Iyayen da aka ƙwace wa ƴaƴa bayan faɗuwa jarrabawar raino na neman a mayar musu da ƴaƴansu

    • Marubuci, Sofia Bettiza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Lafiya
    • Marubuci, Woody Morris
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, Denmark
  • Lokacin karatu: Minti 6

Lokacin da Keira ta haifi 'yarta a watan Nuwamban da ya gabata, sa'a biyu kawai aka ba ta kafin a ƙwace jaririyar daga hannunta.

"Tana fitowa na fara ƙirga lokaci," in ji Keira mai shekara 39. "Na ci gaba da kallon agogo domin na tabbatar minti nawa za mu yi tare."

Lokacin da za a karɓe Zammi daga hannunta, Keira ta ce ta yi ta kuka ba ƙaƙƙautawa, tana bai wa jaririyar haƙuri.

"Na ji kamar wani ɓangare na jikina ne ya mutu."

Keira na ɗaya daga cikin mazauna Greenland da ke ƙasar Denmark da ke fafautikar ƙwato 'ya'yansu bayan raba su da su.

A irin wannan yanayi, akan raba iyaye da jarirai ko 'ya'yansu bayan yi musu gwajin raino, wanda ake kira FKU a ƙasar, domin tantance ko iyaye za su iya raino da tarbiyyar 'ya'yan nasu ko ba za su iya ba.

A watan Mayun wannnan shekarar gwamnatin Denmark ta haramta amfani da wannan gwajin kan mazauna Greenland bayan shafe shekaru ana sukar lamarin.

Amma duk da haka an ci gaba da yinsa.

Akan yi wa iyayen tambayoyi tare da 'ya'yan nasu, da jarrabawar da ta shafi tunani kamar lissafa wasu lambobi da baya-baya, da kuma tambayoyi game da ɗabi'ar mutum.

Masu kare gwajin na cewa aikinsu ya fi kusa da gaskiya fiye da binciken da jami'an kula da walwalar al'umma ke yi.

Amma masu sukar su na cewa ba zai yiwu su iya hasashen ko iyaye za su iya kula da 'ya'yansu da gaske ko kuma ba za su iya ba.

Sannan sukan ce akan yi wa mutane tambayoyin da harshen ƙasar Denmark maimakon na Kalaallisut, wanda shi mazauna Greenland ke ji, wanda hakan ka iya jawo rashin fahimta.

Mazauna Greenland 'yan ƙasar Denmark ne, wanda hakan ke ba su damar zama da kuma aiki a ainahin ƙasar Denmark.

Yiwuwar ƙwace 'ya'ya daga iyaye 'yan Greenland ta fi yawa sau 5.6 fiye da 'yan ainahin ƙasar Denmark, a cewar cibiyar bincike ta Danish Centre for Social Research, wadda gwamnati ke ɗaukar nauyi.

A watan Mayu gwamnati ta ce tana fatan sake duba lamarin mutum 300 cikinsu har da 'yan Greenland da aka raba su da 'ya'yansu ta ƙarfin tsiya.

Zuwa watan Oktoba, BBC ta gano cewa jarabawar mutum 10 kacal gwamnati ta sake dubawa amma kuma babu wani yaron Greenland da aka mayar wajen iyayensa sakamakon haka.

Sakamakon jarabawar Keira da aka yi a 2024 ya nuna cewa ba ta da "cikakkiyar ƙwarewa ta uwa da za ta iya kula da jaririyar ita kaɗai".

Keira ta ce tambayoyin da aka yi mata sun ƙunshi: Wace ce Mother Teresa?" da kuma "Tsawon wane lokaci hasken rana ke ɗauka kafin ya iso duniyarmu?'

Keira ta ce sun "saka ni yin wasa da 'yartsana kuma suka ce ban yi kokari ba saboda ba ni kallon idonsu sosai".

Da ta tambaya dalilin da ya sa ake yi mata jarabawar a haka, sai masanin tunanin ya ce mata: "Domin a gano ko kina da wayewa sosai, ko za ki iya mu'amala kamar sauran mutane."

A 2014, 'ya'yan Keira biyu - mai shekara takwas da mai wata takwas - an ƙwace su bayan yi mata gwaji a lokacin bisa cewa ƙwarewarta a matsayinta na uwa ba ta ƙaruwa cikin sauri kamar yadda suke buƙata.

Babbar 'yarta Zoe mai shekara 21 a yanzu ta koma wajenta lokacin da take shekara 18, amma yanzu tana zaune a gidanta na kanta.

Keira na fatan za a dawo mata da 'yarta Zammi na har abada.

'Baƙin ciki mai munin gaske'

Amma ba duka mazauna Greenland ne za su samu damar sake duba lamarinsu ba kan jarabawar FKU.

Johanne da Ulrik, an karɓe ɗansu riƙo a 2020 kuma gwmanati ta ce ba za ta sake duba duk waɗanda aka karɓi ɗansu riƙo ba.

An gwada Johanne mai shekara 43, a 2019 lokacin da take da ciki. Kuma an tsara za a karɓe ɗan nata da zarar ta haife shi.

Amma sai aka haife shi bakwaini kuma a lokacin hutun ƙarshen shekara, wanda ya sa ita da mijinta suka ci gaba da zama da shi tsawon kwana 17.

"Shi ne lokaci mafi farin ciki a rayuwata a matsayina na uba," in ji Ulrik mai shekara 57.

Wata sai ga ma'aikatan kula da al'umma da 'yansanda biyu sun je gidan Johanne da Ulrik domin karɓar ɗansu.

Ma'auranatan sun ce sun yi ta roƙon su su ƙyale musu shi. Johanne ta nemi a ƙyale ta ta shayar da shi karo na ƙarshe.

"Lokacin da nake shirya shi domin bai wa iyayen da za su karɓi riƙonsa, na ji baƙin ciki mai munin gaske," a cewar Ulrik.

'Ban samu damar ganin tatatarsa ba'

Bayan an karɓe riƙon ɗan Johanne da Ulrik, an ba su damar ganin sa duk mako har zuwa lokacin da aka karɓe shi gaba ɗaya a 2020.

Ba su sake ganinsa ba tun daga lokacin.

"Ban samu damar ganin tatatarsa ba, da fara maganarsa, da yin haƙorinsa, da saka shi a makaranta," a cewar Johanne.

Lauyansu na fatan shigar da ƙara a gaban kotun kare haƙƙi ta nahiyar Turai ta European Court of Human Rights.

Amma ministar kula da walwalar jama'a ta Denmark, Sophie Hæstorp Andersen, ta faɗa wa BBC cewa gwamnati ba za ta sake duba lamarin iyayen da aka karɓi 'ya'yansu riƙo ba saboda yaran sun samu "cikakkun iyaye da dangi".

Pilinguaq na ɗaya daga cikin 'yan Greenland ƙalilan da aka mayar wa da 'ya'yansu.

Ita da 'yar tata da hukumomi suka karɓe tana shekara ɗaya, sun sake haɗuwa a watannin baya. Yanzu shekararta shida.

Pilinguaq mai shekara 39 ta ce ta samu kiran da ba ta yi tsammani ba wata rana daga hukumar kula da al'umma.

"Na ɓarke da kuka da kuma dariya a lokaci guda. Ban yi tsammani ba. Na yi ta tunanin dawowarta."

Duka yaran Pilinguaq uku an karɓe su a 2021. Sauran biyun suna da shekara shida da kuma tara a lokacin.

Ta ce da amincewarta aka karɓi yaran kafin ta samu gidan da zai ishe su zama.

'Ƙwace ta cikin sa'a ɗaya'

'Yan watanni bayan 'yarta mai shekara shida ta koma gida, an faɗa wa Pilinguaq cewa za a dawo mata da sauran 'ya'yanta biyu manya a watan Disamba.

Hukumomin yankinta ne suka yanke shawarar mayar mata da 'ya'yan maimakon su jira gwamnati ta amince da hakan. Amma sun ƙi yarda su ce uffan game da lamarinta.

"Idan na shiga banɗaki na rufe ƙofa, sai ta shiga ruɗani tana cewa: 'Mama ban gan ki ba,'" a cewar Pilinguaq.

Ta ce kuma tana fargabar za ta iya sake rasa 'yarta nan gaba.

"Za su iya ƙwace ta cikin sa'a ɗaya. Za su iya sake ƙwace ta."