Sojojin Najeriya sun halaka mai kitsa hare-haren Boko Haram a kasashe uku

Nigerian troops fighting Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun hallaka 'yan ta-da-ƙayar-baya 28 ta hanyar hare-haren jiragen sama a yankin jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.

Harin ya faru ne a ranar Larabar da ta wuce. Cikin waɗanda aka kashe ɗin har da wani babban kwamandan Boko Haram, Alhaji Modu wanda aka fi sani da suna Bem Bem.

Ana zargin Alhaji Modu da kitsa hare-haren Boko Haram a Najeriya da Nijar da kuma Kamaru daga wasu kogunan da ke tsaunin Mandara.

Kafofin yada labarai na cikin gida a aNajeriya sun ambato wani kwararre kan harkokin yaki da 'yan tayar da kayar baya mai suna Zagazola Makama na cewa Alhaji Modu dan fashi da makami ne kafin ya zama kamandan Boko Haram.

Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin wannan rahoto ba.

Gwamnatin Najeriya ta ce dukkan dakarunta na soji na samun gagarumar nasara a yakin da suke yi da mayakan Boko Haram da suka mika kansu ga hukumomi bisa radin kai a yankin na arewa maso gabas.

An hallaka kasurgumin ɗan fashin daji da ya addabi yankunan arewacin Najeriya

A wani labarin daban kuma, rundunar sojin Najeriyar ce ta ce ta yi nasarar kashe wani kasurgumin ɗan fashin daji Albdulkarim Boss da mutanansa 27 a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaƙi ya yi a kan maboyarsu.

Abdulkareem Lawal wanda aka fi sani da Abdulkareem Boss, an jima ana farautarsa kafin a hallaka shi a wannan lokaci.

An hallaka ɗan fashin ne a kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana ta Katsina.

Hare-haren sama da sojojin suka kaddamar na zuwa ne kasa da mako guda da Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da manyan hafsoshin tsaron ƙasar da su ka yi alkawarin kawo ƙarshen matsalolin tsaron Najeriya.

Abdulkareem ne ya jagoranci muggan hare-haren ta'addanci da dama a yankunan arewacin Najeriya da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Sannan shi ya jagoranci kai hari kan ayarin motocin shugaban kasa a Daura da kuma mutuwar shugaban 'yan sanda yankin Dustinma a cikin watan Yuli.

An kuma kai irin wadannan hare-haren sama a maboyar 'yan bindiga a kauyukan Abuja a cewar jaridar PRNigeria.

A cewar rahotanni 'yan bindiga da ke maboya a dazukan Kaduna da Neja da Zamfara ke haifar da barazanar tsaro a babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.