Shin ya dace ƙasashen duniya su shiga damuwa kan halin da dajin Amazon ke ciki?

Taswirar dajin Amazon da ke Latin Amurka

Asalin hoton, BBC, Getty Images

    • Marubuci, Navin Singh Khadka, Antonio Cubero and Visual Journalism Team
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 7

Ana gudanar da taron sauyin yanayi wato COP30 na bana ne a birnin Belem da ke arewacin ƙasar Brazil, inda ake wa kallon hanya mafi sauƙi zuwa wajen shiga katafaren dajin Amazon, wanda shi ne daji mafi girma a duniya.

Shekara 10 bayan yarjejeniyar sauyin yanayi ta COP, inda aka shiga yarjejeniyar taƙaita illolin ɗumamar yanayi domin kare mutanen duniya.

Sai dai har yanzu babu wani sakamako a fili da aka gani, domin har yanzu ɗumamar yanayi na ci gaba da ta'azzara, kuma dajin Amazon, wadda ke laƙume kaso da yawa na sinadarin CO2 mai gurɓata muhalli, yana da matuƙar muhimmanci wajen samun wannan nasarar da ake buƙata.

Sai dai shi kansa dajin yana fuskantar ƙalubale babba da rashin tabbas, kamar yadda masana kimiyya suka bayyana.

Taswirar dajin Amazon
Bayanan hoto, Taswirar dajin Amazon

Brazil ce ke da kusan kashi 60 na dajin Amazon, inda ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare dajin tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya.

Dajin na ɗauke da albarkatu da dama da yanayi mai kyau da ruwa da sauran su.

Girmansa ya kai murabba'in ƙasa miliyan 6.7, kuma ya kai nunkin girman ƙasar India, kuma yana cikin dazukan da suka fi tattara albarkatu da arziƙi a duniya.

Daga cikin abubuwan da Amazon ya ƙunsa akwai:

- aƙalla nau'ukan tsirrai guda 40,000

- aƙalla nau'ukan dabbobi guda 427

- aƙalla nau'ukan tsuntsaye 1,300

- aƙalla nau'ukan dabbobi masu jan jiki guda 378

- sama da nau'uka 400 na dabbobin ruwa

- kusan na'ukan kifi 3,000

Kuma yawancin abubuwan da ake samu a dajin ba a samu a ko'ina a dajin na Amazon.

Hoton nau'ukan wasu dabbobi da tsirrai da ke dajin Amazon
Bayanan hoto, Hoton nau'ukan wasu dabbobi da tsirrai da ke dajin Amazon
.

Tekun Amazon ne taku mafi girma a duniya, wanda yake kwarara zuwa tekun Atlantika kuma yana taka rawa a tekunan duniya, wanda kuma hakan ke taka rawa wajen saisaita ɗumamar yanayi a duniya.

Dajin na taimakawa wajen janye sinadarin carbon, duk da cewa akwai wasu yankunan dajin da aka gano sun fara fitar da sinadarin CO2, sannan dajin yana taimakawa wajen samar da abinci da magani.

Me ke faruwa yanzu?

Ƙungiyoyin masu kare muhalli sun ce an rasa wajen kashi 20 cikin ɗari na dajin, kuma an lalata wani kashin kamar wannan na dajin a sanadiyyar ayyukan mutane da suka haɗa da noma da kiwo da sare itatuwa domin yin katako da kuma haƙar ma'adanai - sannan kuma a yanzu da sanadin fari wanda sauyin yanayi da ɗumamar yanyi ke haddasawa.

Bayan sauyin gwamnati a Brazil a 2023, yawan ɓarnata dajin na Amazon ya ragu nan da nan, da rabi (abin da duniya ta ji daɗi a kai), kodayake ban da yankunan dajin da ke cikin wasu ƙasashe.

To amma kuma nan da nan sai aka gano cewa wasu sassan dajin sun yi illar da ba za su taɓa dawowa kamar baya ba.

Wannan kuwa ta kasance ne ba don ɓarnata dajin da aka daɗe ana yi ba, har da matsalar sauyin yanayi, wadda ta zama wata sabuwar barazana ga dajin da halittu da albarkatun da ke cikinsa.

Hoton wata mace tsaye a wani sashe na kogi da ya ƙafe

Asalin hoton, Reuters/Amanda Perobelli

Bayanan hoto, Fari ya daɗe yana shafar kogunan da ke cikin dajin na Amazon kamar wannan na Tapajos

Karin yanayin zafi da fari na dogon lokaci sun yi mummunar illa ga yanayin raɓa da sanyi da aka san dajin mai dausayi, da shi, inda yanzu ya zama busasshe ƙayau, da ke da haɗarin gobarar daji.

Misali a watan Satumba na 2024 an samu wurare har 41,463 da wutar daji ta fara tashi a dajin.

'Kogi mai shawagi' ya gamu da matsala

Dajin yana da wani irin yanayi na ruwan sama mai ban mamaki, da har ta kai ake yi wa yanayin laƙabi da ruwan sama mai tashi ko shawagi.

Raɓar da take tashi daga Tekun Atalantika tana haddasa ruwan sama a yankin gabashin dajin kusa da Tekun na Atalantika, kuma daga nan ruwan yake sake tashi ya zuba a wasu sassan dajin.

Wannan yanayin na ruwan sama na nuni da irin girman katafaren dajin na Amazon.

To amma sakamakon halin da dajin ya shiga a yanzu yanayin da yake haddasa wannan nau'in ruwan sama ya gamu da cikas, an gurgunta shi.

Hoton yanayin sama na dajin Amazon a yankin jihar Para ta Brazil

Asalin hoton, AFP via Getty Images/NELSON ALMEIDA

Bayanan hoto, Raɓa a sama wadda ta yi kama da ruwan kogi a sama
Ruwan kogunan cikin dajin na Amazon ya ragu a shekarun nan

Asalin hoton, AFP via Getty Images/Pedro Pardo

Bayanan hoto, Ruwan kogunan cikin dajin na Amazon ya ragu a shekarun nan

An kai maƙura ne?

Dajin mai dausayi a baya ya kasance mai jure wa gobarar daji - ba ta iya tashi ko yi masa illa saboda yanayinsa na raɓa, to amma a yankunansa da ba a samun ruwan sama sosai a yanzu, wannan garkuwa ta gobarar daji ta yi rauni.

Wasu masana kimiyya na fargabar cewa wataƙila an kai kusan maƙura wajen illa ga dajin, inda zai yi wuya ya iya farfaɗowa daga illar da aka riga aka yi masa, kuma za a rasa shi har abada.

Hoton wasu shanu na kiwo a dajin.

Asalin hoton, The Washington Post via Getty Images/Rafael Vilela

Bayanan hoto, Ayyukan noma , da kiwo da sare itatuwa domin yin katako da kuma haƙar ma'adani sun yi illa sosai ga dajin

Kogunan dajin na cikin matsala

Ƙarancin ruwan da yake zagayawa a saman dajin na Amazon, ba matala ce da ta shafi kyawu da lafiyar dajin ba kaɗai matsala ce da take illa ga dajin da kogunan da ke cikinsa, in ji ƙwararru.

An ga raguwar ruwan kogunan cikin dajin a shekarun nan inda a 2023 aka yi fari mafi muni a dajin a shekara 45.

Hoton wasu mutane a kwale-kwale a cikin ruwa

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images/Rafael Guadeluppe

Bayanan hoto, Akwai miliyoyin mutane da ke zaune a yankin na Amazon

Illar haƙar ma'adanai

Ba sare daji kaɗai ba da kuma matsalar sauyin yanayi, haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba ita ma ta taimaka wajen yi wa wannan katafaren daji mai dausayi illa.

Kuma yanzu haka an fara haƙar ma'adanai na musamman a dajin - ma'adanan da ake amfani da su wajen yin motoci masu amfani da lantarki, da wayoyin salula da tauraron ɗan'adam, da na'urar samar da lantarki daga iska.

Kuma yanzu ma aka fara haƙar waɗannan ma'adanai, waɗanda duniya ta karkata a kansu yanzu a fannin tattalin arziƙi.

Duk da cewa aikin haƙar ma'adanai shi kansa ba wai yana yi wa daji illa ba ne sosai, to amma yana gurɓata ruwa, da ƙasa da bishiyoyi da sinadarai irin su makyuri (mercury), waɗanda ke zama guba ga dabbobi da mutane.

Hoton wajen aikin haƙar ma'adanai na zinare ba bisa ƙa'ida ba.

Asalin hoton, Reuters/Ueslei Marcelino

Bayanan hoto, Illar haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba, ba ta tsaya ga dajin ba hatta mutanen yankin ta shafe su

Kasancewar dajin ya shiga ƙasashe takwas, kuma kowace ƙasa da irin dokokinta da yadda take aiwatar da dokokin, wannan ya ƙara irin girman ƙalubalen da ke tattare da yaƙi da matsalar aikata miyagun laifuka na tsakanin ƙasashe.

Wata babbar barazana ga dajin kuma, ita ce gano ɗimbin albarkatun makamashi mai gurɓata muhalli da aka yi a dajin, inda aikin haƙar zai ƙara illa ga dajin.

Tun ma kafin gano waɗannan albarkatun, bincke ya nuna cewa nau'ukan dabbobi da tsirrai 10,000 na fuskantar haɗarin ɓacewa gaba ɗaya a sanadiyyar illar da ake yi wa dajin.

Amfaninsa ya wuce yankin kaɗai

Hoton zane

Duk da yanayin da yake ciki dajin na Amazon har yanzu wata kafa ce da za ta iya zuƙe tarin hayaƙi mai gurɓata yanayi da duniya ke fitarwa.

Saboda haka rasa dajin na Amazon zai zama kamar rashin nasara a yaƙi da matsalar ɗumamar yanayi.

Yadda aka sare wasu bishiyoyi domin noman waken soya a wani yanki na Amazon

Asalin hoton, REUTERS/Amanda Perobelli

Bayanan hoto, Yadda aka sare wasu bishiyoyi domin noman waken soya a wani yanki na Amazon

Surƙuƙin daji mai dausayi yana kuma samar da kariya da ke zama tamkar wata garkuwa da ke mayar da hasken rana da ke zuwa duniya ya koma samaniya, kuma yana sanyaya duniya.

Idan dai har wannan ya ci gaba, to zai rage zafin da duniya ke yi.

''Wanna shi ne ma ya sa muke kiran Amazon, katafariyar na'urar sanyaya wannan duniya mai ɗumi,'' in ji Tasso Azevedo, masanin kimiyyar daji na Brazil.

Masana kimiyya sun ce ɗimbin ruwan daɗin da dajin yake bai wa Tekun Atalantika, na taimaka wa igiyar ruwa, kuma idan aka samu matsala ta samar da wannan ruwa, za ta iya shafar ƙarfin ruwan teku da da kuma yanayi na yankin da ma duniya.