Yadda ƴanbindiga ke tilasta wa manoma biyan haraji kafin girbe amfanin gona a Zamfara

Yanbindiga a Najeriya

Asalin hoton, @DanKatsina50

Lokacin karatu: Minti 2

Wasu manoma a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce ƴanbindiga sun tilasta masu biyan haraji kafin girbe amfanin gonarsu.

Mazauna yankin ƙananan hukumomin Tsafe da Talatar Mafara a jihar Zamfara sun ce ƴanbindigar sun mayar da yanzu gonaki wurin da suke kai hari, lamarin da ya jefa manoman yankin cikin tsoro da fargaba.

Wasu al'ummar yankin sun shaida wa BBC cewa sun biya ƴanbindigar maƙudan kuɗi kafin suka amince suka girbe abin da suka shuka.

"Na biya naira dubu 50 a gonata sannan aka bari na samu buhu uku na waken soya da na noma," in ji wani manomi a yankin Tsafe.

Ya ce ƴanbindigar sun tilasta masa sayo lemu da ayaba da ruwan roba na Swan kafin suka bari aka yi aikin girbin gonarsa.

"Akwai wani makwabcina sai da ya biya N350,000 kafin ya yi girbi, domin yanayin girman gonarka yanayin abin da za ka biya."

"Ba ka isa ka yi aiki a gonarka ba sai a gabansu kuma ba a gardama da su, duk abin da suka yanke haka za a biya," a cewarsa.

Ya ƙara da cewa sun kama wasu saboda ba su biya ƴanbindigar kuɗin da suka biya ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani manomi a yankin Tsafe a jihar Zamfara ya ce suna cikin tashin hankali domin ko an biya kuɗin suka dawowa su kwashe amfanin gonar.

"Wasu sun biya kuɗin tarar amma suka dawo suka kwashe abincin da suka noma," in ji shi.

Mazauna yankin sun ce a shirye suke su yi sulhu da ƴanbindigar saboda halin tashin hankalin da suke ciki na rasa abincin da suka noma kuma suke dogaro da shi.

Wannan ba shi ne karon farko da 'yanbindiga wadanda suka addabi yankuna a wasu jihohin yankin arewa maso yamma da suka hada da jihar ta Zamfara da Sokoto da Kebbi da Katsina ke tilasta wa manoma biyan haraji ba kafin girbe amfanin gona.

Masana tsaro a Najeriya sun ce akwai buƙatar baza jami'an tsaro domin yaƙar ƴanbindigar musamman a wannan lokacin da manoma ke girbe amfanin gona, domin kawar da barazanar ƙarancin abinci da za a iya fuskanta.

Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar ƴanbindiga masu fashin daji suna kashe mutane tare da satar mutane domin kuɗin fansa, kuma matsalar na ci gaba da ƙaruwa duk iƙirarin da hukumomi da jami'an tsaro ke na ƙoƙarin yaƙi da su.