Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda China ke sauya fannin iliminta da ƙirƙirarriyar basira
- Marubuci, Laura Bicker
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC a China
- Aiko rahoto daga, Beijing
- Lokacin karatu: Minti 5
Kansa a dafe da hannayensa, Timmy mai shekara takwas da haihuwa na faman yadda zai doke mutum-mutumi mai basira yayin wani wasan dara - ko kuma chess a Turance.
Sai dai ba fa a wani ɗakin gwaji ko bincike hakan ke faruwa ba, mutum-mutumin na zaune ne a wani shagon shan shayi da ke birnin Beijing tare da Timmy.
"Kamar wani malami ne a gare ni, ko kuma aboki," a cewar yaron yayin da yake faɗa wa mahaifiyarsa salon da zai bi a faifan wasan darar.
Jim kaɗan bayan haka, mutum-mutumin ya ce: "Ina taya ka murna! Ka yi nasara."
China na rungumar ƙirƙirarriyar basira ta AI domin mayar da kanta ƙasaitacciyar ƙasa a fannin fasaha nan da 2030.
Manhajar DeepSeek, sabon shafin nan mai ƙirƙirarriyar basirar hira da mutane da ta ja hankalin duniya a watan Janairu, wata alama ce kawai ta neman cika wannan burin.
Akwai kamfunna sama da 4,500 da ke haɗawa da kuma dillancin AI. Makarantu a birnin Beijing sun fara koya wa yara 'yan firamare darussan AI kafin 'yan sakandare a cikin wannan shekara. Su kuma jami'o'i sun ƙara yawan gurabe ga ɗalibai masu nazarin basirar AI.
"Wannan abu ne da ya zama dole,. Rayuwarmu za ta koma ta AI," a cewar mahaifiyar Timmy, Yan Xue. "Ya kamata yara su san ta tun farkon rayuwarsu. Bai kamata mu zubar da ita ba."
Babu mamaki wannan ne abin da jam'iyyar kwamunisanci ta nufata lokacin da ta ayyana a 2017 cewa basirar AI ce "za ta zama jagora" a cigaban ƙasar. Yanzu Shugaban Ƙasa Xi Jinping na zuba kuɗi a harkar sosai.
China na da niyyar zuba jarin yuan tiriliyan 10 (kusan dala tiriliyan 1.4) domin yin gogayya da Amurka a fannin cikin shekara 15 masu zuwa.
Wannan na zuwa ne bayan jarin yuan biliyan 60 da aka ƙaddamar a watan Janairu 'yan kwanaki bayan Amurka ta ƙara tsaurara sayar wa China kayayyakin ƙirƙire-ƙirƙire tare da saka wa ƙarin kamfanonin China takunkumai.
Amma DeepSeek ya nuna cewa kamfunnan China za su iya jurewa, kuma abin da ya ɗaure wa ƙasaitattun kamfunnan Amurka kai kenan - ba su taɓa tunanin China za ta kamo su nan kusa ba.
Gasa tsakanin 'yan ƙasa
Kamfanin SenseRobot ne ya ƙirƙiri faifan darar Timmy da ke iya yin abubuwa da dama - ciki har da cinye manyan ƙwararru a cacar.
"Iyaye na tambayar farashin, amma sai sun ƙara da tambayar ɗan asalin ina ne ni. Suna tsammanin daga Turai nake ko kuma Amurka. Sai ka ga sun yi mamaki idan na ce musu daga China nake," in ji Mista Tang, wanda ke tallan faifan wasan darar ta chess.
"Kodayaushe sai sun ɗan yi shuru na 'yan daƙiƙoƙi idan na ce musu ni ɗan China ne,"
Kamfaninnsa ya sayar da sama da faifai 100,000, yanzu kuma ya ƙulla yarjejeniya da wani katafaren shagon sayar da kayayyaki a Amurka mai suna Costco.
Ɗaya daga cikin sirrin cigaban da Chinar ta samu shi ne matasanta. A 2020, sama da ɗalibai miliyan uku da rabi ne suka kammala jami'a da digiri a fannin kimiyya da fasaha, injiniyanci da lissafi abin da ake yi wa laƙabi da STEM a Turance.
Sama da kowacce ƙasa kenan a duniya - kuma ta zaƙu ta ga ta yi amfani da wannan damar.
"Ƙarfafa matsayinmu a fannin ilimi, da kimiyya haƙƙinmu da rataya a kan kowa," kamar yadda Shugaba Xi ya faɗa wa shugabannin jam'iyyarsa a makon da ya gabata.
Tun bayan da China ta buɗe ƙofar tattalin arzikinta ga duniya a shekarun 1970, "ba ta da aiki sai neman ƙwararru da kuma kimiyya," in ji Abbott Lyu, mataimakin shugaban kamfanin Whalesbot da haɗa mutum-mutumin AI.
Kamfanin na ƙiƙirar 'yartsana mai ƙirƙirarriyar basira da ke taimaka wa yara koyon sarrafa kwamfuta. Kowane ƙunshi na zuwa da takardun koyarwa, sai yaran su zaɓi abin da suke so su koya da kuma yadda za su koya. Mafi araha na kaiwa dala 40.
"Sauran ƙasashe na da 'yartsanonin koyarwa su ma, amma idan ana maganar gasa da kuma kyawun basirar, China ta ɗara saura," in ji Mista Lyu.
Nasarar da DeepSeek ta samu ta sa shugaban kamfanin ya zama wani gwarzo na ƙasa kuma yanzu "arzikinsa ya kai yuan biliyan 10 saboda tallace-tallacen da yake yi a fannin basirar AI ta China," cewarsa.
Yanzu ana yi wa wasu kamfunnan China shida, cikinsu har da DeepSeek, laƙabi da sunan ƙananan dabbobin dragon shida - sauran su ne Unitree Robotics, Deep Robotics, BrainCo, Game Science, Manycore Tech.
'Ƙoƙari'
Yayin da duniya ke ci gaba da shaida cigaban China a fannin AI, akwai kuma fargabar abin da Chinar ke iya yi da basirar a kan masu amfani da ita.
AI na buƙatar bayanai sosai - yawan bayanan da aka zuba mata, girman basirarta kenan. Yayin da mutum kusan biliyan ɗaya ke amfani da wayar salula a China, ƙasar na da dama fiye da Amurka, wadda ke da miliyan 400 da 'yar ɗoriya kacal.
Ƙasashen Turai da ƙawayensu na ganin cewa bayanan da China ke tattarawa ta hanyar manhajojinta kamar DeepSeek, RdNote, ko TikTok jam'iyya mai mulki za ta iya yin amfani da su.
Wasu kan ce sabuwar dokar tattara bayanan sirri da ƙasar ta kafa ɗaya ce daga cikin dalilansu na faɗin hakan.
Sai dai kamfunnan China kamar ByteDance da ya mallaki TikTok, ya ce dokar ta bai wa kamfunna da kuma tsare bayanan masu amfani da su kariya. Duk da haka Amurka ba yarda ba, har ma ta rufe dandalin TikTok a ƙasar.
Akwai kuma maganar tsare bayanan sirri, wadda ta ci karo da tsaron ƙasa. Koriya ta Kudu ta haramta sauke mahnajar DeepSeek, yayin da Taiwan da Australiya suka hana amfani da ita a kan na'urorin gwamnati.
Yanzu babban ƙalubalen shi ne ta yadda za a aiwatar da ayyuka masu yawa da kuɗi kaɗan.
Mista Tang ya ce kamfaninsa ya fahimci cewa wasu daga cikin kayan haɗa 'yartsanar na da tsada matuƙa, kuma zai iya jawo hauhawar farashi zuwa kusan dala 40,000.
Saboda haka ne suka fara yin amfani da basirar AI wajen maye gurbin injiniyoyi a kamfanin. Ya ce hakan ya sa farashin ya koma dala 1,000.