Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙwallon da Valverde ya ci Man City ce mafi ƙayatarwa a Champions League
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta zaɓi ƙwallon da Valverde ya ci Manchester City a matakin mafi ƙayatarwa a Champions League a 2023/24.
Ya zura ƙwallon ne a karawar zagayen quarter finals a wasan farko a Santiago Bernabeu ranar Talata 9 ga watan Afirilun 2024.
Masu gudanar da zaɓen wadanda suka yi bajinta a gasar ta zakarun Turai da aka kammala, sun ce ƙwallo na uku da ya ci da ta kai an tashi 3-3 ba wadda ta kamo ta a ƙayatarwa.
Haka kuma akwai biyu daga cikin 10 masu ƙayatarwa da ƴan wasan Real Madrid ne suka zura a raga a kakar nan.
Akwai ƙwallon da Rodrygo ya ci Napoli a wasa na biyar a cikin rukuni na uku da Real Madrid ta ja ragama zuwa zagaye na biyu.
Sai kuma ƙwallon da Bellingham ya zura a raga a dai karawa da ƙungiyar Italiya a karawar da aka yi a filin Diego Armando Maradona.
Real Madrid ta lashe Champions League na bana na 15 jimilla ranar Asabar a Wembley, bayan da ta doke Borussia Dortmund 2-0.
Wasan karshe na 18 da ƙungiyar Sifaniya ta buga kenan da ɗaukar Champions League na 15 kakar nan, wadda ba wata ƙungiyar da ta kamo Real a yawan ɗaukar kofin.
Dortmund ta sa ran lashe Champions League na biyu a tarihi a karo na uku da ta kai wasan karshe a gasar zakarun Turai.
Kuma karon farko da suka fafata a wasan karshe a gasar, amma na 15 da suka kece raini a tsakaninsu, inda Real ta ci wasa bakwai da canjaras biyar, Dortmunt ta yi nasara uku.
Wannan shi ne wasan karshe na biyu da Dortmund aka doke ta a Wembley, bayan da Bayern Munich ta yi nasara a 2013.