Ina cikin tashin hankali tun bayan sace ƙawayena a jami'ar Gusau - Ɗaliba

    • Marubuci, Ibrahim Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Fatima, wadda muka ɓoye sunata na gaskiya, na daga cikin ɗalibai mata da Allah Ya yi wa gyaɗan dogo a harin da ƴan bindiga suka kai jami'ar Tarayya da ke Gusau, arewa maso gabashin Najeriya.

A lokacin harin na daren 22 da watan Satumba, ƴan fashi ɗauke da makamai sun sace mutane kimanin 40, waɗanda yawanci ɗalibai ne ƴan mata da ke zama a gidajen da ƴan kasuwa suka gina domin bai wa ɗalibai haya a wata unuguwa da ake kira Sabon Gida.

Akasarin ɗalibai mata na jami'ar na zama ne a irin waɗannan gidaje kasancewar babu isassun wurin kwanan ɗalibai a cikin makaranta.

Fatima, wadda a yanzu take a shekara ta biyu a karatun digiri da take yi a jami'ar, ta ci sa'a ba ta nan a ranar da ibtila'i ya afka wa gidan ɗalibai da take haya, sai dai lamarin ya rutsa da ƙawayenta uku.

Ta ce "na so na koma makaranta bayan kammala hutu, amma sai yayana ya ce min na dakata tukuna saboda ƴan fashi na yin barazana ga makarantarmu."

Hakan ne ya sanya tun bayan buɗe makarantar bayan hutun zangon karatu da ya gabata, sai Fatima ta riƙa zuwa ɗaukar darasi daga gida, kasancewar tana zaune ne a wani gari da ke maƙwaftaka da Gusau, babban birnin jihar.

Takan kashe aƙalla naira 2,000 a kowace rana domin zuwa da dawowa daga jami'ar a kowace rana.

Hakan ba ƙaramin aiki ba ne a ƙasa kamar Najeriya, wadda al'ummarta ke kokawa kan tsadar rayuwa da ƙarancin kuɗi a hannun jama'a.

Duk da cewa hukumomin jami'ar sun sanar da cewa an samu nasarar karɓo mutum 16 daga cikin waɗanda aka sace, har yanzu babu labarin sauran ɗaliban.

Cikin waɗanda suke ci gaba da kasancewa a hannun ƴan bindigar har da ƙawayen Fatima, su uku.

Ta ce: "Yanzu haka ko bacci nake yi su ne a raina, mafarkinsu nake yi."

"Gaskiya tun da abin ya faru ban ƙara samun kwanciyar hankali ba." In ji ta.

Ba wannan ne karon farko ba

Fatima ta shaida wa BBC cewar wannan ba shi ne karon farko da ake yin garkuwa da ɗaliban makarantar ba, sai dai wannan ya ja hankali ne saboda an kwashi ɗalibai da yawa.

Ta ce: "Ana shigowa tun ba yau ba, ana ɗauka ɗaya bayan ɗaya daga cikin ɗalibai, daga baya iyaye sukan biya kuɗi a amso su."

Tun farko, bayanai sun nuna cewa an yi ta raɗe-raɗin cewa akwai yiwuwar ƴan fashin dajin waɗanda suka addabi jihar ta Zamfara da maƙwaftan jihohi za su iya kai hari a jami'ar, kasancewar sun kai hare-hare a unguwannin da ke maƙwaftaka da ita.

A watan Afrilu ma rundunar ƴan sandan Njeriya a jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace sun sace ɗalibai mata guda biyu na jami'ar tarayyar da ke Gusau a jihar Zamfara, daga unguwar da maƙwaftaka da jami'ar.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce: "ƴan sanda sun samu rahoton sace ɗaliban a ɗakunan kwanansu da ke a wajen makarantar, kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta tura jami'anta zuwa wajen da lamarin ya auku. Sai dai kafin zuwan jami'an tsaron 'yan fashin sun tsere da ɗaliban."

Ko a farkon shekarar 2022 irin waɗannan ƴan bindiga sun shiga unguwar Damɓa da ke maƙwaftaka da jami'ar, inda suka sace tare da yin garkuwa da mutum biyar daga cikin iyalan wani malamin jami'ar.

Kuma kwana guda bayan haka suka buƙace shi da ya biya miliyoyin kuɗi kafin a sako su.

'Rashin tsaro zai hana ƴaƴan talaka karatu'

A yanzu dai Fatima ta buƙaci hukumomi a Najeriyar su samar da tsaro a jami'o'i da kuma sauran makarantu da ke faɗin yankin domin bai wa yara damar yin karatu.

Domin a cewar ta matuƙar hakan ba ta samu ba to akwai yiwuwar lamarin ya hana yara zuwa makaranta.

Ta ce: "Ya kamata a kai security (tsaro) jami'o'i domin idan ba haka ba, a kwana a tashi wata rana karatun jami'a zai zama mai wahala gare mu ɗiyan talakawa saboda irin yadda suke shiga jami'o'i suna ɗaukar ɗalibai."

Ta ƙara da cewa "Ya kamata a samu mafitar da za ta kawo ƙarshen wannan al'amarin, shi ne kawai abin da zan ce."

Satar ɗalibai a makarantun Najeriya

Sace ɗaliban jami'ar tarayya ta Gusau dai ba shi ne karon farko ko na biyu ko ma na uku ba da ƴan bindiga ke kai hari a makarantu suna kwashe ɗalibai ba arewacin Najeriya.

Matsalar ta fito fili ne tun ranar 15 ga watan Afrilun 2014, lokacin da matsalar tsaro ta tsananta sanadiyyar rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.

A lokacin ne mayaƙan Boko Haram suka sace ɗalibai 276 daga makarantar sakandaren mata ta garin Chibok a jihar Borno.

Duk da cewa an ceto wasu daga cikin su, wasu kuma sun tsere daga inda aka tsare su, amma har yanzu akwai da dama daga cikin ƴanmatan waɗanda ba a san halin da suke ciki ba.

Matsalar satar ɗaliban a makarantu ta kuma ƙara ƙamari ne sanadiyyar sabbin matsalolin tsaro a arewa maso yamacin ƙasar.

Ƴan fashin daji waɗanda suka kwashe shekaru suna addabar jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Neja sun ari wannan ɗabi'a sun yafa.

Ko a ranar Larabar nan ƴan bindiga sun sace kimanin ɗalibai mata biyar na jami'ar tarayya da ke Dutsin Ma a jihar Katsina.

BBC ta gano cewa lamarin ya faru ne a cikin dare da misalin karfe biyu a ɗakunan kwanan da dalibai ke kamawa a wajen makarantar.

A watan Fabarairun 2021 ma rundunar ƴan sandan Najeriya ta tabbatar da sace ɗalibai mata 317 daga makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a Jihar Zamfara.

A cikin watan Yunin 2021 irin waɗannan ƴan bindiga sun kai hari a makarantar sakandaren gwamnatin tarayya ta Birnin Yauri a jihar Kebbi, inda suka sace ɗalibai sama da 100 tare da malamansu.

Haka nan a ranar 5 ga watan Yulin 2021 ne 'yan bindigar suka kutsa makarantar Bethel Baptist da ke kan titin Kafanchan zuwa Kaduna, inda suka sace ɗalibai 121.