Wani alƙali ya nemi Luis Rebiales ya bayyana gaban kotu

.......

Wani alƙali a Sifaniya ya nemi tsohon shugaban hukumar kwallon ƙafa ta ƙasar Luis Rebiales ya bayyana gaban kotu, kan sumbatar da ya yi wa kyaftin ɗin tawagar ƙasar ta mata Jenni Hermoso a Kofin Duniya.

Mista Rubiales ya kamo kan Hermoso ya sumbace ta lokacin da ake gabatar da kyauta ga Sifaniya da ta yi nasara kan Australia.

Ta ce ita ba “izininta” ya yi mata wannan sumba, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa da ta musanta alaƙa da shi.

Alƙalin ya ce akwai cikakkun shaidu da za su iya sa a ci gaba da sauraron shari’ar.

Yayin sauraren ƙarar a babbar kotun da ke Madris, alƙalin ya bayyana sumbar a matsayin wadda ba a “amince da ita ba”.

.......

Masu gabatar da ƙara sun tuhumi Mista Rubiales da cin zarafi ta hanyar lalata da tilastawa.

Hukuncin irin wannan sumba ya fara ne daga tara mai yawa zuwa zaman gidan yari na shekara hudu.

Lamarin ya hada da mutane da dama da ke cikin harkokin kwallon kafa na Sifaniya, ciki har da tsohon kocin Hermoso, tsohon manajan kasuwanci da kuma mai lura da wasanni na tawagar maza.

An zargi Jorge Vilda da Rubén Rivera da kuma Albert Luque da tilastawa Hermoso ta fito bainar jama’a ta ce da saninta aka yi mata sumbar.

Lauyoyin da ke cikin shari’ar na da kwanaki 10 ne kacal domin su shigar da buƙatar sauraren ƙarar gaban kotu.

A shaidar da ta bayar gaban kotu a watan Janairu, ta ce ya yi mata ne kwatsam ba tare da saninta ba.