Abin da shugaban Hamas ya shaida wa BBC game da rikicin Gaza

Moussa Abu Marzouk
Bayanan hoto, Moussa Abu Marzouk ya ce bangaren Hamas da ke dauke da makamai "ba sai sun tuntubi shugabannin siyasa ba."
    • Marubuci, Feras Kilani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic

Ɗaya daga cikin jagororin kungiyar Hamas ya ƙi amincewa da cewa ƙungiyarsa ta kashe fararen hula a Isra'ila, yana mai cewa manufarsu ita ce kai hari kan dakarun ko-ta-kwana ne kawai.

Moussa Abu Marzouk ya shaida wa BBC cewa "an tsame mata da yara da fararen hula daga hare-haren na Hamas."

Ikirarin nasa ya sha banban da tarin bidiyo da ke nuna mayaƙan Hamas suna harbin manya da yara marasa makami da bindiga.

Isra'ila ta ce sama da mutane 1,400 ne Hamas ta kashe a hare-haren ranar 7 ga Oktoba, yawancinsu fararen hula.

An tattauna da Mr Marzouk, mataimakin shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar, wanda aka ƙwace kadarorinsa a Burtaniya karkashin dokokin yaki da ta'addanci, a ranar Asabar a yankin Gulf.

Shi ne ɗan ƙungiyar Hamas mafi girman muƙami da ya yi magana da BBC tun a ranar 7 ga watan Oktoba.

BBC ta matsa wa Mista Marzouk lamba kan yakin Gaza, musamman kan ɗimbin mutanen da ake garkuwa da su a yankin.

Ya mayar da martani da cewa, ba za a samu ƴantar da waɗanda ake garkuwa da su ba yayin da Isra'ila ke cigaba kai hare-haren bama-bamai a Gaza.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce an kashe mutane 10,000 tun lokacin da Isra'ila ta fara kai harin a watan jiya.

"Za mu sake su, amma muna bukatar mu dakatar da fadan," in ji shi.

Kwanan nan Mista Marzouk ya je birnin Moscow don tattaunawa kan wasu ƴan Rasha mazau na Isra'ila guda takwas, waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su a ranar 7 ga Oktoba, ƙungiyar da Birtaniya da Amurka da wasu ƙasashen duniya suka ayyana ta a matsayin ta ƴan ta'adda.

Ya ce Hamas "ta duba tare da gano cewa akwai mata biyu da ake garkuwa da su" waɗanda ƴan Rasha ne, sai dai an kasa sakin su sanadiyyar rikicin da ke faruwa.

Ya ce za su iya sakin mutanen da suka garkuwa da su ne kawai "idan Isra'ila ta daina kai hare-hare, ta haka ne za mu iya miƙa su ga ƙungiyar Red Cross."

Lokacin da BBC ta ƙalubalance shi game da harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, Mr Marzouk ya yi iƙirarin cewa shugaban dakarun Hamas ta Qassam, Mohamed el-Deif ya umurci dakarun Hamas da kada su taɓa fararen hula.

Ya ce "El-Deif ya faɗa wa mayaƙa cewa kada ku kashe mace, kada ku kashe yaro kuma kada ku kashe tsoho."

Ya ce an sojojin ko-ta-kwana ne aka nemi "kai wa harin". Ya ce sojoji ko waɗanda ke jiran shiga soja ne aka hallaka.

Amma ba a taɓa mata, yara da fararen hula ba.

BBC ta ƙalubalanci babban jami'in na Hamas game da hotunan bidiyo waɗanda ke nuna yadda mayaƙan Hamas suka riƙa harbin fararen hula a cikin motoci da gidajensu.

Mr Marzouk wanda a wani lokaci yayin da ake tattaunawar ya nuna rashin jin daɗi, bai amsa tambayar kai tsaye ba.

Lokacin da aka tambaye kan ko ɓangaren tafiyar da mulki na Hamas na da masaniyar cewa za a kai wa Isra'ila hari, mataimakin shugaban ya ce "ba dole ba ne sai ɓangaren dakarun Hamas ya sanar da ɓangaren tafiyar da harkokin siyasa na ƙungiyar ba. Babu buƙata."

Sau da yawa ɓangaren tafiyar da harkokin siyasar Hams da ke da mazauni a Qatar na nuna cewa ba ya da alaƙa ta ƙut da ƙut da dakarun ƙungiyar.

Sai dai gwamnatin Birtaniya ba ta ga wani banbanci ba tsakanin ɓangarorin biyu - ta ayyana ɓangaren siyasa na Hams a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda a shekarar 2021, tana mai cewa "banbance ɓangarorin Hamas wani dodorido ne kawai. Hamas ƙungiya ce guda ɗaya."

Haka nan ma'aikatar kuɗ ta Amurka ta sanya sunan Mr Marzouk a jerin ƴan ta'adda na duniya, kuma an same shi da laifi a tuhume-tuhume da dama da suka shafi shiryawa da samar da kuɗaɗe ga Hamas.

Batun garkuwa da mutane

Tattaunawar da aka yi ta ranar Asabar ta zo ne bayan da Isra'ila ta yi watsi da buƙatar Amurka ta "tsagaita wuta domin kai tallafi" a Gaza da kuma taimakawa kan yadda za a fitar da mutane 240 da Hamas ke garkuwa da su.

A ranar Juma'a, firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce dole sai an sako mutanen da ake garkuwa da su kafin a yi wani batu na tsagaita wuta.

Mr Marzouk bai bayyana sunayen mutanen da ya bayyana a matsayin "baƙi" ba, kuma bai san inda da dama daga cikin su suke ba domin ana tsare da su ne a "wurare daban-daban."

Akwai ƙungiyoyi da dama da ke gudanar da ayyukansu a Gaza, ciki har da ƙungiyar masu jihadi ta Palestinian Islamic Jihad, wadda ke aiki kusa da kusa da Hamas sai dai tana zaman kanta ne.

Ya bayyana cewa ana m=buƙatar tsagaita wuta domin tattara bayanai - amma a a yanzu akwai wasu abubuwan da suka fi muhimmanci yayin da yankin ke fama da ruwan bama-bamai.

Mr Marzouk zai taka muhimmiyar rawa a yadda za a warware rikicin na Gaza, kuma akwai yiwuwar cewa zai zama mai matuƙar muhimmanci a tattaunawar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.