Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Asali da muhimmancin ranar mata ta duniya
Ƙila kun taɓa ganin inda aka ambaci ranar mata ta duniya a kafafen yaɗa labarai ko kuma a bakin abokai.
Amma yaushe ne wannan rana? Me take nufi? Akwai irin wannan rana da aka ware wa maza a matsayin ranar su? Kuma me ya sa ranar ke da muhimmanci?
Fiye da ƙarni ɗaya ke nan mutane a sassan duniya ke bikin ranar mata a duk ranar 8 ga watan Maris.
Karanta domin sanin dalili.
Mene ne asalin ranar?
Ranar mata ta duniya da ake yi wa laƙabi da IWD ta samo asali ne daga gwagwarmayar ƙungiyoyin ƙwadago har ta kai Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da rana ɗaya a kowacce shekara domin tunawa da ranar.
An yi dashen icen da ya samar da ranar ne a 1908, lokacin da wasu mata 15,000 suka yi gangami a birnin New York suna neman a rage yawan lokacin aikin su, da ƙarin albashi da kuma ƴancin kaɗa ƙuri'a. Shekara ɗaya bayan haka ne kuma jam'iyyar Socialist ta ƙaddamar da ranar mata ta farko a duniya.
Wata mata mai suna Clara Zetkin, mai aƙidar kwamunansanci kuma mai rajin kare ƴancin mata ce ta kawo shawarar samar da ranar. Ta bayar da shawarar ne a 1910, a wajen taron ma'aikata mata na duniya a birnin Copenhagen. Mata 100 ne daga ƙasashe 17 suka halarci taron, suka kuma amince da shawararta baki ɗayan su.
A 1911 aka fara bikin ranar a Austria da Denmark da Jamus da kuma Switzerland. Kuma a 2011 aka cika shekara 100 da fara bikin ranar.
Ranar ta samu karɓuwa a hukumance ne a 1975 lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga bikin a karon farko. A 1996 kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da taken ranar wato ''Murnar abin da ya faru baya da kuma tsara abin da zai faru nan gaba''
Ranar mata ta duniya ta zamo rana ta bikin nasarorin da mata suka samu a cikin al'umma, a fannin siyasa da tattalin arziki, yayin da siyasar da ke cikin bikin ranar ke nufin amfani da yajin aiki da kuma zanga-zanga wajen wayar da kai a game da ci gaba da samun rashin daidaito musamman ga yadda ake tafiyar da harkokin mata.
Me ya sa aka tsayar da ranar 8 ga watan Maris?
Lokacin da Clara ta ƙirƙiri ranar mata ta duniya ba ta tsayar da wata rana ta musamman domin bikin ba.
Ba a amince da ranar a hukumance ba sai a yajin aikin 1917 lokacin da wata 'yar Rasha ta buƙaci abin da ta kira ''Burodi da zaman lafiya'' kuma kwana 4 da fara yajin aikin ne aka tilasta wa gwamnati bai wa mata ƴancin yin zaɓe.
Ranar da aka fara wannan yajin aiki a kwanan watan Julian, wanda Rasha ke amfani da shi a wancan lokaci ya faɗo a ranar 23 ga watan Fabarairu. Wannan rana ce kuma ta zo daidai da 8 ga watan Maris a kwanan watan miladiyya.
Me ya sa ake sanya kaya launin shanshanbale a ranar?
Launin shanshanbale da kore da kuma fari duk suna da alaƙa da ranar mata ta duniya kamar yadda shafin intanet na ranar ya bayyana.
"Shanshanbale na nuni da adalci da mutunci. Kore na nuni da fata. Fari kuma na nuni da tsarkaka. Waɗannan launuka sun samo asali ne daga ƙungiyar siyasa ta matan Birtaniya a 1980," inji shafin.
Akwai ranar maza ta duniya?
Akwai ranar maza ta duniya da ake bikin ta a ranar 19 ga watan Nuwamba.
Sai dai a shekarun 1990 ne aka fara bikin ranar kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta amince da ranar ba. Ana bikin ranar a ƙasashe fiye da 80, ciki har da Birtaniya.
Ranar ta mayar da hankali ne ga bikin "Gudunmuwar da maza ke bayarwa a duniya, da iyalinsu da kuma cikin al'ummarsu", masu tsara gangamin ranar sun ce manufarta ita ce bayyana gudunmmawar maza wajen kawo ci gaba, da zaman su abin koyi da kula da walwalar su da kuma inganta alaƙa tsakanin jinsi.
Ya ake bikin ranar mata ta duniya?
Ana bayar da hutu a ƙasashe da yawa domin bikin ranar mata ta duniya, ciki har da Rasha inda ake sayar da furanni a cikin kwana uku ko huɗu da ake bikin daga ranar 8 ga watan Maris.
A ƙasar China, ana bai wa mata damar tashi aiki da wuri a ranar 8 ga watan Maris a bisa shawarar majalisar ƙasar.
A Italiya ma, ana bikin ranar mata ta duniya da aka fi sani da la Festa della Donna ne ta hanyar rarraba wasu furanni masu ƙayatarwa. Babu dai cikakken bayani kan tarihin wannan al'ada amma ana ganin cewa ta samo asali ne daga Rome, bayan yaƙin duniya na biyu.
A Amurka kuwa, watan Maris wata ne na tarihin mata. Fadar shugaban ƙasar ta sanar da cewa a kowacce shekara ana karrama matan da suka yi zarra a fannoni daban-daban a Amurkan.
Menene taken ranar mata ta 2024?
Taken da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bai wa ranar mata ta 2024 shi ne ''tallafa wa mata domin haɓɓaka ci gaba''
Taken yana nuni ne da ƙarancin fitar da kuɗi wajen tallafa wa mata da daidaiton jinsi.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce "Rikici da hauhawar farashi za su iya tilastawa kashi 75 cikin 100 na ƙasashe rage kuɗin da suke kashewa nan da 2025, lamarin da zai shafi mata da ayyukansu."
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana buƙatar ƙarin dala biliyan 360 kowacce shekara idan har ana son cimma daidaiton jinsi nan da 2030. Kashi 5 cikin 100 ne kacal gwamnati ke warewa domin magance matsalar cin zarafin mata a duniya, kuma ana kashe ƙasa da kashi ɗaya ne domin yin rigakafin faruwar cin zarafin mata, kamar yadda rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana.
Amma akwai wasu ƙarin take da shafin intanet na ranar mata ta duniya ya wallafa da suka haɗa da ''Inganta tafiya tare'' inda aka yi tsare-tsaren ''Magance abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaban mata, da kuma tabbatar da ganin ana mutunta mata da mutunta su''
Me ya sa muke buƙatar wannan rana?
A shekarun baya, mata a ƙasashe da dama kamar Afghanistan da Iran da Ukaraine da kuma Amurka suna fafutukar neman ƴancinsu a cikin yanayin yaƙi da tashin hankali da kuma sauye-sauyen tsarin gudanarwa.
Mata a Gabas ta tsakiya na fuskantar mummunan tashin hankali a yaƙin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa. Ƙwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce sun tattara bayanan zargin cin zarafin mata a Gaza, ciki har da fyaɗe da ake zargin dakarun Isra'ila da aikatawa. Haka nan kuma, BBC ta samu wasu bayanai da ke bayyana aikata fyade da cin zarafin mata a harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba.
Tashin hankalin yana kuma jefa mata cikin yanayin tsananin buƙatar agaji. Nan da wata mai zuwa, mata aƙalla 5,500 ake sa ran za su haihu a Gaza, kuma hukumar kula da yawan jama'a ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wannan zai faru ne cikin yanayi na ƙarancin ayyukan kiwon lafiya.
A Afghanistan, ƙungiyar Taliban ta haramta wa ƴanmatan da suka kammala makarantun sakandare ci gaba da karatu, lamarin da ke daƙile ƴancinsu na neman ilimi.
Rikicin da ake yi tsakanin rundunar sojin Sudan da mayaƙan RSF ya ƙara munana yanayin da mata ke ciki. Akwai rahotannin garkuwa da mata da kuma yi masu fyaɗe a yankin da mayaƙan RSF ke da iko, inda ake tilasta masu auren mayaƙan da kuma karɓar kuɗin fansa. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fiye da mutane miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu ne suka gudu daga ƙasar zuwa ƙasashe maƙwabta, kuma 9 daga cikin kowanne mutum 10 da suka yi hijirar mata ne da ƙananan yara.
A watan Satumban bara aka cika shekara ɗaya da mutuwar Mahsa Amini, ƴar shekara 22, wadda jami'an hisba suka kama a bisa zargin ta karya dokar sanya mayafi ta Iran. Ana ƙara samun mata masu karya dokar, yayin da masu fafutuka irin su Narges Mohammadi, wadda ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ke fuskantar zaman yari na tsawon lokaci.
Amma an samu sauƙin lamarin a shekarar da ta gabata.
A watan Oktoban 2023 majalisar Argentina ta amince da dokar Olimpia wadda ke neman hana cin zarafin mata a kafafen intanet da kuma hukunta masu aikata hakan. Ƙungiyar Amnesty International ta ce ɗaya daga cikin matan Argentina uku suna fuskantar cin zarafi a Intanet.
Taiwan ta yi fama da yaɗuwar cin zarafin mata ta hanyar lalata, wanda gangamin 'MeToo' da aka yaɗa a wani shirin Netflix ya tunzura. Wannan ya sa gwamnati ta tsaurara yaƙi da cin zarafi, ta yadda aka buƙaci wuraren aiki su kafa hanyoyin kai rahoton cin zarafin mata. Dokar ta kuma tilasta wa kamfanoni yin bincike da kuma gabatar wa hukumomi rahoton binciken da suka yi kan cin zarafi.
Ƙungiyoyin kare ƴancin mata sun yi maraba da matakin sassauci kan zubar da ciki da aka ɗauka a watan Satumban bara a Mexico. Ƙasar ta bi sahun ƙasashen kudancin Amurka da suka sassauta dokar hana zubar da ciki.
A baya bayan nan ma majalisar dattawan Faransa ta kaɗa ƙuri'ar sanya ƴancin zubar da ciki ga mata, a cikin kundin mulkin ƙasar.
Mutane aƙalla miliyan biyu suka halarci gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya da aka yi a ƙasashen Australiya da New Zealand a watan Yuli zuwa Agusta, lamarin da ke nuni da Ƙari sosai a kan tarihin ƴan kallo dubu ɗari shida da ake da shi a baya. Hakan na nuna yadda ake ƙara samun masu ƙaunar wasanni mata, kuma wasu mutane miliyan arba'in da shida da dubu ɗari bakwai ne suka kalli wasannin motsa jiki na mata da aka yaɗa a talabijin a Birtaniya a 2023, kamar yadda wani bincike kan wasannin mata ya tabbatar.
Yanayin da ya kamata ya zamo na murna da farin cikin lashe gasar ƙwallon ƙafa ta duniya ga tawagar Sifaniya ta mata ya zamo wani lamarin na daban, inda aka koma tattauna yadda tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar, Luis Rubiales ya sumbaci Jenni Hermoso. Hermoso ta ce ya yi hakan ne ba tare da izinin ta ba, ta kuma shigar da ƙorafi a kan Rubiales, wanda ya yi murabus ya kuma musanta aikata ba daidai ba.
Lamarin ya buɗe sabon babin tattaunawa kan ɗabi'ar rashin mutunta jinsi a ciki da wajen duniyar ƙwallon ƙafan mata.