Villa na son Sancho, Newcastle na harin Trafford

Jadon Sancho

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Aston Villa ta kasance ƙungiya ta baya-bayanan da ke nuna zawarcinta kan ɗan wasan Ingila, Jadon Sancho mai shekara 25 daga Manchester United wanda ke zaman aro a Chelsea. (Teamtalk)

Newcastle United ta ƙwallafa rai kan mai tsaron raga a Burnley da Ingila, James Trafford mai shekara 22. (Times - subscription required)

Liverpool ba ta da niyyar sayar da ɗan wasanta na Colombia, Luis Diaz mai shekara 28, kuma babu wanda ya mika mata tayi, duk da cewa ana raɗe-raɗin wai Barcelona da Al-Nassr na Saudiyya sun kwaɗaitu. (Times - subscription required)

Amma ya dace Diaz ya tafi?, Ɗan wasan Newcastle da aka yi wa kuɗi har £80m daga Ingila, Anthony Gordon mai shekara 24, ake ganin Liverpool ke son maye gurbinsa da shi. (Teamtalk)

Ƙungiyar Liverpool na iya kalubalantar Arsenal kan ɗan wasan Belgium, Sesko daga RB Leipzig, matashin mai shekara 22 daga Slovenia an kiyasta kuɗinsa a kan £67m. (TBR Football)

Harvey Elliott na iya komawa ƙungiyar Seria A idan ɗan wasan na tsakiya a Ingila mai shekara 22, ya bar Liverpool. (Football Insider)

Everton sai ta cika sharuɗan rabuwa da Thierno Barry na yuro miliyan 40 kamar yadda yake a kwantiraginsa, kafin ta iya sayen shi daga Villarreal. (Teamtalk)

Chelsea a shirye take ta biya £25m kan ɗan wasan AC Milan mai tsaron raga da ke da shekara 29, Mike Maignan. (Standard)

Brentford na son naɗa kocin Ipswich, Kieran McKenna, inda kocinta na yanzu Thomas Frank ya tafi maye gurbin, Ange Postecoglou a Tottenham. (Football Insider)

West Ham ta tuntubi Club Brugge kan sayen ɗan wasan Najeriya, mai shekara 24, Raphael Onyedika, amma tana fuskantar kalubale daga AC Milan. (TBR Football)

Manchester City da Barcelona na zawarcin ɗan wasan Arsenal mai shekara 15, Max Dowman. (FootballTransfers)