Abin da ya sa Tanzania take kishi da kasar Kenya kan zabe

.

Asalin hoton, Getty Images

A jerin wasikun da marubuta na Afrika suke aiko mana, dan jarida Sammy Awami, dan kasar Tanzania ya fahimci cewa kasarsa ta fara yi wa Kenya kallo a matsayin abar koyi ta fuskar siyasa.

'Yan kasar Tanzania na kallon abin da ke faruwa a makwabtansu Kenya, kallo irin na 'kishi da ina ma a ce', saboda nasarar da ta samu ta gudanar da zabe lami lafiya, da kuma yadda aka mika mulki daga Shugaba Uhuru Kenyatta zuwa abokin hamayyarsa wanda a baya dan na hannun-damansa ne, wato William Ruto.

'Yan Tanzania sun cika da mamaki, ganin yadda shugaban hukumar zaben Kenya ya nuna cikakken 'yancin da yake da shi, ya bayyana Mr Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai Raila Odinga, mutumin da ya sha kaye, ya garzaya kotu, ko da yake ita ma Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Mr Ruto a kan Mr Odinga, wanda Shugaba Uhuru ya mara wa baya a lokacin zaben.

Duk da wasu kwamishinonin zaben sun nuna rashin amincewarsu da sakamakon, amma a cewar Kotun Koli, Mr Ruto ya ci zabe wanda ta ce sahihi ne, kuma hakan ya dadada ran 'yan kasar Kenya da dama.

Jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM), wadda ta kankane mulki tsawon sama da shekara 50, za ta yi mamakin yadda Raila Odinga ya sha kaye a zaben Kenya.

Gabanin zaben Tanzania na 2015, mai magana da yawun jam'iyyar ta CCM a lokacin, Nape Nnauye ya yi alkawarin cewa jam'iyyarsu za ta lashe zabe ko ta halin kaka.

Shekaru biyar bayan haka, Sakataren CCM na lokacin Bashiru Ally ya fadi cewa abin ban dariya ne a yi tunanin jam'iyyar ta ki amfani da damar da take da ita, ta cewa ita ke rike da madafun iko don ta ga ta lashe zabe.

Har ma ya bayar da misali da makomar jam'iyyu a kasashen Kenya da Zambia, da suka kasa amfani da damarsu har ya sa suka yi rashin nasara.

''Idan ka ki amfani da damar da kake da ita, za ka zama kamar jam'iyyar Kenyan African National Union (Kanu). Daga lokacin da Kanu ta kasa amfani da damar da take da ita ba ta sake dawowa mulki ba. Ko kuma United National Independence Party a Zambia.''

A Tanzania, da zarar aka ce CCM ta tsayar da mutum takara, to kamar ya lashe zabe ne tun kafin ma a fafata.

A zaben 2020, an soke takarar majalisa a jam'iyyu da dama, lamarin da ya bai wa 'yan jam'iyyar CCM 18 damar cin zabe ba tare da hamayya ba.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu sukar gwamnatin Tanzania na zargin jami'an tsaro da cin zarafin duk wani mai adawa da gwamnati
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

'Yan Tanzania sun fara mamakin yadda tsarin gudanar da zaben Kenya ya gudana tun kafin ranar zaben.

Sun yi mamakin alal misali, yadda 'yan adawa suka sayi fom-fom, suka cika suka mayar wa hukumar zabe, kuma da dama sun samu amincewar hukumar ba tare da wata matsala ba.

A Tanzania, 'yan takara da dama sukan samu hukumar zaben na take-taken lalata musu shirin tsayawa takara, ta hanyar rufe ofisoshinsu kafin su mika musu fom din da suka cike na takara.

Wasu ma akan kai musu hari a balla gidajensu, ko ma a illata su a daidai lokacin da suke shirin zuwa ofis din hukumar zabe.

Wani abu da ke burge 'yan kasar Tanzania game da zaben Kenya shi ne irin yadda 'yan takarar ke kokarin yi wa juna zarra, ta hanyar tara dimbin jama'a a lokacin kamfe.

Shekaru hudu kafin zaben 2020, shugaban Tanzania a lokacin, John Magufuli, ya hana 'yan adawa yakin neman zabe.

A lokacin da aka ba su damar yakin neman zaben 'yan makonni kafin a gudanar zabe, sun kuma fuskanci matsaloli daga jami'an tsaro, irin yadda suka rika cin zarafinsu da kuma kama masu fafutuka da shugabannin jam'iyyu.

A daya daga cikin gangamin an taba jefa wani abin fashewa daga wasu mutane da ba a san ko su waye ba a tsakiyar jama'a.

Wani abin kunya kuma shi ne yadda ake amfani da fasahar zamani. A Kenya, duk dan kasa zai iya shiga ta intanet ya samu bayanan zabe kai-tsaye, ya kuma ga sakamakon zaben da yake nema.

.

A Tanzania, batun saka zabe ta internet na fuskantar zagon kasa. A zaben da ya gabata, sai da aka samu daukewar intanet wanda hakan ke nufin duk wani abu da za ka yi da ya hada da rubutu ko kuma shiga shafukan sada zumunta, ko kiran waya ma ya zama abu mai wahala.

Kazalika dan takarar da ya sha kaye ba shi da ikon kalubalantar zabe a gaban kotu, kamar yadda Raila Odinga ya yi, ballantana a yi maganar mutane su rika kallon shari'ar kai-tsaye ta talabijin.

A Tanzania kundin tsarin mulki ta tsara cewa hukumar zabe ce ke da wuka da dama, kuma hatta Kotun Kolin kasar ba ta iya soke matakin da ta dauka.

'Yan Tanzania na kwatanta yadda shugaban hukumar zaben kasar wanda shugaban kasa ya nada, zai iya abin da takwaransa, Wafula Chebukati na Kenya ya yi, ko da kuwa jam'iyyar CCM da 'yan takararta ne suka yi rashin nasara.

'Yan kasar Tanzania na kallon kansu a matsayin mutane masu son zaman lafiya, a kasar da ke da sama da kabilu 100 ba kamar a Kenya ba inda kabilanci ke tasiri a zabe.

A lokacin da marigayi Mr Magufuli ya ziyarci Kenya a karon farko bayan zamansa shugaban kasa a 2016, ya fadi cewa ''da a ce Kenya za ta magance kabilanci, da ta zama kasar da babu irinta.''

Sai dai kuma a zaben da ya gabata, kabilanci bai yi wani tasirin a zo a gani ba, lura da yadda Mr Ruto ya saka batun tattalin arziki a gaba wurin yakin neman zabe.

Hakan ya burge yan Tanzania, ganin irin yadda dimokradiyya ke dada gyaruwa a Kenya.

'Yan kasar Tanzania na ganin cewa bai kamata saboda a zauna lafiya su bari a rika yi musu magudi da yadda aka ga dama ba a lokacin zabe. A ganinsu zaben Kenya ya fito da bukatar da suke da ita a fili, ta neman a sabon kundin zabe.

Da dama na ganin yin hakan zai ba da dama garambawul ga hukumar zabe da kotuna, da ake tunanin su yi aiki ba sani ba sabo.

Shugaba Samia Saluhu Hassan, wadda ta karbi mulki bayan mutuwar Mr Magufuli a 2021, ta yi alkawarin magance matsalar da yan adawa ta samar da sabon kundin tsarin mulki, to amma ba bu masaniya kan ko yaushe hakan za ta faru.

Kuma babu wata alama da ta nuna cewa jam'iyyar CCM ta shirya rasa mulki, yayin da jiran zuwan zaben 2025.