PDP da APC na cacar baki kan sauya sheƙar 'yan majalisar dokokin jihar Rivers

Asalin hoton, OTHER
Babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya PDP ta zargi takwararta ta APC mai mulki da kitsa makircin da ya haddasa sauya sheƙar da wasu `yan majalisar dokokin jihar Rivers suka yi daga PDP zuwa APC.
A ranar Litinin ne 'yan majalisar dokokin jihar River su 27 suka sanar da sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Ana kallon matakin a matsayin wani sabon babi da rikici siyasa tsakanin tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike da gwamnan jihar mai ci, Siminalayi Fubara.
Me jam'iyyar PDP ta ce ?
Jam`iyyar PDP ta ce APC na so ne ta murkushe jam`iyyun hamayya domin ta mamaye siyasar kasar ta yadda za ta yi mulki ba tare da wani ya taka mata birki ba.
Jam`iyyar PDP ta ce maitar APC ta fito fili da sauya shekar da `yan majalisar dokokin jihar Rivers su 27 suka yi, tana zargin cewa APC ce ke neman kwashe mata kafa a jihar da Najeriya baki daya, domin ta sakata ta wala a fagen siyasa, kuma wannan ne ya sa take amfani da ministan birnin tarayya yana yi wa PDP kafar-angulu.
Alhaji Ibrahim Abdullahi mataimakin kakakin jam`iyyar PDP na kasa ya ce "abin da ke gaban APC shi ne ta rungume duk wata jam’iyya don ganin an koma jam’iyya guda."
”Daga ganin abin da ya faru an san ya sabawa hankali domin babu laifin zaune balle na tsaye a tashi lokaci guda ace cikin mutum 32, mutum 27 ko 28 sun sauya sheka, dole akwai lauje cikin nadi," in ji shi.
Ya ƙara da cewa "yanzu uwar jam’iyya ta yanke shawara za a zauna idan kora ce a kori wanda muke ganin shi ya haddasa wannan sauya sheka wato ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.”
Me Jam'iyyar APC ta ce?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jam'iyyar APC da ke mulki a martaninta ta ce rashin iya takun siyasa ne ya jefa PDP cikin matsalar da ta tsinci kan ta.
Malam Bala Ibrahim daraktan yada labarai ne jam`iyyar APC, ya ce siyasa tamkar karatun allo ce wato kowa ya biye allonsa sai ya wanke.
"Duk wanda ya ce jam`iyyarsu ta fi karfin PDP a fagen karatu irin na siyasa kuma wanda ya fi ka karfi, sai ya kama hannunka ya mare ka da shi."
Ya ce, “ PDP ita ce lokacin da ta ke kan mulki ta yi kuri ta cika baki ta ce za ta yi shekaru 60 tana mulki, sai gashi ko watanni 60 ba su yi ba aka kore su daga kan mulki, sannan yanzu kuma ake koya musu yadda ake siyasa.”
Malam Bala Ibrahim, ya ce, “ Gasa ce ta siyasa ba wai gaba ba, kuma ana so a nunawa jam’iyyar PDP cewa,basu iya ba kuma ‘ya’yansu za su rinka juya musu baya saboda ‘yan Najeriya yanzu kan Mage ya waye.”
Masana siyasa na ganin rikicin siyasar kan rura wutar wata sabuwar rigama watakila ta kai ga matakin tsige gwamnan jihar, wanda ke zaman doya da manja da tsohon ubangidansa na siyasa ministan birnin tarayya Nyesom Wike, wanda PDP ke zargin cewa ya zama sawun keke tun da ya karbi mukami daga hannun jam`iyyar APC.











