Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kofin duniya na mata 2023: Super Falcons tana rukuni na biyu
Najeriya tana rukuni na biyu da ya hada da Australia da Jamhuriyar Ireland da Canada a gasar kofin duniya ta mata a 2023 da za a yi a Australia da New Zealand.
Wannan shi ne karon farko da Jamhuriyar Ireland za ta buga gasar, tana kuma rukuni tare da wadda ta lashe Olympic wato Canada.
Ingila wadda ta lashe gasar nahiyar Turai za ta fafata da Denmark da China a rukuni na hudu tare da ko dai Senegal ko Haiti ko kuma Chile.
Za a fara wasan daga 20 ga watan Yuli zuwa 20 ga watan Agustan 2023.
Za a yi bikin bude gasar a Auckland, New Zealand, sannan a yi bikin rufe wasannin a Australia a birnin Sydney.
Tawagogi 32 ne za su kece raini, kenan an samu kari daga 24 da suka kara a Faransa a gasar kofin duniya a 2019.
Cikin tawagogi 32, biyar daga ciki za su buga gasar kofin duniya a karon farko da suka hada da Morocco da Philippines, da Jamhuriyar Ireland da Vietnam da kuma Zambia.
Yadda aka raba jadawalin
Group A: New Zealand, Norway, Philippines, Switzerland
Group B: Australia, Republic of Ireland, Nigeria, Canada
Group C: Spain, Costa Rica, Zambia, Japan
Group D: England, wadda ta ci wasan cike gurbi a rukunin B, Denmark, China
Group E: USA, Vietnam, Netherlands, Wadda ta ci cike gurbi a rukunin A
Group F: France, Jamaica, Brazil, Wadda ta ci cike gurbi a rukunin C
Group G: Sweden, South Africa, Italy, Argentina
Group H: Germany, Morocco, Colombia, Korea Republic