Abin da Ministan Sufurin Najeriya ya ce kan dawo da jigilar jirgi tsakanin Abuja-Kaduna
Ministan Sufurin Jiragen Kasa na Najeriya Mu'azu Jaji Sambo ya ce suna sa rai nan ba da jimawa jigila za ta dawo tsakanin Abuja zuwa Kaduna.
Ya bayyana haka ne ranar Juma'a a Abuja, babban birnin kasar.
Ministan ya fadi dalilin da ya sa fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da aka ceto ba su je Abuja domin ganawa da gwamnati ba.








