Dokar jefar da jarirai a Namibia: Ina son wanda zai lura da jaririna yadda ya dace

Asalin hoton, Getty Images
Tsintar gawar wata jaririya da aka ajiye a bayan wata makaranta a Windhoek babban birnin Namibia a watan Nuwambar da ya gabata ta nuna sauya doka kawai ba zai samar da abin da ake so ba wajen shawo kan matsalar.
A 2019, Namibia ta yi dokar da ke cewa duk matar da ta jefar da ɗanta saboda damuwar rayuwa ba za a gabatar da ita ba a gaban kotu.
An samar da wuraren da ya kamata a kai jarirai da iyayensu suka jefar da su, amma da alamar har yanzu akwai buƙatar wayar da kan mutane kan hakan.
Shekara biyu bayan nan, Linda wata da muka sauya sunanta ta yi amfani da irin waɗannan wurare wajen rainon ‘yarta.
Linda ta riƙa kuka lokacin da take magana kan 'yarta da ta haƙura da ita.
“A matsayina na uwa matakin da na ɗauka ba mai sauƙi ba ne, in ɗauki ‘yata na kai na ajiye a wani wuri.
Amma na zaɓi yin hakan ne saboda yanayin da na tsinci kaina ciki,” in ji Linda cikin wata murya mai taushi.
Ta ma yanke ƙaunar sake haihuwar wata yarinyar.
Linda na zaune ne da ‘ya’yanta da kuma saurayinta a wani ɗan ƙaramin wuri a yankin Swakopmund da suke zaune ba bisa ƙa’ida ba.
Sau da yawa ma ba ta iya cin abinci, kuma ta ce sauran 'ya'yanta huɗu na fahimta idan “mahaifiyarsu ba ta da abin da za ta ba su, ba za mu ci komai ba yau”.
Ta ƙara da cewa: “Amma na biyar ɗin idan babu abinci, ba zai fahimta ba. Sai na ga ya kamata na haƙura da wannan jariri ga wanda zai iya kula da shi yadda ya kamata.”
Linda na cikin ɓacin rai amma ta yi imanin wannan ne abin da ya dace ta yi wa ɗanta.
“Ina kewarsa saboda na shayar da shi na kimanin kwanaki uku, amma na san yana nan ƙalau, yana tare da mutanen kirki.”
'Uwa mai daɗi'
Dalilin da ya sanya hankalinta ya kwanta da inda jaririnta yake shi ne barin shi da ta yi a cikin wata akwatin jarirai jikin wata katanga a Swakopmund akwai katifa da bargo.
Ta kuma ajiye wata wasiƙa a wajen.
“Uwa mai daɗi ..... ka sani ba za mu yanke maka hukunci ba,” ka karanta saƙon da ke nuna yana da uwa.
“Ba za mu iya fahimtar yanayin da ya janyo aka kawo ka nan yankin ba,” ta ƙara da cewa.
Wani saƙo da gidauniyar Ruach Elohim ta wallafa, aka maƙala shi a Swakopmund a matsayin saƙon ga jariran da za su tsinci kansu a nan.
“Mun samu wannan ɗan ƙaramin a jiya,” in ji Peters da ke rungume da wani ƙaramin jariri.
“Kwanan shi huɗu da haihuwa. har yanzu ko suna ba mu sa masa ba, saboda aiki ya mana yawa.”

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ita ce ta assasa gidauniyar da ke samar da akwatin da ake sanya jariran, kuma akwai irin wannan wuri a wurare da dama a faɗin duniya.
Akwatin wadda ita kaɗai ce a Namibia, wata hanya ce da iyaye mata kan kai jariransu, musamman sabbin haihuwa.
Su sanya su a cikin akwatin ba tare da bayyana kansu ba domin a kula da su yadda ya kamata.
Dama akwai wajen tun kafin a sauya dokar, amma Mrs Peters na fatan sake buɗe wasu wuraren a cikin ƙasar a wasu yankunan.
Ko da yaushe aka sanya jariri cikin akwatin Mrs Peters da tawagarta da suke aiki tare suna jin sakon haka a wayoyinsu sai su garzaya domin ɗauko shi.
Uwar na da kwana 30 domin ta nemi a dawo mata da ɗanta da zarar ta sauya shawara.
“Idan kwana 30 ɗin ya wuce ba ta je ba, kawai muna ƙaddara cewa ta gamsu da matakin da ta ɗauka.
Sai a yi wa jaririn rijista a matsayin wanda za a raina a Namibia,” in ji Mrs Peters.
A jikin bangon gidan akwai wani ƙaton allo da ke ɗauke da hotunan jariran da kuma ranakun da aka kawo su.
Nikolai da Miracle da Gabriel da kuma Joshua suna cikin hotunan da muka maƙale.

Akwatin da ake sanya yaran wata hanya ɗaya ce da ake iya kai yara gidan, tun bayan buɗe shi sama da shekara huɗu, jarirai 10 kawai aka ajiye a wajen.
Duk da wannan sabuwar dokar da aka sauya, har yanzu ana kai jariran wuraren da babu aminci a ajiye su.
Alƙaluman da ‘yan sanda suka fitar sun nuna cewa daga 2018 zuwa 2022 an jefar da jarirai kusan 140 a faɗin kasar – sama da waɗanda aka kai wuraren da ke da aminci, wannan adadi ne mai yawa ga ƙasar da yawan jama’arta ba su fi miliyan biyu da rabi ba.
Mrs Peters na fatan a samu ƙarin mutane da za su san yadda ake amfani da wannan akwatu.
“Dole a sanar da iyaye cewa kina da damar ki kai jaririnki wajen, ba tare da cutarwa ba a wuri mai kyau, ba kuma tare da kowa ya san hakan ba, idan hakan suke so.
“Duk lokacin da na ji an ce an yar da jariri sai na ji ba daɗi, Ina jin kamar laifina ne, saboda ban yi aikin wayar da kan mutane ba yadda ya kamata.”
‘Ina fatan zai yafe ni’
Talauci na ɗaya daga cikin dalilan da suke sanyawa iyayen ke jin ba za su iya kula da 'ya'yansu ba kamar dai abin da ya faru a kan Linda.
Amma wasu na barin jariran nasu ne saboda sun yi ƙanƙanta su lura da su, ko kuma an yi musu fyaɗe ne suka haifi yaran.
Ko mahaifin ya tsere ya bar ta da yara in ji Donata Tshivoro, wadda ke lura da ayyukan shafukan sada zumunta a ma’aikatar mata.
Jefar da yaran da ake yi, ya samu sauyin fasali ne a 2019, kuma dokar da aka ƙirƙira ta ƙara wa iyaye ƙwarin gwiwar kai ‘ya’yansu irin wuraren nan masu aminci.
Kamar zuwa asibiti da ofishin ‘yan sanda da kuma irin akwatinan nan.
Bai kamata ɗan da bai san komai ba a watsar da shi ko a ci mutuncinsa ba.
Matukar an miƙa jariri irin wuraren nan to za a miƙa shi ga masu aikin taimako.
Mercia Chingwaramusee, mai irin aikin taimakon ta ce duk da dokar da aka ƙirƙira har yanzu ana nuna “tsangwama da tsoro idan mutane suka gano cewa za ka ajiye jaririnka ne a irin waɗannan wurare.”
Sai dai ta ce, wayewa ce ga iyayen da suka fahimci ba za su iya ɗaukar nauyin ‘ya’yansu ba, su kai su irin waɗannan wuraren domin a lura da su daidai yake da “ka bayar da damar rayuwa gare shi”.
Hukumomi sun amince da cewa har yanzu ana buƙatar a ƙara ƙoƙari saboda wayar da kan mutane su fahimci irin gidajen nan da kuma aikin da suke yi saboda rage mutuwar jarirai.
“Muna magana a radiyo, da harsuna daban-daban, muna zuwa makarantu, muna bin ƙauyuka mu tattauna da su, in ji Tshivoro.
Yayin da aka samu irin wuraren da ake ajiye irin waɗannan yara maimakon jefar da su, yanzu mutane irin su Linda za su rage shiga damuwa.
“Ina roƙon Allah in ɗana ya ta shi ya gafarce ni,”in ji ta, “ko kuma wata rana ya dawo gare ni.”










