'Yadda Putin ke son ya ci gajiyar yaƙin Isra'ila da Gaza'

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Steve Rosenberg
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan BBC na Rasha
Abin kwaɗaitarwa ne, a riƙa ayyana Vladimir Putin a matsayin wani mugu, irin na cikin fina-finan James Bond, zaune a gaban wani ƙaton faifan sarrafa kwamfuta, idonsa kuma na kan majigin da ke jikin bango a wata maɓoyar ƙarƙashin tsauni.
Yana tsara abubuwan da za su hargitsa ƙasashe a faɗin duniya.
Ya latsa wani madannin kwamfuta, sai ga rikici ya ɓarke a yankin Balkans.
Ya sake latsa wani madannin sai Gabas ta Tsakiya ta fashe.
Abin kwaɗaitarwa ne… sai dai mai yiwuwa ba gaskiya ba ne. Yana zuzuta irin ƙarfin faɗa-a-ji a duniya, da shugaban na fadar Kremlin yake da shi.
E, gaskiya ne Rasha tana da alaƙa da Hamas kuma ta zama abokiyar ƙawancen Iran ta ƙuƙut. A cewar Amurka, shugabannin Moscow da Teheran a yanzu sun ƙulla cikakken ƙawance kan sha'anin tsaron ƙasa.
Sai dai hakan ba ya nufin Rasha tana da wani hannu kai tsaye a ciki, ko wata masaniya kafin aukuwar harin da Hamas ta kai wa Isra'ila.
"Ba mu yarda Rasha na da hannu a ciki ta kowacce irin hanya ba," jakadan Isra'ila a Moscow, Alexander Ben Zvi, ya faɗa wa jaridar Kommersant cikin wannan mako.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ƙara da cewa "shashanci ne tsagwaro" a riƙa tunanin akwai hannun Rasha a cikin wannan aika-aika da Hamas ta aikata a Isra'ila.
"Ban ga wata shaida ba kai tsaye cewa Rasha ta samar da makamai ga Hamas, ko kuma rundunar sojin Rasha tana horas da mayaƙan Hamas," cewar Hanna Notte, wata ƙwararriyar masaniya kan al'amuran da ƙasar Rasha da Gabas ta Tsakiya da ke zaune a birnin Berlin a Cibiyar James Martin kan Nazarin Kawar da Bazuwar Makamai.
"Gaskiya ne cewa Rasha na da daɗaɗɗiyar dangantaka da Hamas. Rasha ba ta taɓa ayyana Hamas a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda ba. Jami'an Hamas sun je Moscow bara har ma da bana.
"Amma ba zan yanke hukunci daga hakan ba, cewa akwai gagarumin taimakon soji a tsakani. Duk da yake, mun sani makaman da Rasha ta ƙera sun shiga Zirin Gaza, mai yiwuwa ta Sinai [a Masar] kuma da taimakon Iran."
A wani ƙaulin kuma, Shugaba Putin bai latsa wani madanni da aka yi wa alamar "yaƙin Gabas ta Tsakiya" ba.
Amma ko yana da shirin ya ci gajiyar sa?
Wannan tabbas ne, Ga yadda abin yake.
Karkatar da hankula daga Ukraine
Da ƙaruwar tarzoma a Gabas ta Tsakiya, wadda ta kankane tsare-tsaren kafofin labaran duniya, Moscow ta mayar da hankali wajen ganin gawurtaccen kanun labarai daga Isra'ila domin ya karkatar da hankula daga yaƙin da Rasha take yi a Ukraine.
Sai dai wannan abu ne zarce sauyin labaran da aka saba ji ba ne. Hukumomin Rasha kuma suna fatan cewa, sakamakon wannan lamari na Gabas ta Tsakiya, wasu makaman da Ƙasashen Yamma ke bai wa Ukraine za su karkata zuwa Isra'ila.
"Na yi imani wannan rikici kai tsaye zai yi tasiri wajen sauya alƙiblar aikin sojoji na musamman [a Ukraine]," jami'in diflomasiyyar Rasha Konstantin Gavrilov ya faɗa wa jaridar Izvestia mai goyon bayan gwamnatin Rasha.
"Hankalin masu ɗaukar nauyin Ukraine zai karkata zuwa yaƙin Isra'ila. Wannan ba yana nufin Ƙasashen Yamma za su juya wa Ukraine baya ba ne. Amma dai yawan taimakon kayan aikin soji zai ragu….kuma alƙiblar faɗan na iya matuƙar juyawa ga ribar [Rasha] ."
Tunanin abin da ba zai yiwuwa ba daga Rasha? Tabbas mai yiwuwa ne.
"Za mu iya kuma muna goyon bayan Isra'ila, duk da yake muna tare da Ukraine," a cewar Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin yayin wani taron ministocin tsaron ƙungiyar Nato.
Sai dai tsawaitaccen rikicin Gabas ta Tsakiya zai jarraba ƙarfin jimirin Amurka na tallafa wa manyan abokan ƙawance biyu a mabanbantan yaƙe-yaƙe guda biyu lokaci ɗaya.
Rasha ce mai shiga tsakani?
Rasha tana ƙoƙarin bunƙasa matsayinta a Gabas ta Tsakiya ta hanyar fito da kanta a matsayin mai yiwuwar samar da zaman lafiya.
Tana kan wannan matsayi kafin yanzu, inda ta shiga ƙoƙarin ƙasashen duniya wajen kawo ƙarshen rikici a yankin.
"Rasha na iya yi kuma tana iya ba da gudunmawa wajen sulhunta [rikicin]," in ji Dmitry Peskov, mai magana da yawun Shugaba Putin. "Muna ci gaba da tuntuɓar ɓangarorin da ke cikin rikicin."
A yayin wata ziyara da ya kai Moscow cikin wannan mako, Firaministan Iraƙi ya yi kira ga Shugaba Putin ya fito ya ba da "sanarwa ta wata tabbatacciyar yarjejeniyar tsagaita wuta" a yankin.
Rasha da kawo zaman lafiya? Da wuya a yarda.
Ko ba komai fa, wannan ita ce ƙaddamar da cikakkiyar mamaya a kan maƙwabciyarta. Bayan kusan wata ashirin yaƙin Rasha a Yukren ya haddasa mutuwa da ruguje-ruguje masu tarin yawan da har suka ɗimauta duniya.
Kuma, faɗar ku "za ku iya kuma za ku taka rawa" wajen cimma zaman lafiya, ba tabbaci ba ne cewa waɗanda rikicin ya shafa, za su karɓe ku a matsayin masu shiga tsakani.

Asalin hoton, Reuters
Tun da daɗewa Rasha tana da wani muradi a Gabas ta Tsakiya, inda Tarayyar Sobiyet amince da wani matsayi na nuna goyon baya ga Larabawa yayin da Isra'ila ta ƙulla alaƙa ta ƙuƙut da Amurka. Tsawon shekaru masu yawa ƙin jinin Yahudawa da goyon bayan gwamnati wani tambari ne na rayuwar Sobiyet.
Bayan rushewar Tarayyar Sobiyet, dangantaka tsakanin Rasha da Isra'ila ta inganta, a wani ɓangare saboda kwararar Yahudawa fiye da miliyan ɗaya zuwa Isra'ila daga tsoffin jamhuriyoyin Sobiyet
Sai dai a baya-bayan nan, Rasha ƙarƙashin mulkin Vladimir Putin ta riƙa kusantar abokan gabar Isra'ila, musamman Iran - lamarin da ya dangantaka tsakanin Rasha da Isra'ila ta yi tsami.
Yin tur da Amurka
Fadar Kremlin ta leƙo wata dama a nan ta yin abin da tuni ta sha yi - ɗora laifi kan Amurka.
Tun da Hamas ta kai wa Isra'ila hari, babban saƙon Vladimir Putin shi ne cewa "wannan shi ne misali na gazawar manufar Amurka a Gabas ta Tsakiya".
Ya dace da ɗaukacin salon gwamnatin Moscow na sukar abin da ta kira "babbakewar Amurka".
Kuma nuna Amurka a matsayin babbar mai laifi a Gabas ta Tsakiya wata hanya ce fadar Kremlin ke amfani da ita wajen haɓaka kwarjinin Rasha a yankin.











