Za a riƙa biyan Faransawa lada idan suka yi wa rigunansu faci

Ɗaya daga cikin manufar gwamnatin ita ce samar da aikin yi ga masu yin gyaran tufafi

Asalin hoton, JEAN CHRISTOPHE VERHAEGEN/AFP

Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin manufar gwamnatin ita ce samar da aikin yi ga masu yin gyaran tufafi

Ƙasar Faransa ta kaddamar da wani shiri na bayar da lada domin shawo kan Faransawa da su dinga gyara tufafinsu da takalmansu da suka lalace a maimakon jefar da su da kuma sayen sabbi.

Daga watan Oktoba, ladan zai zo ta sigar ragi a kuɗin da ake karɓa na gyara, inda ragin zai kai na kuɗi tsakanin yuro shida (dalar Amurka biyar/kimanin naira dubu huɗu) zuwa yuro 25 (dalar Amurka 21) a kowane gyara.

Bérangère Couillard, wadda ita ce karamar ministar muhalli, ta yi korafin cewa tan dubu 700 ne na tufafi ake zubarwa a bola a Faransa duk shekara.

Gwamnati za ta bayar da gudunmawar yuro miliyan 154 wajen bayar da ladar na tsawon shekaru biyar.

Ms Couillard ta buƙaci "dukkanin shagunan dinki da masu sana'ar takalma da su shiga tsarin", wanda zai mayar da kudi wajen yuro bakwai na sabon takalmin da aka siya da kuma yuro goma zuwa 25 na sabon tufafi da aka siya.

Manufar ita ce tallafa wa sashin masu gyare-gyare da kuma samar da sabbin ayyukan yi.

Ta ce gwamnati ta himmatu wajen magance “amfani da kayan yayi” marasa inganci tare da neman karfafa gwiwar mutane da su dinga siyan kaya masu “inganci” da gyara su in sun barke a maimakon sayen sabbi.

Refashion, wata kungiya da aka bukaci da kafa wannan tsari, ta ce an sanya kaya biliyan 3.3 a kasuwa da suka kunshi kayan sawa da takalma a bara a Faransa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai ba kowa ne ya ji dadin yadda gwamnatin ta kawo wannan sauyin ba.

Kungiyoyin 'yan kasuwa sun yi gargadin cewa hakan ka iya zama "tsangwama" a kan wani ɓangare mai muhimmanci na kamfanoni a Faransa, yayin da dan takarar jam'iyyar Republican Eric Pauget ya koka da cewa gwamnatin ta riga ta shiga cikin bashin Yuro tiriliyan 3 kuma ya kamata "ɓarnatar da ku da den gwamnati".

Wani mai ruwa da tsaki a ɓangaren haɗa tufafi, Pascal Morand ya damu game da tasirin wannan matakin a kan kaya masu tsada da wasu kamfanoni ke samarwa.

Wani bangare na shirin Faransa na kawo gyara a bangaren ado ya haɗa da gindaya sharuɗɗan bayanan da ake sanyawa na tufafi daga ranar ɗaya ga Janairun 2024.

A karkashin sabbin dokokin, masana'antun za su lissafo adadin ruwan da ake buƙata wajen haɗa sutura, da sinadaran da za ayi amfani da su, da sinadarai masu roba da kayan za su iya fitarwa da kuma ko akwai wani kayan da aka sake sarrafawa wajen haɗa tufafin.

Masana'antar kayan ado tana ɗaya daga cikin manyan abubuwan dogaro a Faransa, wanda ya samar da kusan Yuro biliyan 66 a kasuwa a bara da dubunnan guraben ayyuka.

Ko da yake Faransa ita ce ta huɗu mafi girma Tarayyar Turai wajen fitar da kayan ado, masana'antar ta yi ƙasa a cikin 'yan shekarun baya-baya nan.