Hikayata ta 2024: Ƙa'idojin shiga gasar

Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai wadda ke samar da dama ga mata marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru.

Hakan kuwa zai ba damar nuna fasaharsu da kuma ba da damar karanta labaran nasu a harshen Hausa.

To sai dai dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo.

Ga ka'idojin Shiga Gasar:

Dole ne duk wani labari da za a turo da nufin shiga gasar Hikyata ya cika waɗannan sharuɗɗan:

1.Wajibi labarin ya kasance mace ce ko mata ne suka rubuta shi. Lallai ne labarin ya kasance cikin ingantacciyar Hausa, da bin duka ƙa'idojin rubutu. Wajibi ne mai turo da labarin ta kasance ta kai shekara 18 da haihuwa sannan ba ta wuce 35 ya zuwa ranar 24 ga watan Agustan 2024 ba. Ga masu turo da labarin haɗin gwiwa, wajibi ne kowaccensu ta kasance shekararta 18 sannan ka da ta wuce 35. Ba a yarda mata masu haɗaka su wuce biyu ba ga labari guda ɗaya ba. Ba a yarda ma'aikatan BBC ko 'yan uwansu su shiga gasar ba.

2. Dole ne labarin ya kasance ƙagagge kuma gajere da bai gaza kalma 1,000 sannan bai haura kalma 1,500. Za kuma a aiko da shi ta tsarin PDF ko ta hanyar kwafo labarin a zuba shi akwatin da aka tanada da ke cikin fom ɗin ko kuma ta hanyar sauke fom ɗin a cike a aike ta wannan imel ([email protected]).

3. Dole ne masu son shiga gasar su aike da labarin nasu ta hanyar fom ɗin ko kuma ta hanyar sauke fom a cike shi sannan a aika shi ta imel. Ba a yarda a aike ta duka hanyoyin ba. Hanya ɗaya ta wadatar.

Yadda za a shiga gasar:

  • Za dai a aiko da labarin ne ta tsarin PDF ko ta hanyar kwafo labarin a zuba shi akwatin da aka tanada da ke cikin fom ɗin nan ( Yadda za a shiga gasar ) ko kuma ta hanyar sauke fom ɗin a cike a aike ta wannan imel ([email protected]).
  • Ba za a yi maraba da labarin da ba cikakke ba ne.
  • Sau ɗaya kawai kowacce ko kuma haɗakar labari za su samu kaɓuwa. Sa a soke duk labarin da aka aike da shi fiye da sau ɗaya. Saboda haka za a yi amfani da labarin da kuka fara aikawa a yi watsi da sauran. A lura sosai kafin a shiga gasar.
  • Dole ne ki samu yardar amincewar abokiyar haɗaka idan labarin na haɗaka ne kuma dole a ga sa-hannunta a fom ɗin.

4. Za a rufe wannan gasa da karfe 23:59 agogon GMT na ranar 24 ga watan Agustan 2024. Ba za a yi maraba da duk wani labarin da aka aiko bayan nan ba. Ba za a dawo muku da labarin da kuka aiko mana ba saboda haka ku ajiye kwafin labarin naku kafin ku aika. Za kuma mu tuntubi wadanda aka zaɓi labaransu ne kawai. Z a dai a yi alƙalancin labaran naku ta wannan hanya:

5. Matakin Farko - Tantancewa: A cikin ma'aunin da za a yi amfani da shi don tantance labaran da aka turo akwai:

  • Dole ne ya kasance mace ce ta rubuta labarin
  • Labari ya kasance ƙirƙirar shi aka yi, ma'ana ba kwafo shi aka yi ba.
  • Amfani da ƙwarewa, ma'ana labari ya zama mai jan hankali da taurarin da suka dace;
  • Bin ƙa'idojin nahawu da na rubutun Hausa
  • Ka da labari ya ci zarafi ko mutumcin wani

6. Tawagar BBC za ta zabi labarai guda 30 da suka yi fice bisa doron ka'aidojin da aka wallafa a sama. Ta hanyar aiki tare da alkalai bisa jagorancin ma'aikacin BBC, za a zabi guda uku da suka ciri tuta sannan za a sake zabar guda 12 da suka yi rawar gani. BBC ka iya gayyatar waɗanda suka yi nasara da wasu waɗanda labaransu suka cancanci yabo, domin halartar taron bayar da kyaututtuka a Abuja wanda za a yi a watan Nuwamban 2024. Za a sanar da lokacin bikin karramawar a shafinmu na bbchausa.com.

7. Wadda ta zo ta ɗaya, da ta biyu, da ta uku ne kawai za su samu kyauta: Za a bayar da N1,000,000 (naira miliyan ɗaya) da lambar yabo ga labarin da ya zo na ɗaya; N750,000 (naira dubu ɗari bakwai da hamsin) da lambar yabo ga labarin da ya zo na biyu; da kuma N500,000 (naira dubu ɗari biyar) da lambar yabo ga labarin da ya yi na uku. Ga waɗanda suka yi haɗaka kuwa hakan na nufin za a raba musu kuɗin ne da sauran kautukan da za su samu. BBC za ta wallafa sannan za ta watsa labaran wadanda suka yi nasarar a shafinta na intanet da kuma rediyo. BBC za ta gudanar da bikin karrama gwarazan a Abuja, Najeriya a watan Nuwamban 2024. Kafar za ta ɗauki nauyin kuɗin mota da masauki wanda bai wuce ƙima ba. Waɗanda aka gayyata su ne ke da alhakin nema wa kansu izinin shiga Najeriya idan su ba 'yan kasar ba ne.

8. Dole ne labaran da za ku aiko su dace da tsarin aikin BBC da ke kunshe a nan a wannan shafin na kasa:

Abubuwan kuwa sun haɗa da

  • Ka da su nuna banbanci ga wata ƙabila ko jama'a;
  • Ka da labari ya tallata rikici ko kuma ta'addanci ko tallata 'yan siyasa da ma yin barazana ga tsaron kasa;
  • Ka da labari ya tallata wata haja indai ba BBC Hausa ba, ko kuma
  • Haddasa ƙiyayya bisa doron addini ko ƙabila ko jinsi ko kuma nuna ƙyama ga masu nakasa.

9. Wajibi ne labarin da za a aiko ya kasance aikin wadda ta turo da shi, kuma ya dace da ƙa'idojin da aka shimfiɗa. Kada labarin ya shiga haƙƙin wani (wanda ya haɗa da bayanan sirri), kuma kada a ɓata wa wani suna ko a aikata abin da ya saɓa wa doka.

10. Ba a yarda wata ta shiga gasar ta hanyar aikewa da labaran da aka rubuta shi ta hanyar amfani da fasahar AI kuma duk wadda ta yi hakan to za a soke rubutun nata.

11. Waɗanda suka yi na ɗaya da na biyu da na uku da kuma waɗanda suka cancanci yabo dole ne su san cewa babu wani abu da zai hana BBC watsa ko wallafa labaran nansu kamar yadda aka fada.

12. Mutum uku da suka zamo zakara da kuma 12 da alƙalai suka ce labaransu sun cancanci yabo na nufin sun bai wa BBC damar amfani da labaran nasu har abada kuma ta kowace irin kafa. Wannan ya kunshi bai wa wasu damar yin amfani da labarin. Sannan sun bai wa BBC 'yancin gyara ko fassara labaran nasu domin dacewa da yadda ake son yin amfani da shi. Marubutan kuma sun bai wa BBC damar sayarwa ko wallafawa da duk abin da kafar ke son yi da rubutun. Wannan dama ta shafi hadaka da mata biyu suka hadu suka rubuta labari.

13. BBC ba za ta ɗauki alhakin komai ba idan masu shiga wannan gasa suka yi biris da waɗannan ƙa'idoji, sannan kuma masu shiga gasar sun amince su bai wa BBC cikakkiyar kariya daga duk wani iƙirari da wani zai yi sakamakon yin karan-tsaye ga waɗannan ka'idoji. BBC na da ikon soke ko cire dukkan labarin da ya saɓa wa ko wanne daga cikin waɗannan ƙa'idojin.

14. Idan ba a iya tuntubar wata daga cikin wadanda suka zamo zakara ba bayan duk wani kokarin yin hakan ya ci tura, to BBC na da damar bai wa wadda take biye da ita damar.

15. Wadanda suka zamo na ɗaya ko biyu ko uku da kuma 12 da alkalai suka ce sun cancanci yabo (ko da kuwa hadaka ce) za a bukaci su shiga karin yarjejeniya da BBC kafin ci-gaba. Kin yin hakan ka iya sanya BBC dakatar da labarinki, inda za ta koma ga labaran wasu daban. Duk waɗanda suka zamo na ɗaya da biyu da uku ba su da damar sake shiga gasar har sai bayan shekara biyar. BBC ta ba su damar su bayyana kansu a matsayin zakarun gasar BBC Hausa ta Hikayata.Sai dai kuma zakarun dole ne su amince ka da su yi amfani da kambun a waɗannan abubuwa kamar haka:

  • A tallace-tallace
  • Neman kuɗi
  • Neman alfarma ko a kamfe
  • Gidauniya

16. Shiga gasar na nufin amincewa da dukkannin dokokin da BBC ta gindaya da suka hada da na soke duk labarin da ta ga dama a kowane lokaci idan har ta gamsu da cewa an yi dokokin nata karan tsaye ko kuma an aikata wani abu da yake kaskantar da ita.

17. BBC na da ikon sauya waɗannan ƙa'idojin a kowanne lokaci, ciki har da sauya hanyoyin zaɓen ko kuma alƙalan. Idan hakan ta kasance, to za a sanar a wannan shafin na intanet: bbchausa.com.

18. BBC da dukkan abokan huldarta ba za su dauki alhakin rashin amincewa da duk labarin da aka samu matsalar aikowa da shi sakamokon matsalar na'ura.

19. BBC ba za ta dauki alhakin duk wata asarar kudi ko kuma zubewar kima ba.

20. Ka'idojin da BBC ta shimfida sun shafi wannan gasar ne kawai:

21. Waɗanda suka shiga gasar suna da hakkin malllakar labaran nasu. Kuma sun bai wa BBC 'yancin yin amfani da labaran nasu kamar yadda yake a ka'idodjin nan.

22. An tsara waɗannan Ƙa'idojin ne bisa tanade-tanaden dokokin Ingila da Wales..