Asibitocin da yakin Isra'ila da Hamas ya ritsa da su a Gaza

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Graeme Baker
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Asibitoci da cibiyoyin lafiya ne a matsanancin faɗa ya ritsa da su, yayin da Isra'ila ke zafafa hare-harenta kan mayakan Hamas a Birnin Gaza.
Hankali ya fi karkata a kan Al-Shifa, asibitin Gaza mafi girma, inda aka yi kiyasin cewa akwai mutum 2,300 da yakin da ake gwabzawa a titunan da ke zagaye da wurin, ya ritsa da su.
Sauran cibiyoyin lafiya na Gaza su ma suna bayar da rahotannin shiga irin wannan lamari - na yankewar kayan bukatun lafiya da lantarki da kuma barazana ga rayuka da ta kasance saboda fada.
Isra'ila ta ce ba ta kai farmaki kai tsaye a kan asibitoci amma ta amsa cewa ana "gwabza fada" a zagayen Al-Shifa da sauran cibiyoyin lafiya.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an lalata cibiyoyin lafiya 36 ciki har da asibitoci guda 22 tun bayan barkewar yaki a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma kalilan ne kawai har yanzu suke aiki.
Ga abin da BBC ta sani game da halin da ake ciki a manyan asibitocin da ke arewacin Gaza.
Asibitin Al-Shifa, Birnin Gaza
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce a ranar Lahadi Al-Shifa na Birnin Gaza - asibitin yankin mafi girma da gado 700 - ya daina aiki kuma al'amura a ciki sun kasance "cike da tsanani da kuma hatsari".
Rikici ya kaure tsakanin mayakan Hamas da sojojin Isra'ila a titunan da ke zagaye da asibitin. An lalata muhimman kayayyakin aiki, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Isra'ila ta ce mayakan Hamas na aiki ne daga hanyoyin kasa da ke karkashin asibitin - ikirarin da Hamas ta musanta.
Ma'aikatan da ke ciki sun ce abu da ba zai yiwu mutum ya fita wajen asibitin ba, ba tare da an ji masa rauni ko ma an kashe shi ba.
Babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya fada a shafin X cewa "harbe-harbe da luguden bama-bamai babu kakkautawa a yankin na ci gaba da ta'azzara halin da tuni ya zama mawuyaci".
Rahotanni birjik daga cikin asibitin sun ce babu abinci kuma babu man fetur da za a kunna jannaretoci. Ana ci gaba da amfani da makamashin hasken rana don bai wa muhimman sassan asibitin wutar lantarki.
An katse layukan sadarwa - kungiyar Doctors Without Borders ba ta iya tuntubar wakilanta da ke cikin Gazan a karshen mako. Yunkurin da BBC ta yi na tuntubar ma'aikata shi ma sau da yawa bai yi nasara ba.
Ma'aikatar lafiya wadda Hamas ke tafiyarwa ta ce akwai akalla mutum 2,300 har yanzu da ke cikin asibitin - kuma marasa lafiya fiye da 650, da kuma ma'aikata 200 zuwa 500, sannan akwai mutane kimanin 1,500 da ke neman mafaka.
Adadin ya hadar da jarirai sabbin haihuwa da ke kwance a dakin tiyata na asibitin.
Ma'aikata sun ce uku daga cikin jarirai guda 39 da suke kula da su, sun rasu a karshen mako saboda rashin kwalaben da ake sanya jarirai. Jariran da suka tsiran kuma na cikin gagarumin hatsarin mutuwa, a cewar likitocin.
Babban mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila, Rear Admiral Daniel Hagari ya fada a ranar Asabar cewa Isra'ila za ta samar da taimako don kwashe jariran zuwa wani "asibiti mafi aminci".
Sai dai har zuwa safiyar Litinin din nan, ba a iya kwashe jariran ba.
Ma'aikatan asibitin sun shaida wa BBC cewa kwashe jarirai cikin aminci zai bukaci ingantattun kayan aiki na zamani, kuma babu wani "asibiti mai aminci" a cikin Gaza.

Asalin hoton, Reuters
A ranar Asabar, Kanal Moshe Tetro na rundunar sojin Isra'ila, ya ce an samu gwabza fada a kusa, amma ba su harbi a kan asibitin ba, sannan ba a yi masa kofar rago ba.
Duk wanda yake son fita, in ji shi, yana iya yin haka. Ya dage a kan cewa sabanin abin da ya fada kuwa, karya ne kawai.
Marwan Abu Saada, wani likitan fida a asibitin Shifa, ya fada wa BBC an yi luguden bama-bamai a kusa da asibitin kuma motocin marasa lafiya ba sa iya shiga ciki.
Rundunar sojojin Isra'ila ta kuma ce kokarin kai man fetur lita 300 zuwa asibitin Al-Shifa ya ci tura saboda Hamas ta ki karba - wani abu da Hamas ta musanta.
Abu Saada ya shaida wa BBC cewa a ranar cewa lita 300 zai "yi tsawon minti 30 ne" - amma asibitin na bukatar man fetur lita 10,000 a rana don yin aiki kamar yadda ya saba.
Bugu da kari a kan haka shi ne karuwar hatsarin barkewar cuta saboda rashin tsafta, da kuma zagwanyewar gawawwakin da ba a iya sanya su a gidan sanyi ba.
Mista Abu Saada ya ce yunkurin binne gawawwakin ya gamu da cikas daga fadan da ake gwabzawa a zagayen ginin asibitin, kuma gidan sanyi na dakin ajiyar gawa ya daina aiki saboda rashin lantarki.
Akwai gawa 100 da ba a binne ba a harabar asibitin, ya kara da cewa.
Isra'ila ta jaddada cewa akwai cibiyar gudanar da harkokin mayakan Hamas a karkashin asibitin Al-Shifa, kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila Libbu Weiss ta ce: "Muna da tabbas kan abin da muka fada. Mun fitar da muhimman bayanai a kan haka."
Ta fitar da wata taswirar na abin da ta yi ikirarin cewa hanyoyin karkashin kasa ne a kasan asibitin, da kuma bayanan da aka nada wadanda ta ce na mayakan Hamas ne da ke tattaunawa game da su.
Hamas ta musanta cewa tana amfani da asibitin ko kuma tana da cibiyar gudanar da aikace-aikace a kasan asibitin. Likitocin da ke ciki sun dage cewa babu kasancewar Hamas a wurin.
Wakilin BBC na Gaza, Rushdi Abdalouf ya ce bai taba ganin "wasu harkokin mayaka" a cikin asibitin ba, amma ya amsa cewa abu ne mai wuya a iya tantance gaskiyar ikirarin Isra'ila da na Hamas.

Asibitin Al-Quds
Asibiti na biyu mafi girma a Zirin Gaza shi ma, a cewar kungiyar ba da agaji ta Red Crescent, ya dakatar da aiki. Kungiyar Red Crescent ta Falasdinawa a ranar Asabar ta ce an ritsa da jami'anta a cikin asibitin tare da marasa lafiya 500 da kuma mutanen da rikici ya raba da muhallansu kimanin 14,000, akasarinsu mata da kananan yara.
A ranar Lahadi, kungiyar ta ce asibitin ya "dakatar da aiki.... saboda raguwar makamashi, kuma an samu katsewar lantarki".
"Ma'aikatan lafiya na yin duk wani kokari wajen bai wa marasa lafiya da wadanda aka raunata kulawa, ko da ta kama su yi amfani da hanyoyin likitanci na zamani cikin tsananin bukatar ayyukan jin kai da karancin kayan kula da lafiya da ruwan sha da kuma abinci.
"An bar asibitin ya nema wa kansa mafita yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta, lamarin da ya jefa ma'aikatan lafiya da marasa lafiya da fararen hulan da rikici ya raba da muhallansu, cikin gagarumin hatsari."
Kungiyar ba da agaji ta Doctors Without Borders ta fada ranar Asabar cewa ta gaza tuntubar wani likitan fida da ke aiki kuma yake samun mafaka a asibitin Al-Quds tare da iyalansa.
Wani mai magana da yawun kungiyar Red Crescent ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an datse asibitin kusan tsawon mako daya kenan "babu shiga, babu fita", kuma ana ci gaba da kai hari ba kakkautawa a yankin da ke zagaye.
Al-Rantisi da al-Nasr, a arewacin Birnin Gaza
An kwashe marasa lafiya daga karamin asibitin Rantisi na kwararru mai kula da lafiyar kananan yara da kuma asibitin Al-Nasr da ke kusa, a arewacin Birnin Gaza ranar Juma'a, in ban da ma'aikata da marasa lafiya kalilan.
Asibitin Rantisi ne kawai yake da dakin kula da lafiyar jarirai masu cutar kansa a Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila ta saki wani bayani ga BBC dangane da wasu hirarraki tsakanin wani jami'i a asibitin Rantisi da kuma wani babban jami'i a rundunar sojojin Isra'ila, inda suka tattauna kan shirye-shiryen samar da motocin daukan marasa lafiya da za su kwashe masu jinya.
Jami'in asibitin ya yi tambaya game da daruruwan fararen hula da rikici ya raba da muhallansu wadanda suka yi sansani a asibitocin guda biyu.
Jami'in sojan Isra'ilan ya shaida masa cewa ya fada musu su fita ta babbar kofa da misalin karfe 11:20, sannan ya yi masa cikakken bayani a kan titunan da ya kamata su bi lokacin da suke fita daga Birnin Gaza.
Kuma sau biyu yana fada wa jami'in asibitin ya tabbatar cewa fararen hulan na dauke da wani abu fari don nuna cewa su ba mayaka ba ne.
"Za su fita, dukkansu sun daga hannuwansu sama," jami'in asibitin ya ce. "Hakan ya yi," a cewar Isra'ila.
Jaridar New York Times ta ruwaito Dr Bakr Gaoud, shugaban asibitin Rantisi na cewa dakarun Isra'ila sun isa a karshen makon jiya kuma ba su taswirar da ke nuna hanyar fita amintacciya.
"Mun rika jan marasa lafiyanmu daga kan gadajensu," in ji shi, ya kuma ce mrasa lafiyan da ke cikin mawuyacin hali an tura su Al-Shifa, wanda tuni shi ma ya cika dankam kuma ya dakatar da aiki.
Kowa kuma daga nan, in ji shi, ya kama hanyarsa zuwa kudancin Gaza don barin yankin da ake gwabza gagarumin fada.











