Waɗanne ƙasashe ne za su fi samun kwararar baƙi a 2025?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Onur Erem
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
Ana ci gaba da samun ƙaruwar ƙaura a duniya duk shekara, kuma babu alamun za a samu raguwar hakan nan gaba.
Sai dai masu yin ƙaura sun samu gagarumin tsaiko a shekarun baya sakamakon matakan da Donald Trump ya ɗauka a lokacin mulkinsa na farko, da kuma matakan taƙaita zirga-zirga da annobar Korona ta haifar da kuma ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai da ta kawo ƙarshen zira-zirga kyauta tsakanin ƙasar da ƙasashen Tarayyar Turai.
Ana kuma sa ran a shekarar 2025, za a samu sauyi a duniya a manyan ƙasashe biyu da aka fi yin ƙaura zuwa can, wato Amurka da Jamus, inda Donald Trump da zai fara wa'adin mulkinsa na biyu a watan Janairu, yayin da a Jamus ake sa ran za a yi zaɓen wuri a watan Fabarairu, inda ake tsammanin jam'iyyun da ke da tsanani kan matakan ƙaura za su iya samun nasara.
Yayin da ake bikin ranar ƙaura ta duniya a ranar 18 ga watan Disamba, mun duba yadda al'amura za su iya sauyawa a 2025.
Wane hali ake ciki kan batun ƙaura a duniya?
Yawan mutanen da suke yin ƙaura a duniya na ƙara ƙaruwa cikin sauri a cikin shekaru talatin.
Sai dai , har yanzu adadin mutanen da ke yin ƙaura daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa ba shi da yawa idan aka kwatanta da yawan al'ummar duniya.
"Mun duba bayanan yin ƙaura na shekara 25, da kuma bayanan cigaban al'umma, inda muka gano cewa, al'ummar ƙasashe masu tasowa na shan wahala wajen yin ƙaura zuwa ƙasashe matsakaita da manyan ƙasashen da suka ci gaba," in ji Marie McAuliffe,shugabar bincike a hukumar kula da masu ƙaura ta Majalisar Dinkin Duniya, {IOM}.
"Akwai alamun da ke nuna cewa ana shan wahala wajen samun damar amfani da hanyoyin yin ƙaura."
"Yawanci ana ƙaura ne tsakanin ƙasashe masu arziƙi, misali kamar Turai, "McAuliffe.
An fi samun yawan yin ƙaura a tsakanin ƙasashen da ake zirga-zirga kyauta kamar ƙasashen Tarayyar Turai da Ecowas da Mercosur, ana kuma samu sosai a tsakanin ƙasashen gabashin Asia da ƙasashen yankin tekun Fasha, in ji McAuliffe.
An samu ɗalibai miliyan bakwai da ke karatu a ƙasashen duniya a 2022, adadin da ya ninku har sau uku idan aka kwatanta da shekaru talatin da suka gabata.
Hamɓarar da gwamnatin Assad a Syria zai ba ƴan Syria sama da miliyan shida damar komawa ƙasarsu.
A bayan hamɓarar da gwamantin, Bashar al-Assad ya tsere zuwa Rasha, ind aka riƙa samun tururuwar ƴan Syria a kan iyakar Turkiyya wadanda ke ƙoƙarin komawa gida.
Sai dai babu tabbas kan ci gaba da faruwar hakan da kuma lamarin tsaro a yankin, saboda rashin tabbas kan makomar ƙasar.
Ta yaya wa'adin mulkin Trump na biyu zai shafi ƙaura a duniya?
Batun ƙaura yana da mahimmanci wajen Donald Trump da kuma muƙarrabansa.
Amurka ita ce ƙasar da aka fi yin ƙaura zuwa can, kuma batun na cikin batutuwan da suka mamaye zaɓen 2016.
"Gina katanga" na daga cikin kalmomin da Trump ya riƙa nanatawa a lokacin yaƙin neman zaɓenshi, inda ya yi alƙawarin tsaurara tsaro a kan iyakar Mexico domin hana shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba.
A mulkinsa na farko, Trump bai yi nasarar dakatar da shigar baƙi ta kan iyakar Mexico ba, sai dai, ya kawo tsaiko, an kuma samu sauƙin masu shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba.
Abu na farko da ya fara yi bayan hawa mulkinsa a watan Janairun 2017, shi ne ya haramta wa ƙasashen Musulmi bakwai, (Iran, Iraq, Libya, Somalia, Sudan, Syria da Yemen) shiga Amurka, matakin da aka kira da na haramta wa Musulmi shiga ƙasar.
Ƴan ƙasashen kusan 2,000 ne Trump ya bada umarnin a tsare bayan sun sauka filin jirgin a Amurka .
Akwai kuma dokar hana bada izinin aiki ga ƴan ƙasashen waje da Trump ya sanya, matakin da ya ce ya yi haka ne domin kare ƴan ƙasar.
Gwamnatin Trump ta kori mutane da dama daga Amurka ciki har da masu neman mafaka.
Kusan mutane 400,00 ne aka tsare daga bisani aka sake su bayan ya bar mulki a watan Janairun 2021.
Me ake tsammanin zai faru a wa'adin mulkinsa na biyu ?

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga cikin manyan alƙawurran da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓenshi na wannan shekarar shi ne, gagarumar korar baƙin da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.
Donald Trump ya ce zai yi amfani da rundunar sojin Amurka wajen cimma burinsa, inda ya ce zai ayyana dokar ta-ɓaci kan baƙin haure.
Mataimakin shugaban ƙasa da Trump ya dauka, JD Vance ya ce za su fara da korar mutane miliyan guda, sai dai masana sun nuna shakku kan yiwuwar hakan.
Masana sun ce korar baƙi miliyan daga ƙasar, za a iya kashe biliyoyin daloli.
Kuma yana da wahala korar baƙin haure ta aiwatar da aikin mutane miliyan daya a lokaci guda, saboda dole ne matakin ya hadu da cikas ta ɓangaren shari'a.
Me zai sauya bayan zaɓen Fabarairun 2025 a Jamus?

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasa ta biyu da aka fi yin ƙaura ita ce Jamus, akwai yiwuwar ta samu sabuwar gwamnati bayan zaɓen watan Fabarairun, 2025.
A shekarun baya-bayan nan dai ƙasar na sauƙaƙa matakan yin ƙaura domin daukar ma'aikata, amma shin hakan zai iya canjawa idan jam'iyyu masu tsattsauran ra'ayi suka samu nasarar ɗarewa mulki?
Gwamnatin ƙasar mai mulki, ta sauƙaƙa matakan yin ƙaura domin cike guiɓin ƙarancin ma'aikata da ake samu a ƙasar, sai dai Firaiminista Olaf Scholz na jam'iya mai mulki wato Social Democratic Party shine na uku cikin ƴan takarar.
"Tsaurara matakan yin ƙaura na cikin batutuwan da suka mamaye yaƙin neman zaɓen jam'iyyun da ke kan gaba musamman CDU/CSU DA KUMA AfD ta masu tsatsauran ra'ayi, " cewar Victoria Rietig shugabar cibiyar lura da harkar ƙaura ta ƙasar Jamus.
Jam'iyyun siyasa a Jamus ba su cika sukar batun ƙaura ba, saboda ƙarancin ma'aikata da ake da su a ƙasar, cewar Rietig.
Ƙarin wasu ƙasashen

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ƙaura zuwa Jamus da Amurka ke fuskantar barazana, akwai yiwuwar wasu ƙasashen ba za su tsaurara matakan shigi da ficensu ba.
Akwai yiyuwar yin ƙaura tsakanin ƙasashen Tarayyar Turai da kuma tsakanin ƙasashen ƙungiyar Ecowas ba za su gamu da ƙalubale ba.
"Akwai yiwuwar za a ci gaba da yin ƙaura daga ƙasashen gabashin Asia zuwa yankin tekun Fasha saboda buƙatar ma'aikata da ake da ita, cewar, Marie McAuliffe ta IOM.
Ta kuma yi ƙarin haske kan cewa akwai wasu bayanan ƙarya da ake yaɗawa kan ƙaura.
"A ganina babban abin da ke haifar da rashin tabbas kan ƙaura shi ne labaran ƙarya da ake yadawa."











