Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Abin da ya fi ci min rai bayan na kamu da HIV shi ne rashin aure’
- Marubuci, Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC Pidgin
Talatu (wadda ba sunanta na ainihi ke nan ba) tana zaune ne arewacin Najeriya, tana rayuwa da cuta mai karya garkuwar jikin ɗan adam, wadda ake kira da HIV.
Cutar HIV na buƙatar kulawa wanda kuma gaza samun kulawar kan kai ta mataki na gaba na AIDS.
‘Yar shekara 35 ɗin ta bayyana wasu abubuwa uku da tace suna ci mata tuwo kwarya, ciki har da rashin samun haihuwa.
Matar wadda ta kwashe shekara 19 ɗauke da cutar ta ce daga ita sai mahaifiyarta da wasu mutane ƙalilan ne suka san tana ɗauke da cutar, saboda gudun tsangwama.