Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan ƙasashen waje ne ke taimaka wa 'yan ta'adda a Najeriya - Sheik Gumi
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheik Ahmad Mahmud Abubakar Gumi, ya ce suna zargin cewa manyan ƙasashen waje ne suke taimaka wa 'yan bindiga da 'yan ta'adda a Najeriya.
A hirarsa da BBC malamin ya ce idan aka yi la'akari da irin yadda matsalar tsaron da najeriya ke fama da ita ta ƙara ta'azzara a 'yan kwanakin nan alamu na tabbatar da zargin da suke yi na hannun manyan ƙasashe a matsalar.
Malamin ya ce kafin yanzu ana samun raguwar hare-hare inda ya bayar da mislai da hanzyr Abuja zuwa Kaduna inda ya ce a da wannan hanya ta zama takmar wani tarko ga masu bin hanyar, amma yanzu kusan abin ya zama tarihi.
Haka kuma ya ce a yanzu wasu manoma da dama sun koma suna gudanar da harkokinsu na noma a yankin Birnin Gwari, saɓanin irin yadda hakan ba zai yiwu ba a baya.
Sai dai ya ce lamarin ya sake tasowa ne a yanzu bayan da aka yi magana da ƙasashen waje a kwanakin nan a kan Najeriyar:
''Akwai magana da aka yi daga ƙasashen waje wanda kuma mu tuntuni muna zargi waɗannan 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayin addini daga kayan aikinsu mun gane cewa daga waje ake taimaka musu.''
Gumi ya ƙara jaddada hakan inda ya ce : ''Mutanen waje ne masu ƙarfi masu arziƙi masu kuma iya kutsawa cikin al'amarin ƙasashe su ke yi. Wannan abu ne da ake maganarshi a duniya sosai.''
Dangane da yadda ake samun ƙaruwar hare-hare da tashin hankali mai nasaba da tsaro a Najeriyar a kwanakin nan kuwa, Gumi ya ce:
''Ba abin mamaki ba ne in an tuhumi Najeriya da wani abu wani rikici ya tashi don ya nuna abin haka ne.''
A kan yadda yake da ra'ayin yin sulhu da 'yan bindiga, har ma wasu na ganin kamar ya san masu tayar da hankalin malamin ya ce : ''Ai kowa ma ya san su. To amma abin da ba a magana a kai shi ne. Mene ne sababin mutanen da a da muna zaune lafiya da su, suka rikice mana suka zamar mana annoba cikin al'umma? Akwai dalili.''
Ya ce : ''Akwai mutane biyu in sun yi abu ba a mamaki - mahaukaci da jahili. ba wani abu da za ka yi bayani da zai iya cewa ɓarna gaskiya ce babu shi.''
''Wato duk abin da suke yi ɓarna ce. To amma waye mai hankalin da zai gaya musu kar su yi? Mu da muka yi ƙoƙarin shiga mu gaya musu wannan haramun ne, cin dukiyar mutane haramun ne, kamu haramun ne, lokacin waccan gwamnatin ba ta ba mu goyon baya ba, da yanzu an gama da wannan babin.''
''Matuƙar ba a yi maganin tsatson abin da ya kawo wannan fitina ba haka za ta ci gaba,'' in ji malamin.
Ya ƙara da cewa, bai kamata mutane su rinƙa tunanin kamar yana goyon bayan 'yan bindigan ba, ''domin ko addinin mu bai yarda da zalunci ba, abin da muke yi muna yi ne tsakani da Allah.''
Sannan game da kalaman da sabon ministan tsaron Najeriyar, Janar CG Musa mai ritaya ya yi na cewa babu sulhu da 'yan bindiga, Sheik Gumi ya ce hakan da ya yi daidai ne domin, '' bai kamata soja ya yi sassauci ba, saboda su ma su san cewa sulhu bai yiwuwa sai da karfi.''
Dangane da jagoran haramtacciyar ƙungiyar 'yan a-ware ta Biafra kuwa Nnamdi Kanu, wanda kotu ta yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samunsa da laifin ta'addanci, malamin ya ce masalahar zaman lafiya ce ta sa shi tayin neman afuwa ga jagoran Kanun.
Fitaccen malamin ya ce matuƙar Kanu zai yarda da sharruɗansa, ya nuna nadama kan abubuwan da yake yi ya tuba, ya umarci mutanensa su ajiye makamai, ya ce, ba shakka zai nema masa afuwa kamar yadda yake da'awar a yi sulhu da 'yan fashin daji.
Malamin ya bayar da mislain yadda Shugaba Shehu Shagari ya yi wa Ojukwu afuwa a kan yaƙin basasar da aka kashe mutum sama da miliyan biyu, da kuma yadda Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ya yi wa masu tayar da ƙayar baya a yankin Naija Delta afuwa.
Ya ce, ''kullum muna neman afuwa don afuwar na sa a rage kakkashe waɗansu mutanen na daban.''