Rikicin Boko Haram: Matan da ke tafiya mai nisa don kubutar da rayuwar ‘ya’yansu

Asalin hoton, Getty Images
Dan Fati Usman na kwance a gadon asibiti da ke arewa maso gabashin Najeriya, cikin halin rai-kwakwai mutu-kwakwai.
Da kyar yake iya numfashi, yanayinsa abin tausayi, wasu tarin kudaje sun samu mazauni a kumatunsa.
Yanayin jikinsa zai sa ka yi tunanin bai wuce shekara uku ba, amma mahaifiyarsa ta shaida mana cewa shekararsa biyar.
Yana daya daga cikin miliyoyin mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa, inda yake bukatar tsananin taimako, sakamakon yadda hare-haren mayakan Boko Haram suka sanya su tserewa daga muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya.
Dubun dubatar iyalai ne ke tsananin bukatar taimakon abinci da magani.
Kungiyoyin agaji sun ce rashin kudade ne ya janyo halin da ake ciki, saboda gwamnatin Najeriya ta dogara ga kungiyoyin agaji, da Majalisar Dinkin Duniya wadda yanzu ta mai da hankali kan yakin da ake yi a Ukraine.
Ga yawancin mutanen da rikici ya raba da muhallansu, sansanin 'yan gudun hijira shi ne kadai zabin da suke da shi da zarar sun tsere daga inda rikicin yake faruwa.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai a bara gwamnatin jihar Borno, wadda nan ne cibiyar rikicin Boko Haram, ta dauki matakin rufe sansanonin 'yan gudun hijirar, bayan da ta ce wuraren sun zama matattarar yin abubuwan da ba su dace ba, ko da yake ana bai wa iyalan da aka tilasta wa barin sansanin dala 200.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kiyasin jami’an agaji ya nuna cewa kusan yara miliyan biyu ne za su fuskanci karancin abinci mai gina jiki a Najeriya a bana.
Hakan na nufin an samu karin kashi 20 cikin 100 idan aka kwatanta da bara.
Sannan ana fargabar yara 5000 ka iya mutuwa a watanni masu zuwa saboda yunwa.
Fati Usman ta shaidawa BBC cewa danta ya fara rashin lafiyar ne da zazzabi, daga bisani amai da gudawa suka kwantar da shi.
“Na dan samu magani na ba shi, amma babu wani sauki sai wajen Allah. Yau kwanaki 37 kenan yana fama da amai da gudawa,” in ji Fati.
Lokacin da rashin lafiyar ta yi tsanani, dole ta garzaya da shi asibiti a birnin Damaturu na jihar Yobe. “Kwananmu biyu da zuwa asibitin nan.”
‘Ya’yan ta biyar sun rasu cikin rikicin nan Boko Haram, Wannan shi ne daya daga cikin ‘ya’yan Fati hudu da suka rage a raye, shekarun ya 34 amma ta fita a hayyacinta Saboda rashin kwanciyar hankali da sukuni.
Hare-harem BOko Haram ya tilasta ma ta yin hijira daga garin Maino a jihar Yobe, kuma shekarar ta biyar a sansanin yan gudun hijira.
“Ba mu dauki komai ba, haka muka tsere daga mu sai kayan jikin mu,” in ji Fati.
Karuwar matsalar rashin abinci mai gina jiki ta ta'azzara halin da ake ciki da barkewar cutuka kamar amai da gudawa, ga kuma rashin yin noma saboda hadarin da manoma ke shiga idan sun je gona.
Mijin Fati, Malam Usman malamin adddinin Musulunci ne, kuma ba tare suke zaune a sansani guda ba. Fati tana sana'ar tela domin ta samu abinci.
Lamarin ba mai sauki ba ne, domin su ma makwabtata kansu suke yi, su ma rikicin Boko Haram din ne ya raba su da muhallansu, kowa ya dogara ne ga tallafin gwamnati ko kungiyoyin agaji.
An ce idan dambu ya yi yawa, baya jin mai. Dalilin da ya sanya mazauna sansanin yan gudun hijira ke fadawa halin ni-'ya-su saboda rashin abinci.
“Anan matsalar ta fi kamari, don haka duk wanda ka ga ya zo nan, suna cikin mawuyacin hali ne,” in ji Dakta Udokwu Japhet, da ke aiki ba dare ba rana a wannan sansanin.
Kuma duk maka yana kwantar da yara 40, da ke fama da karancin abinci mai gina jiki.
Shi ma kamar sauran likitoci, fargabarsa ita ce barkewar wata annoba.
Likitan ya fada wa BBC, iyaye kan niko gari tun daga nisan kilomita 100 domin kawo ‘ya’yansu asibiti, saboda rashin magani a garuruwa da kauyukansu.
Yawancin sun fito daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Suna fama da rashin abincin da za su bai wa ‘ya’yansu, saboda rashin shuka amfanin gona domin fargabar harin ‘yan Boko Haram.
Halin da ake ciki ya munana, tun farkon shekarar 2022, aka samu kwararar yaran da ake kai wa asibiti. Hakan ya sanya wannan cibiyar lafiya ta cika makil da marasa lafiya.
Dakta Udokwu ya ce an kawo wani yaro cikin mawuyacin hali, kuma shi da jami’an lafiya suka soma kula da shi cikin gaggawa.
“Yaron ba ya cikin hayyacinsa saboda kwanaki da ya dauka yana amai da gudawa, dole muka ba shi taimakon gaggawa.”
“Kusan ko da yaushe ana kawo marasa lafiya cikin mawuyacin hali, wasu saboda firgita,” in ji Dakta Udokwu.
Cibiyar na daga cikin wadanda aka bai wa tawagar BBC damar shiga a yankuna masu wuyar sha’ani a arewa maso gabashin Najeriya, inda jami’an lafiya ke fadi tashin ceto rayukan yaran.

Asalin hoton, Getty Images
A wata cibiyar lafiya da ke garin Bama mai hada-hadar kasuwanci, jami’an lafiya na fama da yaran masu matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Fatima Bukar, matashiyar uwa ce mai shekara 25, ta ce ‘ya’yanta uku ne suka mutu saboda rashin abinci.
Ta yi tafiyar kilomita 30 dauke da ‘ya’yanta biyu da suka rage a raye zuwa sansanin ‘yan gudun hijira.
‘Ya’yan Fatima na daga cikin yara 22 da aka kwantar a dakin yara mai cin gado 16, a cibiyar lafiya da ke garin Bama.
‘Yarta mai shekara hudu, idanunta sun kumbura, ta yi wa uwar zuru da ido, amma takan fashe da kuka, musamman idan ta juya domin ganin halin da danta bai shekara daya ke ciki.
Gadon da ke kallon na Fatima Bukar, wata yarinyar ce ke canyara kuka duk lokacin da mahaifiyar ta yi kokarin gyara mata kwanciya da son ta yi rigin-gine. Kusan rabin jiki ya yi kama da kuna, har Zuwa fuskarsa.
likitoci, sun ce lalurar fata ce kuma ta na faruwa ne idan jikin yaro ya kumbura da zarar ya Fara warkewa sai fatan jiki ya dinga darewa hakan ya sa ta yi kama da kuna.
Dakta Ibrahim Muhammad shi ke kula da cibiyar, ya fada mana wannan ba daya daga cikin matsalolin da rashin abinci mai gina jiki ke haddasawa.
“Kusan kullum sai an kawo yara masu yawa da matsalar rashin abinci mai gina jiki. Yawanci sun taho daga sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bama.”
Jami’in Lafiya John Mukisa, ya ce idan ba a samu karin tallafin abinci da gaggawa ba, to kuwa yara da dama za su mutu ko makasa.
Tun bayan shan rantsuwar kama aiki a shekarar 2015, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, ta yi alkawarin magance matsalar tsaro da da tada kayar bayan Boko Haram.
Dubban mayakan sun mika wuya ga sojojin Najeriya bi sa radin kansu, Amma ana ganin gwamnatin ta gagara shawo kan matsalar.
A iya cewa mika wuyan da ‘yan Boko Haram ke yi, na dan yin tasiri. Saboda mazauna yankunan da matsalar ta yi kamari na samun 'yar kwanciyar hankali.
Fati Usman ta bayyana fargabarcewa lamura ka iya munana fiye da wadanda ake gani a halin yanzu.
“Tun da aka kai hari kauyenmu, ba a kara samun kwanciyar hankali ba. Cututtuka na kashe ‘ya’yanmu, kuma haka lamura za su ci gaba matukar ba a dauki matakin ceto mu tare da ‘ya’yanmu ba.”










