Sudan: Yadda uwa ta miƙa kanta a yi mata fyaɗe domin tseratar da ƴarta

    • Marubuci, Barbara Plett Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa correspondent, Omdurman
  • Lokacin karatu: Minti 4

Sudan na cikin matsanancin hali

Bayan wata 17 ana gwabza yaƙin basasa da ya ɗaiɗaita ƙasar Sudan, rundunar sojin ƙasar ta kai wani hari a babban birnin ƙasar, Khartoum da niyyar kai hari a kan dakarun RSF.

Dakarun RSF sun ƙwace iko da mafi yawan birnin na Khartoum tun a farkon rikicin, sojojin kuma suna riƙe da birnin Omdurman, wanda ke kusa da Khartoum da zarar an tsallaka kogin Nilu.

Amma har yanzu akwai wasu wuraren da mutane suka iya zuwa a tsakanin biranen biyu.

A ɗaya daga cikin irin waɗannan wuraren ne na ci karo da wasu mata waɗanda suke yin tafiyar awa huɗu zuwa wata kasuwa da sojoji ke kula da ita a ƙarshen Omdurman, inda ake samun abinci mai rahusa.

Matar ta zo ne daga yankin Dar es Salaam, wanda ke ƙarƙashin ikon dakarun RSF.

Mazan matan yankin duk sun tsere, kamar yadda suka bayyana min saboda dakarun RSF suna bugunsu, su ƙace musu kuɗi, a wasu lokuta su tsare su, su ce sai an kawo kuɗi za su sake su.

“Muna shan wahala saboda ko abincin ciyar da yaranmu ma ya gagare mu. Muna fama da yunwa, muna buƙatar abinci,” in ji ɗaya daga cikin.

Gargaɗi; Wasu daga cikin bayanan rahoton nan suna da ɗaga hankali

Sai na tambaye su, matan fa, yaya suka rayuwa ba tare da mazan su ba? ba za a musu fyaɗe ba?

Sai ɗaya daga ciki ta cigaba, "Da yawanmu a nan an ci zarafinmu, amma ba za su yi iya yin magana ba," in ji ta a cikin hawaye. "Ku mun yi maganar ma, me zai faru?"

Ta cigaba da cewa, "wasu ƴan matan idan sun dawo daga kasuwar nan, dakarun RSF suna tare su, su tafi da su, inda suke yin kwana biyar zuwa shida."

Tana magana, mahaifiyarta na gefe ta sunkuyar da kai. Wasu matan kuma sun kuka.

"Idan ƴarki ta fita, za ki bar ta a hannunsu ne?"

"Ba za ki fita nemanta ba? yaya za ki yi? babu abin da za mu iya yi, kuma babu wanda ya damu wa halin da muke ciki. Ina mutanen duniya suke? me ya sa ba su taimaka mana ba?

Matafiya ma sun bayyana yadda suke fuskantar ƙalubale na sata da ƙwace a yaƙin, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya raba sama da mutum miliyan 10.5 da muhallansu.

Amma cin zarafin ne ya fi ɗaukar hankalin mutane a yaƙin wanda ya faro daga rikicin neman mulki tsakanin dakarun RSF da rundunar sojin ƙasar.

Kwamishinan Haƙƙin ɗanAdam na Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Turk ya ce ana amfani da fyaɗe a matsayin "makamin yaƙi."

Ita ma wata mata ta bayyana wa BBC yadda dakarun RSF suka mata fyaɗe.

Mun haɗu da ita ne a kasuwar, wadda ake kira Souk al-Har - wato Kasuwar Zafi.

Tun bayan ɓarkewar yaƙin ne kasuwar take ƙara faɗaɗa saboda talakawa suna samun sauƙin kayayyaki

Miriam - ba asalin sunanta ba ne amma - ta tsere ne daga gidansu da ke Dar es Salaam, inda yanzu take samun mafaka tare da ɗanuwanta.

Yanzu tana aiki ne a wajen sayar da shayi. Ta ce a farkon yaƙin, wasu mutum biyu ɗauke da makamai sun shigo gidanta suka yi yunkurin yi wa ƴaƴanta mata masu shekara 17 da mai shekara 10 fyaɗe.

"Sai na ce yaran nawa su tsaya a bayana, inda na faɗa wa dakarun RSF ɗin cewa: 'idan fyaɗe kuke so ku yi, to sai dai ku min," in ji ta.

"Sai suka buga min wani abu, suka ce in kwaɓe. Amma kafin in kwaɓe sai da na ce yaran su fita. Sauran suka kwasa wasu yara suka tsallafa katanga, wani kuma ya tsaya ya min fyaɗe."

Dakarun RSF ɗin sun ce faɗa wa masu bincike na duniya suna duk ƙoƙarinsu na hana cin zarafi.

Amma an sha samun labaran cin zarafi da dama a wurare daban-daban.

Fatima - ba asalin sunanta ba ne- ta fada min cewa ta zo Omdurman ne domin haihuwa na ƴanbiyu, sannan ta ƙuduri aniyar cigaba da zama.

Ɗaya daga cikin maƙwabtanta, ta ce wata mai shekara 15 ma ta ɗauki ciki, bayan an musu fyaɗe ita da wata mai shekara 17.

Da suka tsala ihu sai maƙwabta suka fito, amma dakarun na RSF suka kore su, suka ce duk wanda bai koma ba za su harbe shi.

Washegari sai suka tsinci wasu mata ƙanana guda biyu da alamar an ci zarafinsu, an kuma kulle ɗanuwansu namiji a wani ɗaki.

"Tun da aka fara yaƙin, da RSF suka zo, sai muka fara jin labaran fyaɗe. Tun muna ji daga nesa, har ya zo kusa da mu," in ji Fatima.

Da suka gama cin kasuwa, haka nan suka fara shirin komawa inda dakarun na RSF suke da iko.

Babu yadda za su yi, dole su koma duk da barazanar da suke fuskanta.