Ta yaya ake zaɓen sabon Fafaroma?

Manyan limamai a lokacin da suke shirin zaɓan wanda zai gaji Fafaroma John Paul II a 2005.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wane ne zai zama Fafaroma, kuma wa yake zaɓar sa?

Manyan limami sun halarci taron addu'o'i a majami'ar St Peter's.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manyan limaman ɗarikar katolika suna yin addu'o'i a cocin St Peter's Basilica kafin fara zama don zaɓan Fafaroma

Ana zaɓan sabon Fafaroma ne idan wanda yake kai ya rasu, ko kuma ya yi murabus (kamar yadda Fafaroma Benedict XVI ya yi a 2013).

Wanda ya gaje shi zai zama jagoran mabiya ɗarikar Katolika a duniya.

Za a iya zaɓan duk wani namiji ɗan ɗarikar Katolika da ya kasance mai tsarki don zama Fafaroma.

Sai dai, aikin zaɓan Fafaroman ya rataya ne kan wuyan manyan limamai a cocin na Katolika.

Sun kasance masu zaɓan sabon Fafaroma.

Akwai manyan limamai 252 a faɗin duniya (zuwa Fabrairun 2025), waɗanda kuma suka kasance bishop-bishop. Waɗanda suke ƙasa da shekara 80 ne kaɗai ke da damar zaɓan sabon Fafaroma.

An taƙaita yawan manyan limaman da za su zaɓi Fafaroman zuwa 120, sai dai akwai su 135 da ke da damar yin zaɓen. (Fafaroma Francis ya naɗa sabbin limamai 21 a watan Disamban 2024.)

Ta yaya limamai ke zaɓen sabon Fafaroma?

Manyan limamai cikin majami'ar Sistine lokacin zaɓan wanda zai maye gurbin Fafaroma John Paul II a 2005.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana zaɓan sabon Fafaroma ne a cocin Sistine da ke cikin fadar Vatican

Idan aka zo zaɓen sabon Fafarroma, dukkan manyan limamai na taruwa a fadar Vatican da ke birnin Rome. Wannan wani tsari na zaɓe ne da ake bi, ba a kuma sauya ba tsawon shekaru 800 da suka gabata.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ranar farko ta zaman manyan limaman, suna gudnaar da addu'o'i a majami'ar St Peter's Basilica. Sannan su taru a cocin Sistine da ke cikin fadar Vatican. A can ne ake bai wa kowa umarni.

Daga nan, za a ajiye dukkan limaman a cikin fadar Vatican har sai an zaɓi sabon Fafaroma.

Limaman da ke zaɓen suna da damar kaɗa kuri'a guda a cocin Sistine a ranar farko da aka fara zama. A rana ta biyu ya yi sama kuma, suna kaɗa kuri'u biyu a kowace safiya, sannan wasu kuri'u biyu da rana a cocin, har sai an rage masu neman zama Fafaroman zuwa ɗaya.

A cikin kuri'un, kowane limami yana rubuta sunan ɗan takarar da yake so a takardar kaɗa kuri'a karkashin wani rubutu mai cewa "Eligio in Summum Pontificem" abin da ke nufin na zaɓi sabon Fafaroma. Limaman suna canza salon rubutu ba irin wanda suka saba yi ba domin kuri'un su zama cikin sirri.

Idan ba a samu wanda ya fi yawan kuri'u har karshen rana ta biyu ba, ana ba da rana ta uku domin yin addu'o'i, sai dai ba a kaɗa kuri'a a ranar. Ana komawa jefa kuri'a bayan an gama addu'o'in.

Ɗan takara na buƙatar kashi biyu bisa uku na yawan kuri'un manyan limaman da ke yin zaɓe domin samun damar zama Fafaroma.

Matakin zai ɗauki tsawon kwanaki, wasu lokuta makonni da dama.

Me yake faruwa a zaman zaɓen sabon Fafaroma?

Dandazon mutane a dandalin St Peter's lokacin da suke jiran jin sakamakon zaɓen sabon Fafaroma a 2013.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yayin zaman zaɓen sabon Fafaroma, dandazon mutane na taruwa a dandalin St Peter's domin jiran sakamakon zaɓen

Ana gudanar da zaman zaɓen Fafaroman ne cikin sirri. Babu limamai da zai bar fadar Vatican ba, haka kuma ba za su saurari radio ko kallon talabijin ko karanta jaridu ko kuma yin hulɗa da wani daga waje ba ta hanyar yin waya.

Babu wanda za a bari ya shiga wajen da limaman suke sai ma'aikatan tsaftace fadar da likitoci da kuma wasu ƙananan fastoci. Dukkansu na alkawarin yin komai cikin sirri.

A tsakanin kuri'un, manyan limaman (wanda ya kunshi masu zaɓe da waɗanda suka yi tsufar da ba za su iya zaɓe ba) na shafe lokaci suna tattauna cancantar ƴan takarar.

Babu wanda ake barin ya yi wa wani kamfe a bayyane. Limaman fadar Vatican ɗin na bin ka'idojin da addinin Kirista ya gindaya. Duk da haka, batun tara wa ɗan takara magoya baya wani abu ne da ake alaƙanta shi da siyasa.

Farin hayaki ya turnuke sama daga cocin Sistine, abin da ke nufin an zaɓi sabon Fafaroma (2013)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Idan farin hayaki ya turnuke sama daga cocin Sistine, hakan alama ce da ke nuna cewa an zaɓi sabon Fafaroma

Ana ƙona takardun kuri'a da aka yi amfani da su sau biyu a kowace ranar zaman zaɓen Fafaroma, kuma mutane da ke wajen fadar Vatican za su ga hayaki na fita daga saman cocin Sistine.

Ana saka baki ko farin abu kan takardun. Bakin hayaki na nufin zaɓen bai kammalu ba; yayin da farin hayaki kuma ke nuna cewa an zaɓi sabon Fafaroma.

Me zai faru idan aka zaɓi sabon Fafaroma?

Fafaroma Francis lokacin da yake yi taron jama'a jawabi a dandalin St Peter's bayan zaɓensa a matsayin Fafaroma a 2013

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A al'adance, sabon Fafaroma da aka zaɓa na yi wa dandazon jama'a jawabi a dandalin St Peter's

Da zarar ya lashe kuri'un da aka kaɗa, ana tambayar sabon Fafaroman cewa: "Shin ka amince da zaɓen ka da aka yi a matsayin jagoran ɗarikar Katolika?"

Yana zaɓar sunan da yake son a kira sa da shi a matsayin Fafaroma wanda kuma ya yi daidai da mukaminsa.

Manyan limaman suna yin mubaya'a da kuma alkawarin yin biyayya ga sabon Fafaroman.

Ana yi wa dandazon jama'a a majami'ar St Peter's sanarwar cewa "Mun samu sabon Fafaroma."

Daga nan sai a bayyana sunan sabon Fafaroman, sannan ya bayyana gaban jama'a. Yana yin taƙaitaccen jawabi da kuma saka albarka "ga birnin Vatican da kuma duniya".

Bayan nan, ana nunawa Fafaroman sakamakon kuri'un da aka kaɗa a kowane zagaye.

Sai kuma a saka kuri'un a wani wuri a cikin fadar Vatican a kuma adana su, inda za a buɗe su kawai tare da umarnin Fafaroma.