'Rufe sansanoni ƴan gudun hijira a Borno ya tagayyara su'

Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto da ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Human Rights Watch ta fitar ya nuna cewa matakin da gwamnatin jihar Borno ta ɗauka na rufe sansanonin 'yan gudun hijirar - da yaƙin Boko Haram ya tilasta wa barin gidajensu - ya ƙara jefa sama da mutum 200,000 cikin mawuyacin hali da tagayyara.
Rahoton ya ce gwamnatin jihar ba ta samar wa mutanen wurin da za su koma ba, abin da kuma ƙungiyar ta ce ya saɓa wa 'yancinsu na muhalli, da abinci da kuma 'yancinsu na rayuwa.
Rahoton mai shafi 59, ya nuna illolin rufe sansanonin 'yan gudun hijirar, abin da ya sa aka dakatar da rabon abinci ga 'yan gudun hijirar tare da tilasta musu barin sansanonin.
Ƙungiyar ta zargi gwamnatin jihar da rashin samar wa 'yan gudun hijirar cikakkun bayanai game da wurin da za ta mayar da su, da tabbatar da lafiya da kare rayukansu.
Bisa wannan dalili ne ƙungiyar ta ce mutanen ke fafutikar neman muhimman abubuwan buƙatun rayuwa kamar abinci da matsuguni a sabbin wuraren da suka koma.
Anietie Ewang wacce wallafa rahoton ta ce ''Ta ce gwamnatin Borno na cutar da dubun-dubatar 'yan gudun hijirar waɗanda ke zaune cikin ƙunci ta hanyar yaɗa manufofinta marasa tabbas domin raba 'yan gudun hijirar da samun kayyakin agaji''.
Ta ƙara da cewa fitar da 'yan gudun hijirar daga sansanoninsu ba tare da samar musu wani taimako ba, babu abin da zai haifar, sai ƙara sanya su cikin tagayyara da halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
Rahoton ya ƙara da cewa tsakanin watan Mayun 2021 zuwa Agustan 2022, gwamnatin jihar ta tilasta wa mutum 140,000 ficewa daga sansanonin 'yan gudun hijira dake birnin Maiduguri.
Haka kuma gwamnatin na shirin rufe wasu ƙarin sansanoni biyu a wannan shekarar, lamarin da zai shafi 'yan gudun hijira 74,000.
An dakatar da rabon taimakon abinci
Rahoton ya ce ƙungiyoyin agaji sun dakatar da rabon taimakon abinci, tun lokacin da gwamnan jihar Babagana Umaru Zulum ya bayyana cewa za a rufe duka sansanonin 'yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri a watan Disambar 2021.
Duk da cewa ba a rufe wasu sansanonin ba, ƙungiyoyin agaji irin su Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya sun dakatar da ayyukansu kasancewar ba su saka shekarar 2022 cikin kasafin kuɗinsu ba, sakamakon sanarwar rufe sansanonin da gwamnatin jihar ta fitar.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar na samar da taimakon abinci ga 'yan gudun hijirar da ke zaune a sansanonin da ba a rufe su ba.
To sai dai 'yan gudun hijirar sun koka cewa abincin ba ya wadatar da su.
Rohoton ya ambato mutane da yawa na cewa ana hana su abincin, ko kuma a ɗauki kwanaki kafin a ba su abincin.
'A baya har kifi ake raba mana'
Wani mutum mai shekara 29 da ke da 'ya'ya huɗu ya ce ''a sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri muna cin abinci mai gina jiki, irin su kifi, amma a nan Bama ba ma samun irin wannan abincin''.
Ya ƙara da cewa yanzu haka yaransa ba su da cikkakiyar lafiya, duk sun rame kuma ba su da wani kuzari kamar yadda ya bayyana.
Haka kuma rahoton ya ce matakin ya tilasta wa yara da dama komawa yin bara a kan titunan jihar domin neman abin da za su ci, duk kuwa da hatsarin da ke tattare da yin hakan, kamar hatsarin ababen hawa, da sace mutane domin neman kuɗin fansa, da safarar bil-adama, da fyade da sauransu.
Mutanen na zaune cikin mummunan yanayi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rahoton ya kuma ce 'yan gudun hijirar da aka tilasta wa ficewa daga sansaninsu a birnin Maiduguri na zaune cikin mawuyacin hali fiye da yadda suke a sansanin 'yangudun hijirar.
Ƙungiyar ta ce gidajen da mutanen ke zaune a yanzu ba su da kyau, da yawa ruwan sama ya lalata su, ga rashin tsafta da rashin ban ɗakuna masu inganci.
Gwamnatin jihar ta ce ta sake gina gidaje a wuraren da ta umarci 'yan gudun hijirar da su koma, irin su Bama wadda aka lalata tare da ƙona gidaje masu yawa sanadiyyar rikicin Boko Haram.
To sai dai mutanen da suka koma wajen sun ce batun sake gina gidajen nasu ba gaskiya ba ne. Daga ƙarshe ƙungiyar ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta sa baki domin kawo ƙarshen mawuyacin halin da 'yan gudun jihar jihar ke ciki, a maimakon shirya wa jiran ɓarkewar wata annoba.
Haka kuma ta yi kira ga gwamnatin jihar Borno da ta dakatar da shirinta na rufe sansanonin 'yan gudun hijirar da ke jihar, har sai an yi cikakken shiri da tuntuɓar 'yan gudun hijirar da sauran masu ruwa da tsaki.
Gwamnatin Borno ta sha bayyana gina wa ƴan gudun hijirar gidaje
BBC ta yi oarin jin martanin gwamnatin jihar Bornon amma hakan bai samu ba har zuwa lokacin wallafa wannan labari.
Sai dai ko a baya-bayan nan gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa aikinta na haɗin gwiwa da wasu ƙungiyoyin agaji na duniya na taimakawa yadda ya kamata wajen sake tsugunar da 'yan gudun hijirar.
Ko a ranar 22 ga watan Oktoban da ya gabata gwamnatin jihar ta ce ta yi bikin buɗe gidaje 804 da ta ce ta gina wa 'yan gudun hijira a jihar.
A wani saƙo da gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya wallafa a shafinsa Tuwita ya ce an yi bikin buɗe gidajen da gwamnatinsa tare da haɗin gwiwar hukumar raya ƙasashe ta Majalisar Dinkin Duniya suka gina, domin sake tsugunar da wasu al'umomi a jihar.
Cikin saƙon da gwamnan ya wallafa ya nuna cewa an raba shanu 2,674 da abinci, da tufafi ga mutanen, tare da bayar da zunzurutun kuɗi har naira 100,000 ga kowannensu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X











