Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ‘Yanbindiga suka dasa bama-bamai a kan hanya a Zamfara
A Najeriya, ana can ana kokarin tantance irin ta'adin da fashewar wasu bamabamai biyu da aka dasa a kan hanyar Dansadau zuwa Gusau a jihar Zamfara, suka yi.
Bayanan da aka fara samu sun nuna cewa mutum goma sha daya suka rasu a fashewar, amma hukumomi sun ce yawan bai wuce mutum bakwai ba.
Ana dai zargin wannan wani salon harin ramuwar gayya ne 'yan bindiga suka kaddamar, game da kisan da 'yan sa-kai suka yi wa wasu 'yan bindiga da mukarrabansa a makon jiya a yankin.
Yanzu haka dai ana can cikin jimami da zaman jugum, da kuma dakon tantance matafiyan da ko dai suka jikkata ko ma suka rasu sakamakon fashewar
Yadda abin ya faru
Wani mutumin yankin, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya yi wa BBC karin bayani game da aukuwar wannan hari:
''Mutane sun bi ayarin sojoji tare da motoci zuwa Gusau kawai sai bam ya tashi. Masu babura da suka hau bam din nan duka ya tarwatse da su. Akalla an rasa rai na mutum biyar nan take.
''Aka taka na biyu kuma ita ma motar da ta taka shi ya tashi da ita har an rasa mutum biyar. Wata mata motar da ke kusa da ita ta taka ta Allah Ya sa kwananta sun kare. Lokacin da muka tattara bayanan nan kusan gawa 11. Akwai kuma wasu da suka ji rauni,'' in ji mutumin.
Ya kara da cewa: ''Daman tare ake tafiya da rakiyar jami'an tsaro to lokacin da bam na farko ya tashi sai 'yan bindigan nan suka dawo suna harbin mutane. To cikin yardar Allah tankar sojoji tana kusa, sai suka yi ta ba-ta-kashi.''
''Wannan shi ne na biyu ko na uku don an taba samun aukuwar irin haka wata shida ko bakwai baya a daidai wannan wajejen da wannan ya tashi, nan ma 'yan ta'addan sun taba dasa bam kuma ya tashi shi ma ya yi ta'adi ya tarwatsa wasu motoci a wancan lokacin.''
Gwamnati ta tabbatar
Shi ma Mustafa Jafaru Kaura, babban mataimaki na mausamman ga gwamnan jihar ta Zamfara kan harkokin yada labarai, ya tabbatar da labarin aukuwar wannan lamari: ''Wannan lamari ya faru Asabar din nan ne a daidaidai wani kauye da ake ce ma Maiayaya cikin ita wannan hanya ta Dansadau.''
''Bayanai na farko-farko sun ce mutum bakwai suka rasu amma watakila a kara samun karin bayani.'' in ji shi.
Jami'in ya kuma danganta kai harin da abin da ya ce ramuwar-gayya: ''Ramuwar-gayya ce barayin suke so su yi ma wasu 'yan sa-kai bisa ga kisan da aka yi ma nasu mutanen ciki har da wani kacallansu a ranar Juma'a da ta gaba a Magami.''
Haka kuma ya ce gwamnatin jihar ta umarci duk inda irin wannan abu ya faru karamar hukuma ta dauki nauyin maganin wadanda abin ya rutsa da su.
Sannan ya ce gwamnatin jihar ta kuma kuduri aniyar gyara hanyar, kasancewar lalacewarta ce ta sa barayin ke samun dama har su dasa bam.
Fashewar bama-baman a kan hanyar ta Dansadau zuwa Gusau a jihar Zamfara dai, wani tsokaci ne game da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da bibiyar shiyyar arewa maso yammacin Najeriya,.
Kuma hakan na faruwa duk kuwa da kokarin da hukumomi da jami'an tsaro kan bayar da tabbacin suna yi, don magance matsalar.