Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sudan na ƙara faɗawa matsalar yunwa - Rahoto
Hukumar da ke nazari tare da bayar da bayanai a kan matsalolin da suka danganci karancin abinci, da ke da alaka da Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargadin cewa matsalar karancin abinci na ci gaba da yaduwa a fadin Sudan.
Hukumar ta IPC, ta ce tuni yankuna biyar suka fada cikin wannan matsala a yankin Darfur da jihar Kordofan ta Kudu.
A rahoton da ta fitar wanda Majalisar Dinkin Duniya, da sauran hukumomi ke amfani da shi, kungiyar ta ce akwai kuma wasu yankuna biyar da za su iya fadawa wannan matsala daga yanzu zuwa watan Mayu na shekara mai kamawa, saboda yakin basasar da ake ci gaba da yi a kasar ta Sudan da kuma rashin samar da kayan agaji.
Sama da mutum dubu 600 ke cikin yunwa, sannan sama da miliyan 24 da rabi na bukatar agajin gaggawa na abinci- kusan rabin al'ummar kasar kenan.
A kan hakan ne jami'ar hukumar abinci da ayyukan gona ta Majalisar Dinkin Duniya, Dervla Cleary ta yi kira da a dakatar da tashin hankalin na Sudan ba tare da wani jinkiri ba domin a samu a kai kayan agaji;
Ta ce ; ''Halin da ake ciki a Sudan ya yi matukar muni. Abu ne da ba za a lamunta da shi ba a duniya irin ta yau, inda ake da yalwa sosai ka ga mutane na mutuwa saboda yunwa.
Ko kadan wannan bai kamata ya rika faru ba a yau. To amma abin da muke bukata matukar bukata shi ne samun hanyar kaiwa ga mutane. Muna bukatar a dakatar da tashin hankalin domin mutane s samu hanyar samun abinci, da ruwa da lafiya da ababan gina jiki da aikin gona.'' In ji ta.
Hukumomin Sudan sun yi watsi da rahoton kungiyar da cewa yunkuri ne na kafar ungulu ga yancin kasar.
Shekara biyu da kazamin yakin basasar a Sudan, ana zargin bangarori biyu da ke yaki da juna wato rundunar sojin kasar da kuma kungiyar RSF da datse hanyoyin kai agaji.