Ƴan Isra'ila na rige-rigen mallakar bindiga bayan harin Hamas

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Ƴan Isra'ila na rige-rigen mallakar bindiga bayan harin Hamas
Gwamnati ta sauƙaƙawa 'yan Isra'ila samun lasisin bindiga tun bayan harin Hamas
Bayanan hoto, Gwamnati ta sauƙaƙawa 'yan Isra'ila samun lasisin bindiga tun bayan harin Hamas

Tun bayan harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a farkon watan Oktoba sama da mutum 120,000 ne suka rubuta takardar neman lasisin riƙe bindiga.

Wuraren koyon harbi suna fuskantar tuɗaɗar mutane da ba su taɓa gani ba na Isra'ilawa waɗanda ke neman haɓaka ƙwarewarsu.

A wajen shagunan bindigogi, akwai dogayen layukan mutane suna jiran sayen makaminsu na farko.

Bayan sanarwar da gwamnatin Isra'ila ta yi na cewa za ta sassauta dokokinta na mallakar bindiga, waɗanda suka cancanta da ba su taɓa aikaita wani laifi ba ko kuma matsalar lafiya, yanzu suna iya samun lasisin bindiga cikin mako ɗaya.

Kuma za a bai wa mutane damar mallakar harsasai har 100, daga 50 da aka ƙayyade a baya.

"Yanzu, saboda sun cire takunkumin, mallakar bindiga na da sauki" in ji Omri Shnaider, wani lauya mai shekaru 41 daga Kibbutz da ke wajen birnin Ƙudus.

Amma Mista Schnaider bai yi farin ciki game da shawarar ba. Ya na duba illolin da kan iya ɓullowa sakamakon dubun dubatar makamai da ake raba wa fararen hula.

"Akwai fa'ida, amma babu shakka kuma akwai rashin fa'idar hakan. Muna ganin abin da ya faru a Amurka.

Amma wannan shi ne abin da nake ganin ina buƙatar in yi, don jama'ar Isra'ila su samu kwanciyar hankali."

Ministan tsaron ƙasar mai tsattsauran ra'ayi, Itamar Ben-Gvir, wanda ya dade yana goyon bayan mallakar bindigogi, yana rangadin kasar yana bayar da dubban makamai.

Ya ce sabbin makaman na musamman na waɗanda ke zaune kusa da kan iyaka da Gaza ne ko kuma ke yankunan da Yahudawa da Larabawa ke zaune tare, ya kuma ƙarfafa wa dukkan waɗannan al'ummomin Yahudawan ƙwarin gwiwar kafa ƙungiyoyin tsaro na farar hula.

Mista Schnaider yana zaune ne a Kibbutz wanda ke da iyalai 200. Ya goyi bayan wannan ra'ayi na "aikin tsaron farar hula".

"Saboda halin da ake ciki, a Kibbutz dina, mun yanke shawarar samun bindigogi mu kuma kaddamar da ƙungiyoyin tsaro na unguwanni. Wannan tawagar masu bayar da agajin gaggawa za su kawo ɗauki idan har ƴan ta'adda suka sake kawo wani harin."

Sai dai yayin da akasarin Yahudawan ke neman hanyoyin da za su kare kansu, Larabawan Isra’ila, wadanda ke da sama da kashi 20% na al’ummar ƙasar, sun ce ba su taɓa jin tsoro irin yadda suke ji ba a yanzu.

Ƴan Isra’ila Larabawa daga ko’ina cikin ƙasar ne suka bayar da rahoto ga BBC kan abubuwan da suka faru na nuna wariya, cin zarafi da cin zarafi ta yanar gizo.

Birnin Lod da ke tsakiyar Isra'ila yana da tarihin tashin hankali na kabilanci tsakanin Yahudawa da Larabawa.

Malama kuma uwa Suhair Hamdouni
Bayanan hoto, Malama kuma uwa Suhair Hamdouni

Suhair Hamdouni, ƙwararriyar malamar masu buƙata ta musamman, ta zauna a Lod tsawon rayuwarta. A gefe ɗaya na layin gidansu akwai gidajen Yahudawa, a ɗaya bangaren kuma Larabawa ne.

Ta ce tun lokacin da aka kai hare-haren, ba ta sake zuwa sayen kayan abinci a unguwar Yahudawa ba amma tana tafiya mai nisa zuwa shagunan Larabawa, kawai saboda tsoron kada a muzguna mata.

"A baya an kai mana hari a gidajenmu, muna fama da jimamin wannan farmakin."

Larabawan da ke zaune a Isra'ila , waɗanda yawancinsu ke iƙirarin cewa su Falasɗinawa ne, gaba ɗaya an keɓe su daga shiga aikin soja.

Idan ba tare da wannan horo ba, yana da wahala a gare su su sami lasisin bindiga.

"In tsoron cewa yayin da 'yan Isra'ila suke amfani da 'yancinsu na kare kansu, zan iya rasa raina, ni da 'ya'yana.

"Ba don na yi wani abu ba, amma don ni Balarabiya ce, idan Yahudawan da ke unguwarmu su na da 'yancin samun bindigogi, to ni ma ya kamata in samu, ko kuma a hana duka bangarorin biyu mallakar bindigogi."

Tun bayan harin da Hamas ta kai, garuruwan da ke da Yahudawa da Larabawa a Isra'ila, waɗanda a da suka bunƙasa sakamakon 'yan yawon bude ido na cikin gida, yanzu sun kasance babu kowa. An rufe shagunan kuma an rufe dukkan gidajen cin abinci.

"Fiye da kashi 60% na abokan cinikina Yahudawa ne," in ji mai gidan abincin Lod, Abu Amir.

"Amma yanzu ba sa zuwa, ba mai zuwa, ba mai kira, Larabawa suna tsoron zuwa unguwannin Yahudawa, Yahudawa kuma suna tsoron zuwa garuruwan Larabawa."