An kama mutum huɗu kan zargin nuna wariya ga Vinicius Jr

Asalin hoton, Getty Images
An kama mutum huɗu a Spain da ake zargi da shirya wani gangamin nuna wariyar launin fata a intanet ga ɗan wasan Real Madrid Vinicius Jr.
Gangamin zai mayar da hankali ne wajen yadda magoya baya za su riƙa nuna wariya ga ɗan wasan da zagi da kuma cin zarafi, ana ce musu su sanya baƙin takunkumin fuska ta yadda ba za a riƙa gane su ba, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.
A farkon wannan shekarar ne ɗan wasan Brazil ɗin mai shekara 24 ya ɓarke da kuka yayin taron manema labarai da ya bayar da labarin yadda ya riƙa fama da wariyar, yana cewa ya ji tamkar ba shi da wani muhimmanci saboda yana yawan abubuwan da suka faru da shi.
An kama mutanen ne a ranarkun 14 da kuma 15 ga watan oktoba sannan daga baya aka sake su amma ana ci gaba da bincike.
'Yan sandan Spain ba su bayyana sunayen mutanen da aka kama ba wadanda aka yi musu tambayoyi, babu kuma wata sanarwa da aka fitar daga wani lauya mai kare su.
Sun ƙara da cewa ana yi binciken ne a buɗe kuma hakan zai iya kai wa ga kama ƙarin wasu mutanen, bayan gangamin intanet din da suka yi ya ja hankali sosai.
Kamun farko da 'yan sanda suka yi da ke da alaƙa da wannan gangamin an yi shi ne a ranar 29 ga watan Satumba lokacin da ake shirin wasan hamayya a Atletico Madrid.
Duk da cewa babu rahoton nuna wariya da aka samu a yayin wasan, amma jami'ai sun dakatar da wasan na wani lokaci saboda abubuwan da aka riƙa jefawa cikin filin wasa.
An kama wasu magoya bayan Valencia a watan Yuni inda aka ɗaure su wata takwas a gidan yari saboda zagin ɗan wasan gaban Madrid ɗin a watan Mayun 2023.
A watan Agusta ya ce shi da abokan wasansa na Brazil za su bar filin wasa duk lokacin da aka ƙara nuna musu wariyar launin fata a wannan kakar.
Yana cewa hanya ɗaya da za a kawar da wariya yayin wasa shi ne ficewa daga filin wasan baki ɗaya.











