Yadda faɗa-a-jin Ƙasashen Yamma ke daɗa raguwa a Afirka

Brics

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, BRICS
    • Marubuci, Daga Andrew Harding
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Johannesburg

Wani yanki mai faɗin murabba'in mil ɗaya na hamshaƙan masu kuɗi a Afirka, na karɓar baƙuncin wani babban taron ƙoli na ƙasashen duniya a wannan mako cike da shauƙin alfahari da sararawa da kuma 'yar dugunzuma.

Sandton - lardin hada-hadar bankuna mai matuƙar ɗaukar ido a wajen birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu - wuri ne na taron ƙungiyar ƙasashe masu haɓakar tattalin arziƙi da aka yi laƙabin Brics.

Ƙungiyar ta ƙasashe masu dogon buri, da ba ta da fayyatacciyar siga ta ƙunshi ƙasashen (Brazil da Russia da India da China da kuma Afirka ta Kudu), da suka haɗu a kan muradin ƙalubalantar babakeren da suke jin Ƙasashen Yamma sun yi cikin al'amuran duniya.

Gomman sauran ƙasashe ne, su ma suka kafa layi da niyyar shiga ƙungiyar.

Ana iya fahimtar jin raguwar fargabar da aka shiga a nan Afirka ta Kudu daga shawarar Shugaba Vladimir Putin a baya-bayan nan ta janye jiki daga taron na ƙungiyar ƙasashe masu haɓakar arziƙi.

Idan ya kafe cewa sai ya zo, a ƙarshe sai Afirka ta Kudu ta fayyace matsayinta a kan ko za ta iya aiwatar da nauyin kasancewarta cikin ƙungiyoyin ƙasashen duniya, wajen kama shugaban na Rasha bisa zargin aikata laifukan yaƙi a Ukraine.

Tsame su daga wannan ƙalubale mai rikitarwa, jami'an Afirka ta Kudu a yanzu suna cike da zumuɗi a matsayinsu na masu karɓar baƙi - cike da alfahari suna gayyatar 'yan jarida zuwa tarukan karin kumallo da baje-kolin kayayyaki da musayar ra'ayoyi na mahalarta taron ƙolin Brics.

Wannan irin ɗokin ba sabon ba daga jami'an gwamnati yana fitowa ne, ga wasu masu lura da al'amura, domin haska tsananin yadda wannan ƙasa ga alama take zame jiki daga kusurwar Ƙasashen Yamma cikin sauri, ba kawai zuwa wata duniya mai ƙarin turaku birjik ba, amma zuwa ga China da kuma kaɗan ga alƙiblar Rasha.

Brics

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ana sa ran Shugaban Rasha zai halarci taron ƙolin ta intanet
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayin wata ganawar ministocin harkokin waje kafin taron ƙolin Brics a birnin Cape Town, wani ɗan jaridan Rasha ya kwanto kusa da Ni a lokacin taron manema labarai inda ya ce: "Kuna iya riƙe alƙaryarku ta 'yancin ɗan'adam (a can Yamma). Mu dai za mu sake fasalin duniya."

Mai yiwuwa har yanzu ƙungiyar Brics tana matsayin jaririya ne, amma tana yunƙuro da - aƙalla a wasu wuraren - wani kuzari da tsimar jiki na haƙiƙa da katse al'amura.

Wani abokin aiki da ya halarci wani taron ƙarawa juna sani kan manufofin hulɗa da ƙasashen waje wanda gwamnatin Afirka ta Kudu ta shirya ya faɗa min cewa rinjayen tunanin mutane a can shi ne China ce matattara a zamanin gobe kuma Ƙasashen Yamma na samun koma-baya.

To nan ne inda rabuwar hankalin Afirka ta Kudu ya shigo cikin lissafi.

Shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa - hamshaƙin ɗan kasuwa - yana cike da masaniyar cewa tattalin arziƙin Afirka ta Kudu wanda annobar korona ta gigita kuma yake fama da alƙaluman rashin aikin yi mafi girma da na rashin daidaito, ido-rufe yana buƙatar ƙarin masu zuba jari daga ƙetare, matuƙar ana son ta kuɓuta daga matsalar da ke ta hauhawa.

Rasha dai tabbas, ba ita ce mafita ba. Hulɗar kasuwancinta da Afirka ta Kudu kusan akwai-ya-babu ne. China tana ƙara zama muhimmiyar abokiyar hulɗa amma, duk da haka, ba ta kama ƙafar daɗaɗɗiyar hulɗar kasuwanci da kuma harkokin zuba jari daga Tarayyar Turai da Amurka ba.

To me ya sa Afirka ta Kudu za ta jefa waɗannan muhimman harkoki - waɗanda da ma sun riga sun yi rauni, da Ƙasashen Yamma cikin hatsari - a lokacin rashin tabbas na tattalin arziƙi da ya ta'azzara?

Amsar dai, aƙalla a wani ɓangare, ga alamu tana tattare da jam'iyya mai mulki da ke daɗa nuna tsananin gajiya kuma ba ta tafiya daidai.

Bayan kwashe tsawon shekara talatin a kan mulki, jam'iyyar ANC na faɗi-tashin raba kanta da rigingimun cikin gida da cin hanci da kuma hargitsin gudanar da al'amuran mulki.

Ganin yaƙin Yukren ya sha gabanta, alal misali, gwamnatin Afirka ta Kudu ta gabatar da martani irin na wadda ruwa ya ci - da farko ta yi tofin Allah tsine ga mamaye, daga nan cikin kakkausar murya ta ƙi yin Allah-wadai, sai kuma ta koma ta soki Nato, ta koma tana yabon Mista Putin, tana gabatar da kanta a matsayin mai sulhuntawa, ta karɓi baƙuncin atisayen sojojin ruwan Rasha, ta garzaya kuma Washington tana bayani game da matsayinta, lokaci-lokaci kuma tana jefo kalaman fadar Kremlin na neman magana.

Daga nan kuma sai ga batun da ya daɗe har zuwa yanzu yana ɗaure kai, na ko Afirka ta Kudu ta yi ssfarar makamai ga Rasha a bara - kamar yadda Amurka ta yi zargi.

Akwai 'yar tantama cewa Shugaba Ramaphosa ya kasa tsaye ya kasa zaune game da mamayen Rasha kuma yana alla-alla ya nuna kansa a matsayin wayayye kuma mai da'awar shiga tsakani don tabbatar wata duniya mai turaku da yawa.

Sai dai gwamnatinsa da jam'iyyar a kai a kai suna shatale wannan matsayin - sau da yawa suna kafa hujja da tuna goyon bayan da Rasha ta bayar a lokacin gwagwarmayar yaƙi da mulkin wariyar launin fata da kuma zargin da mafi yawa ke yi wa manufar hulɗa da ƙasashen wajen Amurka.

Saƙon da aka fitar da shi a hargitse ya yi ƙoƙari wajen ɓata ran kowanne ɓangare a rikicin sannan ya yi nasara kawai wajen nuna Afrika ta Kudu a matsayin ƙasa mai rauni kuma wadda ba tsaida shawara ba.

"Ƙasa mai launin bakan gizo" ta Nelson Mandela tabbas a yanzu tana cikin wani hali - har ma wasu na gargaɗin cewa nan gaba kaɗan za ta iya zama "kasasshiya".

Brics

Asalin hoton, BRICS HANDOUT/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Afirka ta Kudu na zumuɗin kasancewa ƙirjin biki a matsayinta na mai karɓar baƙuncin taron Brics da za a kammala ranar Alhamis

Sai dai taron Brics na wannan mako, ba kamar yadda aka saba ba, zai bai wa fadar Kremlin wata ƙwaƙƙwarar dama ta bayyana nata, ingantaccen tsarin diflomasiyya da ya sha gaban duk wani wanda ake da shi.

Batun juyin mulkin Nijar ne ya mamaye kanun labaran da ke fitowa daga nahiyar, da kuma damar da sojojin hayar Wagner na 'yan bangar Rasha masu neman ta-faɗi gasassa da ke neman hanyar ci da gumin wani hargitsi za su iya samu, don amfanin kansu kamar yadda tuni suka yi a Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.