Waiwaye: Kyautar motocin yaƙi da Buhari ya bai wa Nijar, ɗage Shari’ar Sanata Ekweremadu zuwa watan Oktoba
Ga wasu muhimman abubuwa da suka faru a wannan makon a Najeriya daga ranar Lahadi 31 ga watan Yuli zuwa Asabar 06 ga watan Agusta.
Kyautar Motoci da Buhari ya bai wa Nijar ta 'harzuka wasu ‘yan Najeriya'

Asalin hoton, PRESIDENCY
A cikin makon nan mai ƙarewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tallafawa maƙwabciyarta Nijar da motocin yaƙi da darajarsu ta kai naira biliyan ɗaya da rabi.
Wannan kyauta da Najeriya ta yi ya haifar da zafafar martani da shaguɓe iri-iri.
Sai dai gwamnatin Shugaba Buhari ta ce ta bai wa maƙwabciyar tata motoci10 da zimmar inganta ayyukan tsaro.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriyar ke tsaka da nata matsalolin tsaron a kusan kowane saƙo.
Binciken da BBC Hausa ta gudanar ya nuna cewa ba wannan ne karo na farko da Najeriya ta fara taimaka wa maƙwabtan nata ba, kamar yadda Minista Zainab ta faɗa, amma a yanzu ne abin ya fi fitowa fili.
An ɗage shari'ar Sanata Ekweremadu zuwa watan Oktoba

Asalin hoton, Getty Images
An ɗage sauraron shari'ar ɗan Majalisar Dattawa ta Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice, zuwa watan Oktoba bisa zargin da ake yi musu na yunƙurin yunkurin cire sassan jikin mutum a Birtaniya.
Ana tuhumar sanatan, mai shekara 60 da matarsa 'yar shekara 55, da yin safarar wani matashi mai shekara 21 daga Najeriya zuwa Birtaniya.
Zama na gaba da kotun za ta yi shi ne a ranar 31 ga watan Oktoba, amma sauraron ƙara da gabatar da shaidu a shari'ar sai watan Mayu na shekarar 2023.
Masu shigar da ƙara sun yi iƙirarin cewa mutanen sun kai matashin Birtaniya ne don a cire masa ƙoda da zimmar a saka wa 'yarsu.
Dawo da dokar hana hawa babur a Jihar Katsina

Asalin hoton, other
Rundunar 'yan-sandan jihar Katsina ta Najeriya ta sanar da dawo da dokar hana amfani da babur a fadin jihar.
Rundunar ta bayyana hakan ne wata hudu bayan da gwamnatin jihar ta dage dokar ta dan wani lokaci domin bayar da dama ga jama'a su sarara a lokacin azumi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar Gambo Isah, ya fitar ya ce an sake dawo da dokar ne sakamakon karuwar hare-hare da barazanar 'yan ta'adda da sauran miyagu wadanda ke amfani da babura.
Dokar ta hana amfani da babura daga karfe goma na dare zuwa shida na safe a cikin birnin Katsina. Su kuwa kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaron sosai dokar na farawa ne daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.
ASUU ta tsawaita yajin aikinta da mako huɗu
Kungiyar Malaman Jami'o'i a Najeriya ta ASUU ta bayyana matakin tsawaita yajin aikin da take yi da mako hudu.
Dama ASUU ta shafe sama da watanni biyar tana yajin aikin bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin Najeriya, yanzu kuma gashi ta kara wata daya.
Idan har aka shafe wasu makonni hudu ba a sasanta tsakanin gwamnati da ASUU ba, hakan na nufin ɗaliban jami'o'in sun shafe rabin shekara suna zaman jiran tsammani a gida.
Sanarwar da ASUU ta fitar na dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Emmanuel Osodeke, an kuma fitar da ita ne bayan kammala wani zaman gaggawa na jiga-jigan kungiyar ranar Lahadi a Abuja.
Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta tsunduma yajin aiki, bisa zargin gwamnatin Najeriya da gaza cika alkawuran da ta dauka a yarjejeniyar da suka ƙulla, ciki har da batun inganta rayuwar malaman da kuma dambarwar shigar da kungiyar tsarin biyan albashi na IPPIS da gwamnatin ta fito da shi.
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta haramta aibata jami'anta a fina-finai

Sifeta Janar na Yan sandan Najeriya ya gargadi masu shirya fina-finai a kasar da su guji aibanta aikin dan sanda a shirye-shiyensu na talabijin, ba tare da izinin rundunar ba.
IG Usman Baba ya kara da cewa daga yanzu ka da a ƙara ganin wani mutum sanye da kayan ɗan sanda a fina-finai, ba tare da izini ba kamar yadda doka ta tanadar.
Ya ce idan ba haka ba to kuwa duk wanda ya karya doka zai ɗanɗana kudarsa.
Masu shirya fina-finai a Najeriya kan kwaikwayi jami'an yan sandan kasar, kuma a mafi yawan lokuta ba a nuna su a mutanen kirki.
Sanarwar da rundunar yan sandan ta fitar ta ce "ka da wani mai shirya fina-finai da ya sake nuna ƴan sanda a matsayin marasa kirki ba tare da izini ba a rubuce daga rundunar yan sanda."
Sanarwar ta ƙara da cewa ba za ta amince da bayyana aikin ɗan sanda ba a fina-finai, matsawar abin da aka kwaikwaya a aikin ba shi da kyakkyawan tasiri ga al'umma.
An saki karin fasinjoji biyar na jirgin kasan Abuja-Kaduna

Asalin hoton, other
'Yan bindigar da suka sace fasinjoji a jirgin kasar da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a Najeriya a watan Maris din da ya gabata sun saki karin fasinjoji biyar.
Hukumomin tsaro da gwamnatin kasar ba su tabbatar da sakin karin mutanen ba, amma gidan talbijin na Channels TV ya ambato mutumin da ke shiga tsakani domin sako fasinjojin Tukur Mamu yana cewa an saki mutanen ne a yau Talata.
Ya bayyana cewa mutanen da aka saka su ne: Farfesa Mustapha Umar Imam, Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.
Babu bayani kan ko sai da aka biya kudin fansa kafin a saki fasinjojin.
A watan jiya ne aka saki karin wasu fasinjojin jirgin kasan na Abuja-Kaduna kwanaki kadan bayan 'yan bindigar sun fitar da wani bidiyo wanda ya nuna su suna lakada musu duka.
Gwamnatin Buhari ta ci tarar Trust TV N5m

Asalin hoton, TRUSTTV
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumar da ke sa ido kan kafafen watsa labarai ta Najeriya, ta ci tarar Trust Television Network (Trust TV) naira miliyan biyar saboda labarin da suka wallafa kan hare-haren da ake kai wa a jihar Zamfara mai taken "Nigeria's Banditry: The Inside Story".
Wata sanarwa da kamfanin Media Trust ya fitar ta ce hukumar, a wata takarda dauke da sa hannun darakta janar dinta Balarabe Shehu Illela, ta ce ta ci tarar Trust TV ne "saboda ta watsa rahoto na musamman da ya saba ka'idojin wasu sassan ayoyin dokar hukumar."
Sai dai kamfanin Media Trsut ya ce a "Yayin da muke ci gaba da nazari kan matakin hukumar da kuma duba zabukan da muke da su, muna sanar da cewa a matsayinmu na gidan talbijin, mun yi amannar cewa muna aiki ne domin al'umma ta hanyar karin haske kan batun garkuwa da mutane mai sarkakiya da kuma yadda yake shafar miliyoyin jama'ar kasarmu."
Sanarwar ta kara da cewa rahoton ya bi salsalar zaman dar-dar a tsakanin al'umma da kuma abubuwan da suka sanya rikicin da ya sa wasu ke daukar makamai da ke jefa mutane cikin gagarumin halin kaka-na-ka-yi.
Gwamnatin Plateau ta kwace lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu a jihar
Gwamnatin jihar Filato ta kwace lasisin dukkan makarantun firamare da kuma na sakandari masu zaman kansu a fadin jihar.
Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Elizabeth Wampum, ita ce ta bayyana hakan a yau alhamis.
A cewarta, an dauki matakin ne bayan gano cewa sama da makarantu 5000 na koyarwa ba tare da lasisi ba.
Kwamishiniyar ta ce kashi 90 cikin dari na makarantu masu zaman kansu a Filato ba sa bin ka'idoji da tsare-tsaren gwamnati.
Inda ta kara da cewa kashi 85 na makarantu 495 masu zaman kansu da aka bai wa lasisi tun da farko ba su bi ka'ida ba.
Rashin dala ya sa matafiyan Najeriya sun rasa na yi

Asalin hoton, Getty Images
'Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsala da shan wahala wajen canza dalar Amurka a babban bankin kasar (CBN) a kan farashin gwamnati.
Wadanda wannan lamari ya fi shafa su ne matafiya kasar waje wadanda yake daukar su lokaci kafin su samu canjin yin kasuwanci (BTA) da canjin kashewa (PTA) a sanjin gwamnati mai sauki domin zuwa asibiti ko karatu ko harkar kasuwanci.
Wannan rashi ya shafi iyaye saboda wahalar samun dala domin biyan kudaden makaratun yaransu da ba su kudin kashewa.
Bincike ya nuna cewa akwai matuƙar wahala wajen samun dala saboda bukatarta ta fi adadin da ake da ita, lamarin da ya tursasa wa bankuna ƙara tsawon lokutan samar da PTA/BTA daga makonni biyu zuwa takwas.











