Abin da ya sa gwamnatin Kano ke shirin yi wa tubabbun ƴandaba afuwa

Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana wani shiri na yi wa tubabbun ƴandaba afuwa, ƙarƙashin wani shirinta na musamman domin kakkaɓe matsalar daba a fadin jihar.

Daba da ƙwacen waya su ne manyan matsalolin tsaro da ke addabar birnin Kano da wasu yankuna na jihar.

Matsalar ta haifar da asarar rayuka da dama, inda har gwamnati ta kafa wani kwamitin yaƙi da matsalar, sai dai duk da haka lamarin ya zamo mai wahala.

A lokuta da dama mahukunta sun zargi al'umma da rashin haɗin kai ta hanyar gaza fallasa ƴan daba da ke tsakaninsu, yayin da a ɓangare ɗaya kuma al'ummar ke zargin hukumomi da gaza ɗaukar ƙwararan matakan yaƙi da matsalar.

Yadda shirin afuwar zai gudana

Cikin wata hira da BBC, Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce matakin farko na yadda shirin shi ne su ƴan dabar su yadda za su tuba daga dabancin.

Waiya ya ce mataki na biyu shi ne rundunar ƴansandan jihar ta tantance waɗanda suka ƙudiri aniyar tuba.

''Kuma zuwa yanzu ƴansanda sun tantance kimanin mutum 718 domin shiga shirin afuwar, mu ma daga ɓangarenmu akwai kimanin mutum 960 da suka nuna sha'awar tuba''.

Ya ƙara da cewa bayan kammala tantancewar ne kuma za a miƙa sunayensu ga hukumar NDLEA mai yaƙi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙasar, a cewar Kwamishinan.

Ya ƙara da cewa NDLEA za ta horas da su sana'o'in da za su iya yi domin dogaro da kansu.

Bayan haka kuma gwamnati za ta tabbatar da afuwarta a kansu a hukumance.

Mece ce makomar tubabbun ƴandabar?

A duk lokacin da aka yi maganar yi wa wasu masu aikata laifi da suka tuba afuwa, abin da ke zuwa ran mutane da dama shi ne ɗorewar tuban nasu.

Saboda a wasu lokuta sukan zargi hukumomi da gaza sauke alƙawurran da suka ɗauka na tallafawa domin kauce wa komawa ruwa.

To sai dai kwamisninan yaɗa labaran na jihar Kano ya ce gwamnati ta yi wani ingantanccen tsari na kula da tarbiyyar matasan ta hanyar ba su jari ko mayar da su karatu.

''Akwai tanadin mayar da wadanda suke da sha'awa makaranta domin ci gaba da karatu'', in ji kwamishinan.

A nasa ɓangare kwamishinan ƴansandan jihar CP Adamu Bakori ya ce rashin bai wa tubabbun jari na daga cikin abubuwan da a baya suka kawo cikas ga batun yi wa ƴan daban afuwa.

''Rashin sana'a ne ke sa su sake komawa ruwa, domin duk lokacin da aka kama su za ka gan su, su ɗin ne dai suke maimata abin da suka yi. Indai za a ɓullo da tsarin ba su jari to hakan abu ne mai kyau'', in ji CP Bakori.

Ya kuma ce rundunar ƴansandan za ta yi amfani da tubabbun ƴandabar wajen samun bayanan waɗanda ba su tuba ba, domin kama su.

CP Bakori ya ce rundunar za ta riƙa gayyato malaman addini domin su yi musu wa'azi da huɗuba.

Girman matsalar daba a Kano

Daba matsala ce da aka daɗe ana fama da ita a jihar Kano, inda tsawon shekaru ake ganin mummunan tasirinta.

Matsalar ta sa jama'a a Kano na rayuwa cikin firgici tare da ƙaurace wa fitar dare da kuma yin taka-tsantsan da rana kasancewar harin daba na iya rutsawa da mutum a kowane lokaci.

BBC ta tuntuɓi wani tubabben ɗan daba, wanda ya bayyana matsalar da "gagaruma", ganin yadda take ƙara muni da kuma kai wa ga kisan bil'adama.

Ya ce a yanzu akwai wasu unguwannin da a baya ba a san su da matsalar ba, amma yanzu sun tsunduma ciki.

Matsalar daba ta fi yawo a tsakanin matasa waɗanda ake ganin su ne jagororin gobe.

Matashin mai shekara 32 ya ce daba kamar makaranta ce inda ake da manyan malamai masu ɗalibai waɗanda su ke aikata miyagun laifuka bisa goyon bayan da suke samu.

Ya ce akwai babban koma-baya da harkar daba ke haifar wa Kano, a fannonin zamantakewa da ilimi da kasuwanci da sauransu.

Unguwannin da daba ta fi ƙamari a Kano

A cewar tubabben ɗan dabar, a yanzu matsalar ta daba ta fi shafar unguwannin da ke wajen gari saɓanin baya da matsalar ta fi ƙamari a ƙwaryar birnin Kano.

Ya ce unguwannin da a yanzu suke fama da wannan matsala sun haɗa da:

  • Ɗorayi
  • Chiranchi
  • Gama
  • Rimin Kebe
  • Yankaba
  • Fanshekara
  • Sabon Titi
  • Hotoro

Sai kuma cikin ƙwaryar Kano da a yanzu ya ce matsalar ta ɗan ragu:

  • Madigawa
  • Adakawa
  • Ƙoƙi
  • Dogon Nama
  • Yakasai
  • Fagge
  • Zage
  • Yalwa
  • Dan Agundi
  • Ƙofar mata

Ba wannan ne karon farko da ake samar tsarin yi wa 'yan daba afuwa a Kano ba, ko a watan Oktoban 2023 ma, sai da rundunar ƴansandan Kano ta yi wa ƴandaba da dama afuwa sannan aka ɗauke su a matsayin ƴansandan sa-kai domin yaƙi da aikata laifuka.

To amma duk da haka har yanzu matsalar ba ta kau ba, lamarin da ya sa masana tsaro ke ganin sai hukumomi sun sauya salon yadda ake tunkarar matsalar a Kano.