muka samu, kasancewar ka san asali aiki ne na ƴasanda da sauran jami'an tsaro, sai kwamiti ya ɗan dakata da aiki domin ana ganin an riga an gano bakin zaren lamarin. Amma kuma daga bisani sai abin da ya sake dawowa."
Ya ce wannan ne ya sa gwamnan ya bayar da umarnin cewa kwamitin ya koma aikin cikin gaggawa "a wannan makon domin a sake tsabtace garin."
Ya ce dama asali aiki ne ƴansanda da sauran jami'an tsaro, "saboda babu wanda zai iya aikin da ƴansanda da sauran jami'an tsaro. Kuma a Kano muna da kwamishinan harkokin tsaron cikin gida," in ji shi, inda ya ƙara da cewa suna aiki ne a tare domin tabbatar d samun nasara.
Alaƙa da siyasa
Game da zargin da ake yi na cewa harkar ta ƙi cinyewa ne saboda alaƙar da take da ita da siyasa, kwamishinan ya ce lallar akwai wannan matsalar, wadda a cewarsa tana jawo tsaiko ga kwamitinsa.
"Ba za ka taɓa rasa alaƙar siyasa da daba ba, domin za ka ga wasu mutane an san su sanannun ƴandaba ne, amma kuma za ka ga mun kama su, an ɗaure su, sai ka ga an ɓullo ta wasu hanyoyi ko ta lauyoyi an sake su."
Ya ce a kwanakin baya akwai wanda aka kama a jihar, wanda a cewarsa sanannen mai aikata laifi ne, "amma saboda ba a cika kai rahotanni ayyukansa ba, sai ya zama babu rubutaccen rahoto na ayyukansa.
Sannan lokacin da aka kama shi, ba a kama shi yana cikin aikata laifi ba, haka muna ji muna gani aka ɗauko masa lauyoyi kusan 30, dole aka bayar da belinsa.
Kuma irin haka na faruwa da muna ganin suna da alaƙa da siyasa."
Ƙofar Mata ya ce wannan ne ya sa ya je ya samu ƙungiyar lauyoyi ta Kano, "Sannan na roƙe su a kan idan dai sun ji mutum sanannen ɗandaba ne, ko da an buƙaci su shigo da sunan haƙƙin ɗan'adam, su haƙura su janye duk kuwa da cewa doka ba ta su dama, amma saboda halin da ake ciki, su riƙa haƙura."
Kashe jami'in gwamnatin Kano
A game da batun kashe jami'in gwamnatin jihar, kwamishinan ya ce wasu ɓatagari ne suka masa illa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
"Ko jiya (Alhamis) mun zauna da DPO mun yi taro game da lamarin. Dama mutum biyu ne aka kashe a tsakankanin wato da Sadiq Gentle da wani ɗalibin BUK wato Hafizi. Tuni an kama waɗanda ake zargi da kashe Hafizi, ina tabbatar maka nan da wasu awanni za a samu labarin waɗanda ake zargi da kashe Sadiq."
Ya ce tuni gwamna ya ba da oda a kan a kama waɗanda suka kashe matashin, "kuma muna fata a sanadiyar wannan aikin za a kawo ƙarshen lamarin a jihar Kano baki ɗayanta."
Ya ce duk wanda aka kashe kuma suna samu rahoto, "muna bibiya kuma ana samun nasarar kamawa waɗanda ake zargi da duk wani kisa da aka yi. Wasu da dama an yanke musu hukunci."
Matakan kariya
Dokta Yusuf Ƙofar Mata ya bayyana wasu hanyoyi da yake tunani ya kamata a ɗauka domin samun sauƙin lamarin:
- Mu zama masu sa ido.
- Kula da waɗanda ba sa barci da wuri
- Kula da waɗanda suke ƙulle-ƙulle
- Haɗa kai da ƴansanda
- Haɗa kai da masu unguwanni
- Kafa kwamitin tsaro a unguwanni
Ya ce ko lokacin da kwamiti ya tsagaita aiki, "idan muka samu rahoto cewa akwai masu yunƙurin aikata ɓarna, muna tunkararsa mu daƙile. Mun samu labarin yunƙurin aikta ɓarna kusan 100 waɗanda muka daƙile," in ji Yusuf Ƙofar Mata.











