Kotun daukaka kara ta kori Goodswill Akpabio a matsayin dan takarar sanata na APC

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da wata babbar kotun tarayya a birnin ta yanke inda ta cire Godswill Akpabio a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso yamma a Majalisar Dattijai.
Hukuncin kotun wanda alkalai uku suka yanke da mai shari''a Danlami Senchi ya karanta a ranar Litinin ya ce Akpabio ya gaza gabatar da shaida a cikin lokacin da doka ta tanada.
Alkalan sun kuma ce, kasancewar Akpabio, dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC, ba zai iya shiga sahihin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 27 a watan Mayu ba wanda aka yi a gaban jami'an hukumar zabe mai zaman kanta inda aka gabatar da Udom Ekpoudom a matsayin dan takarar jam’iyyar.
A hukuncin da wata babbar kotun tarraya da ke Abuja ta yanke a ranar 22 ga watan Satumba ta nemi hukumar ta INEC ta mayar da Sanata Akpabio a matsayin dan takarar jam’iyyar ta APC, a matsayin dan takarar da ta tsayar a zaben fid-da-gwani karo na biyu da aka yi a ranar 9 ga watan Yuni.
Abin da Kotu ta ce a hukuncin farko
A hukuncin da wata babbar kotun tarraya da ke Abuja ta yanke a ranar 22 ga watan Satumba ta nemi hukumar INEC ta mayar da sanata Akpabio a matsayin dan takarar da jam’iyyar ta APC ta tsayar a zaben fid-da-gwani karo na biyu da aka yi a ranar 9 ga watan Yuni.
Kotun ta umurci INEC a kan ta karbi tsohon ministan ma’aikatar Neja Delta a matsayin dan takarar jam’iyyar APC.
Kotun ta kuma umarci INEC da ta wallafa sunan Akpabio a matsayin dan takarar sanata mai wakiltar mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma na Jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023 inda ta bayyana cewa hukumar ta aikata ba dai-dai ba da ta ki karbar tare da buga sunan tsohon gwamnan a lokacin da APC ta manta sunansa a matsayin dan takararta.
Mai shari'a Emeka Nwite da ya yanke hukuncin ya ce an zabi Akpabio bisa ka'ida a matsayin dan takarar jamiyyar APC da ke wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a Majalsar Dattijai a zaben fid-da-da-gwani da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya shirya a ranar 9 ga watan Yuni 2022.
Alkalin ya ce INEC ta yi kuskure da ta amince ta sa ido a kan yadda aka gudanar da zaben na fid-da-gwanin da aka yi a ranar 27 ga watan Mayu wanda wani bangare na jam’iyyar ya gudanar karkashin jagorancin Augustine Ekanem domin nuna adawa da zaben fid-da-gwani da aka yi a ranar 9 ga watan Yuni da aka dora wa kwamitin gudanarwa na jamiyyar APC wato NWC alhakin gudanarwa.
Wannan hukuncin ne ya sa Udon Ekpoudom ya garzaya kotun daukaka kara kuma a yanzu kotun ta umarci INEC da ta amince da Ekpoudom a matsayin sahihin dan takarar kujerar sanatan mazabar.











