Me zai faru idan muka gano baƙin halittu irin ɗan Adam na rayuwa a wata duniyar?

    • Marubuci, Tamlin Magee
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future

Marubuta ƙagaggun labarai da masu shirya fina-finai sun kwashe tsawon lokaci suna ɗiga ayar tambayar cewa: wace tarba za mu yi wa baƙin halittu idan da a ce sun shigo duniyarmu?

Abin da aka fi sani shi ne, ana kallon baƙin halittu ko kuma dodanni a matsayin ƙasƙantattu.

Har yanzu ba a kai ga gano alamun wata halitta ba, duk da cewa ana ci gaba da binciken. Idan har an iya ganowa a nan kusa to da alama ƙananan alamu za a gani na waɗanda ba mamaki suka taɓa zama a duniyar Mars ba manya masu kama da mutane ba irin waɗanda ake nunawa a fina-finai ba.

Amma a cewar nazarin Drake, akwai wasu halittu masu kaifin tunani, idan aka yi nazari cikin nutsuwa, da suka taɓa rayuwa - ko da kuwa hakan na nufin sai taurari sun haɗe baki ɗaya sun haɗe kansu za mu iya gani ko haɗuwa da su, saboda irin girma da yawa da kuma nisa tsakanin duniyoyi.

"Gano wata rai ko kuma haɗuwa da ita abu ne mai wuyar gaske har sai ranar da muka yi hakan," a cewar John Zarnecki, farfesa mai murabus kan harkokin sararin samaniya a Jami'ar Karatu Daga Gida a Birtaniya.

"Hakan ya sa na tuna da duniyoyin waje (exoplanets): lokacin ina matashin mai bincike, abin da muka yi ta tattaunawa ke nan, mua tunanin akwai su, amma ba zai taɓa yiwuwa mu gano su ba saboda abu ne mai wuyar gaske."

Yanzu mun san cewa akwai duniyoyin waje, kuma za a iya zama a cikin wasu saboda suna ɗauke da ruwa.

Yayin da ake ci gaba da neman da kuma yiwuwar haɗuwa da halittun, ba asara ba ce idan muka fara tunanin abin da za mu ji idan an yi sa'ar haɗuwa da su - musamman sabda halittu masu ƙwaƙalwa za su zama daban da mu.

Haƙƙin da ba na ɗan Adam ba

Marubuta ba su da ƙwarin gwiwar ɗan Adam zai tarɓi baƙuwar halitta da kyau.

Babu mamaki saboda a tarihinmu na kare haƙƙi a duniyar nan, na ɗan Adam ko na wani daban, ba na kirki ba ne, duk da irin yarjejeniyoyin ƙasashen duniya game da hakan.

Yadda za mu gane hujjar da za ta nuna ba za mu tarɓi baƙuwar halitta da kyau ba idan mun haɗu da su ita ce ta yadda muke kare haƙƙin wasu halittun a duniya.

Duk da cewa ƙasashe sun ayyana kare haƙƙin dabbobi, sai kwanan nan wasu ƙungiyoyi suka fara samun damar ɗaukar matakin shari'a wajen kare haƙƙin nasu.

Jill Stuart, ƙwararriya kan sararin samaniya a jami'ar London School of Economics, ba ta yarda cewa ɗan Adam zai haɗu da baƙin halittu ba a wannan rayuwar tamu. Amma ta yi imanin cewa ganin irin abin da ake tunanin za mu iya yi a irin wannan yanayi, ya kamata a buɗe fagen tattaunawa.

Rashin tsari

Babu wani tsari ko yarejeniya tsakanin ƙasashen duniya kan yadda ɗan Adam zai karɓi baƙuncin baƙuwar halitta mai kaifin tunani, a cewar Niklas Hedman, babban daraktan Majalisar Ɗinkin Duniya kan Harkokin Sararin Samaniya.

ukkan yarjejeniya biyar da aka ƙulla kan ayyuka a sararin samaniya - waɗanda a yanzu suka haramta amfani da makamai da kuma faɗowar ɓaraguzan kumbo - sun mayar da hankali ne kan abin da ɗan Adam ka iya aikatawa da kuma yadda zai cuci sauran mutane.

Aikin neman baƙin halittu da aka ƙaddamar a cibiyar International Academy of Astronautics bai tattauna kan abin da zai faru ba bayan gano halittun a 2010, bayan an shafe shekaru ana tafka muhawara.

Stuart ta yi imanin cewa abu ne mai wuya a iya samun wani karɓaɓɓen tsari tsakanin ƙasashen duniya har sai an samu buƙatar yin hakan.

Babban abin da za a fi tunani game da baƙin halittar shi ne: a taƙaice ko masu son zaman lafiya ne ko kuma fitinannu.

Ganin yadda babu wani tsari ko doka game da yadda tarɓi baƙin halittu idan an gano su, ɗaya daga cikin abubuwan da suka kamata shi ne a kare haƙƙinsu kamar yadda kare na ɗan Adam.

Ana kallon cewa duk halittar da za ta shigo duniyar Earth tana da ƙwaƙwalwa sosai da kuma damar jin abubuwa, saboda haka ya kamata a yi mata mu'amala irin ta ɗan Adam.

"Idan ana maganar baƙin halitta ya kamata mu yi tambaya: wane irin tunani suke da shi," in ji Susan Blackmore, marubuci kuma farfesa a jami'ar Plymouth ta Birtaniya mai bincike kan lura.

Yadda baƙin halitta ke jin abu

Wani abu mai muhimmanci shi ne damar jin raɗaɗi ko kuma jinya.

Shin baƙin halitta za su iya jin raɗaɗi?" kamar yadda Blackmore ya tambaya.

"Idan haka ne, akwai haƙƙoƙinsu da ya kamata mu kare, ko kuma ma mu kafa doka a kansu."

"Ganin cewa baƙin halitta na da damar jin abubuwa, kamar jin raɗaɗi da kuma daɗi, kuma suke da sauran buƙatu da za su ɗauke mu tsawon lokaci kafin mu tantance, abin da ya kamata mu yi amfani da shi shi ne irin na mutane," in ji shi.

"Abubuwa da yawa za su dogara ne kan irin kaifin tunanin baƙin halittar. Idan sun fi mu sosai, to ba lallai mu iya gane ko su wane ne su ba."

Ƙungiyar kare hakkin dabbobi ta Amurka Nonhuman Rights Project, ta ce abin da za a fara yi shi ne a ba su 'yancin kai, wani tsarin kotu da ake amfani da shi a Amurka da ke nufin mutum yana da damar aikata zaɓar abin da yake so ya aikata da kuma kaifin ƙwaƙwalwar tuna abin da ya faru a baya.

Me zai faru idan muka gano alamun rayuwar baƙin halittu a wata duniyar?

Idan har baƙin halittu za su iya shigowa duniyarmu, to da alama ba haƙƙinsu ya kamata mu damu da su ba.

Seth Shostak, wani babban masanin sararin samaniya a cibiyar Seti Institute da ke son fahimta da kuma bayyana asali ko tsarin rayuwar duniya, na da ƙwarin gwiwar haɗuwa da baƙin halitta a wannan lokacin namu. Amma yana da muhimmanci a bambance haɗuwa iri biyu da ake magana a kai.

Abu ne mai yiwuwa mu gano alamun ta hanyar amfani da kayayyakin kimiyya na wasu ƙasashe sama da a ce baƙin halittun sun kawo mana ziyara.

Idan kuma halittun suka kawo mana ziyara to hakan na nufin suna da ƙwarewar kimiyya sosai sama da wadda muke da ita.

"Idan suka iso, ni dai kam zan sayi pizza mai yawa na koma kan duwatsu," a cewar Shostak.

"Idan har za su iya zuwa nan, a madadin su turo saƙo, to suna da ƙwarewa sosai fiye da abin da muke da shi."

Shostak ya yi tambaya: "Me mutum zai yi idan masu cutarwa ne? Kamar fa a ce mutanen farko ne [Neanderthals] su yi ƙoƙarin fafatawa da rundunar sojan Amurka: Neanderthals ka iya samar da duk tsarin da suke so amma ba za su yi wani tasirin komai ba."