Littattafan Hausa 10 mafi shahara a 2023

Asalin hoton, Amira Souley Maraɗi
- Marubuci, Daga Amira Souley Maraɗi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gwarzuwar Gasar Hikayata ta 2022
Bahaushe kan ce har yanzu ruwa na maganin dauɗa!
Ɗumbin marubuta ne a ƙasar Hausa ke ci gaba ƙoƙarin wallafa littattafai a fannoni daban-daban na rayuwa cikin wannan zamani.
Ana kuma samun zaƙaƙurai a cikinsu da ke ƙara tsunduma waɗansu sabbin fagage, waɗanda a baya ba cika shiga ba.
Shekara ta 2023 ma, ba ta kasance daban ba ga marubuta littattafan Hausa, duk da ɗumbin ƙalubalen da harkar karance-karance take fuskanta a tsakanin al'umma.
Domin jin fitattun littattafan da aka fi jin amonsu a sassan ƙasar Hausa cikin shekara ta 2023, fitacciyar marubuciya kuma gwarzuwar gasar Hikayata ta 2022, Amira Souley Maraɗi ta yi nazari, ga kuma litattafan da ta tsamo muku:
1. Ciwon Rai - Abdullahi Hassan Yarima

Asalin hoton, Abdullahi Hassan Yarima
Ciwon Rai, labari ne a kan wata mata wadda mijinta ya haɗu da wata larura da ta canza rayuwarsa gabaɗaya, ta yadda kowa ya kasa gane kansa.
A matsayinta na 'yar jarida ta sha baƙar wahala kafin ta iya fahimtar abin da ke damun sa, wanda har zargi iri-iri ya dinga shiga ranta bisa ingizawar zuciya.
Sai bayan wani hatsari da mijin ya sake gamuwa shi ne, wanda ya zo masa da wata matsalar ta cutar mantuwa, aka iya gano ainihin abin da ke addabar sa.
Saɓanin a baya da matar take tunanin 'yan ƙungiyar matsafa masu shan jini ne suke bibiyarsa, ko kuma asiri aka yi masa ko kuwa ya haɗu da sharrin mace ne.
Marubucin ya baje-kolin basira sosai wajen shigo da bayanai a kan matsaloli daban-daban na ƙwaƙwalwa.
Ya iya jan zaren alƙalaminsa da kyau ta yadda duk wanda ya fara karanta littafin, bai isa ya ajiye shi ba, sai ya kai ƙarshe. Ba zai yiwu a iya hasashen komai da zai faru a gaba ba, idan ana karanta littafin Ciwon Rai.
2. Baƙa ce - Sajida Saidu Kulley Nijar

Asalin hoton, Sajida Saidu Kulley Nijar
Littafin Baƙa Ce, yana ƙunshe da labarin wata buzuwa 'yar ƙasar Nijar daga ƙauyen Timiya, wadda ta kasance ita kaɗai ce baƙa a cikin danginta.
Hakan dai ya haifar mata da ƙalubale mai yawan gaske ciki har da tsangwamar mahaifi wanda ya zamo azzalumin uba.
Domin yana zaune da mahaifiyarta ne ta hanyar asiri ba tare da ko aure ba, a haka aka haife ta ita da sauran 'yan'uwanta... Labarin na ɗauke da yare uku, Hausa, Buzanci da Tubanci.
Haƙiƙa labarin Baƙa Ce ya zo da abubuwa masu yawa na al'adun ƙasar Nijar; irin ƙalubalen da take ciki, ci gabanta da tarin darajar da aka fitar ta duk wani ɗan'adam.
3. 'Ya'yanmu - Kabir Yusuf Fagge (Anka)

Asalin hoton, Kabiru Yusuf Fagge
'Ya'yanmu labari ne a kan rayuwar haifi-ka-yasar, wato yadda iyaye suke haifar 'ya'ya amma su daina kula da duk wasu al'amuransu.
Babi huɗu ne.
Babi na farko a kan yara su Ɗan'amadu da iyayensu suke banzatar da rayuwarsu, yaran su zama 'yandaba zuwa 'yan kidinafin.
Babi na biyu labarin Harira ne, yadda ta haɗa neman ilimi da talla tare da manyan ƙalubalen da take fuskanta, alhalin tana son ilimin.
Babi na uku kuwa labarin Laure ne da Sadi, waɗanda mahaifinsu yake guduwa ya bar su wai saboda talauci, su shiga gararin rayuwa
Babi na huɗu na ƙarshe kuma labarin Ihsan ne da yadda ta rayu a gidan marayu babu kulawa.
4. Harin Gajimare - Hauwa Shehu

Asalin hoton, Hauwa Shehu
Labari ne a kan iftila'in kutsen intanet, irin wanda ake garkuwa ko shaƙe shafin intanet na (Ransomware attack).
Lamarin dai ya auka wa wani mashahurin kamfani, wanda har aka yi garkuwa da kundin bayanansu mai matuƙar muhimmanci a daidai lokacin da suke tsananin buƙatarsa.
Hakan ta sa maharan ko masu garkuwar intanet ɗin suka nemi a biya su kuɗin fansa, kafin su saki kundin kamfanin.
A ƙoƙarin ƙwato 'yancin kundin ne kuma, jarumin labarin shi ma aka yi garkuwa da shi a zahiri, saboda tsabar sakacin shugaban (MD) kamfanin, wanda ya zamo silar da maharan giza-gizan intanet ɗin (cyber criminals) suka ƙaddamar da mummunan harin.
5. Ɗaya a Cikin Dubu - Amira Souley Maraɗi, Hassana Ɗanlarabawa da Maryam Muhammad Sani
Ɗaya A Cikin Dubu, littafi ne wanda ya amsa sunansa, ya haɗa labarai guda uku masu ɗauke da mabambantan jigogi na matsalolin da suka yi wa al'umma da'ira.
Na farko: halin ƙaƙa-ni-ka-yi da masu larurori da kan haifar da tawaya ke shiga, da irin kallon da mutane na nesa da kusa ke yi masu.
Na biyu: Ɗacin maraici da ƙalubalen da zawarawa kan fuskanta a tsakanin al'umma, na munana zato da kyara da gori, kamar su ne suka zaɓar wa kansu rayuwar da suke ciki.
Sai na uku: kwaɗayi da buri waɗanda a dalilinsu ne ake cizon yatsa sanadin cinikin biri a sama.
A ƙarshe dai bayan faɗawa ramuka da haura tsaunuka, taurarin labarin rayuwarsu ta inganta dalilin wata uwa wadda ta zamo Ɗaya A Cikin Dubu gare su, wato BBC Hausa.
Wannan labari gamayyar Gwarazan Hikayata ta 2022 ne suka rubuta shi.
6. Haƙƙin Uwa - Amrah Auwal Mashi

Asalin hoton, Amrah Auwal Mashi
Labari ne a kan wata baiwar Allah Safiyya, wadda ta ɗauki duniya da zafi.
Tun tana 'yar yarinya take gudun a san tushenta, har ta girma da wannan ƙuduri, ta wulaƙanta mahaifiyarta a daidai lokacin da ta fi buƙatarta fiye da kowa, ta gudu ta auri wani.
Sai dai, a rashin saninta ashe ba mutumin ƙwarai ta aura ba.
Ta sha gwagwarmaya sosai kafin ta samu kuɓuta daga hannunsa, bayan iyayensa sun mayar da ita tamkar baiwa.
A lokacin da ta waiwayi mahaifiyar tata da niyyar miƙa dukkan tubanta gare ta, sai ta tarar Allah ya karɓi rayuwarta sanadin cutar sankarar jini da ta kamu da ita tun da ƙuruciya.
Sai dai akwai saƙon da ta bari ta hannun ɗiyar riƙonta, da fatan ta isar da shi ga Safiyya komai daren daɗewa, idan ta waiwayi gida.
7. Dukan Ruwa - Rufaidah Umar Ibrahim

Asalin hoton, Rufaidah Umar Ibrahim
Labari ne a kan wata marainiya ɗaya tilo wadda aka haifa a Jamhuriyar Nijar, mahaifiyarta ta rasu a dalilin wani ɓoyayyen al'amari da ya auku ranar da ta faɗo duniya.
Hakan ya sa ta zauna tsawon wani lokaci a hannun ɗan'uwan mahaifiyarta, daga baya ta koma Najeriya, inda tushe da kuma salsalar komai na rayuwarta yake, hannun Mahaifinta.
Komawar da ta haifar da abubuwa da dama a rayuwarta, ciki kuwa har da tonuwar wasu manyan asirai da suka jima da binnuwa a doron ƙasa.
An dai yi walƙiyar da ta haska wa Humaira ainihin fuskar mutanen da take yi wa kallon bango, kuma majinginarta a rayuwa.
8. Sakacin Waye? - Sumayya Abdulƙadir Takori
Wannan littafi ne mai ƙunshe da labari a kan wata yarinya da rayuwar mafarki ta tasirantu a cikin ƙwaƙwalwarta, har ta himmantu wajen ganin rayuwar tana samuwa a zahiri.
Sakamakon wannan ƙuduri nata na son ganin mafarkinta ya zama gaskiya ne, ta haɗu da ƙalubale daban-daban, waɗanda suka kai har iyayenta sun kore ta daga gidansu.
A ƙarshe muradin nata ya bayyana zahiri lokacin da ta yanke tsammani kuma wuri ya ƙure mata, sai ya bayyana matsayin haramtacce gare ta yadda ba za ta iya samunsa ba.
A dalilin haka ne ta gane ba kowane mafarki ne kan iya zama gaskiya ba.
9. Dambarwar Siyasa - Gasar Aminiya Trust ta kamfanin Media Trust

Asalin hoton, Media Trust
Littafi ne na zube da ya shahara saboda an nazarce shi kuma ana kan nazarinsa a makarantu da sauran fagage daban-daban, kuma ya cika kusan duk wani sharaɗi na cikar ingantaccen littafi.
Ya yi tashe a shekarar da ta wuce a fagen nazari da kuma shiga hannun mutane, shi ne littafin gasar da Aminiya Trust ta samar.
Duka labaran da ke cikin littafin suna magana ne a kan siyasa da abin da ta ƙunsa.
10. Muhalli, Sutura - Gasar Arc Ahmed Musa Ɗangiwa
Littafin Muhalli, Sutura ya ƙara samun ɗaukaka ne bayan shigar da ya samu a cikin jihar Katsina, inda dukkan makarantun sakandiren jihar suka yi amfani da shi a shekarar 2023.
Kuma shi ne littafin da tsawon shekara uku kenan a jere, ana nazarinsa a Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Katsina.
Ɗaukaka da kuma ankararwar da littafin ya yi sun ba da gudunmawa wajen shirya wani taron bita a farkon wannan shekara, inda ake sa ran gayyatar masana a kan matsalolin muhalli da hanyoyin da za a bi wajen magance su.
A 2023 kaɗai, an buga kwafin littafin 5,000 kuma aka raba shi ga hukumomi da makarantu a faɗin Najeriya baki ɗaya.











