Mun samu rahoton take haƙƙin ɗan'adam 106,604 a Najeriya a watan Yuni kaɗai – NHRC

'Yan fafutikar kare haƙƙi a Najeriya

Asalin hoton, NHRC

Bayanan hoto, Irin wannan rahoton da hukumar ta samu a watan Fabrairu ƙorafi 1,484 kawai ta samu

Hukumar Kare Haƙƙi ta Ƙasa a Najeriya ta ce ta karɓi jimillar ƙorafi 106,604 da suka danganci take haƙƙi a watan Yunin 2024 kaɗai.

Hukumar ta bayyana rahoton a matsayin "abin damuwa kuma wanda ba ta taɓa gani ba", tana mai cewa yankin arewa ta tsakiyar Najeriya ce kan gaba da da lamurra 29,462.

Da yake gabatar da rahoton wata-wata karo na shida ga manema labarai ranar Litinin, Babban Sakatare Dr Tony Ojukwu ya ce sun samu rahotonnin kisan taron dangi, da satar mutane, da ayyukan ƙungiyar asiri a johohin Bauchi, da Katsina, da Neja, da Kaduna, da Filato, da Borno, da Binuwai, da kuma Edo.

"CIkin wata shida da suka wuce, alƙaluma sun nuna mana yadda haƙƙin ɗan'adam ke cigaba da lalacewa a Najeriya," in ji shi.

Da yake fayyace alƙaluman, babban mai bai wa hukumar shawara Hillary Ogbonna, ya ce yankin kudu maso kudu ne na biyu a yawan aikata tauye haƙƙin, inda aka samu 21,603.

Haka nan a cewarsa, an samu tauye haƙƙin ɗan'adam sau 18,458 a yankin kudu maso yamma, da kuma 15, 101 a arewa maso yamma, sai 12,907 a arewa maso gabas, yayin da aka samu mafi ƙaranci a kudu maso gabas da 9,164.

Mista Ogbonna ya ƙara da cewa sun samu badaƙalar jefar da yara 1,667, sannan sun samu ƙoranfin fyaɗe 58, da kuma cin zarafi ta hanyar lalata a gida da waje sau 600 cikin watan na Yuni.

Bayanan bidiyo, Haƙƙin ɗan'Adam biyar da ya kamata ku sani

Me ya sa aka samu hauhawar alƙaluman?

An kafa hukumar National Human Rights Commission of Nigeria (NHRC) ne bisa dokar kare haƙƙi ta 1995 (wadda aka yi wa kwaskwarima), kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bai wa mambobinta umarni.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Aikin hukumar shi ne tabbatar da 'yan ƙasa sun samu 'yancinsu, da wayar da kai, da gudanar da bincike, da kuma yin yekuwa kan kare haƙƙi.

Takan fitar da rahotonni na wata-wata game da halin da 'yancin ɗan'adam ke ciki a Najeriya, yayin da take da ofisoshi a duka jihohin ƙasar 36 - har da Abuja.

Irin wannan rahoton da ta fitar na watan Fabrairu ya samu lamurra 1,484 ne kacal idan aka kwatanta da 106,604 a watan Yuni.

"Alƙaluman na tabbatar da irin tasirin da ayyukanmu na haɗin gwiwa ke da su wajen kare haƙƙin ɗan'adam kuma ana iya danganta hauhawar lamurran da yawan wayar da kai da ofisoshinmu ke yi a faɗin jihohi 36," in ji Tony Ojukwu sakataren hukumar.

Ya ƙara da cewa: "Tattara alƙaluman kan haska mana irin cigaba da aka samu ko kuma ƙalubalen da ake da su.

"Ta hanyar gano matsaloli da lamurra, mun samu damar tsara ayyukanmu da zimmar shawo kan matsaloli, wanda hakan ya sa muka ƙara samun kyakkyawan sakamako a al'ummarmu."

A cewarsa, ƙaruwar alƙaluman kansu "darasi ne".

"Ƙaruwar da aka samu abin damuwa ce amma ba abin mamaki ba ne. Hakan shaida ce ta irin jan aikin da muke yi," a cewarsa.

Alƙaluman na da tayar da hankali - Amnesty International

Ƙungiyar kare haƙƙi ta duniya Amnesty International ta siffanta gagaruman alƙaluman a matsayin "masu tayar da hankali".

"Waɗannan alƙaluma da hukumar gwamnatin Najeriya ta fitar abin tayar da hankali ne, amma abu ne da kowa ya sani muna fama da cin zarafi tsakanin ma'aurata, da na jami'an tsaro, da sauransu," in ji Isa Sanusi shugaban ƙungiyar a Najeriya.

Ya ƙara da cewa ba lallai sai gwamnati ce za ta kawo ƙarshen matsalar ba.

"Ya kamata mutane su tabbatar suna gudanar hulɗa da junansu cikin adalaci da kuma gaskiya."

To ta yaya za a shawo kan matsalar?

Isa Sanusi ya ce: "Duk inda aka ga zalinci komai ƙanƙantarsa a yaƙe shi. Idan ba haka ba, to ba ka san wane ne zai zo ya zalince ka ba wata rana kai ma duk ƙarfinka, duk ikonka.

"Idan ma mulki ne da kai wata rana zai ƙare kuma ka dawo kamar kowa. Don haka dole ne a tashi a yi maganin matsalar."