AC Milan da Inter na rububin Arda Guler, Bayern da Madrid na zawarcin Dalot

Lokacin karatu: Minti 1

Matashin ɗan wasan Turkiyya Arda Guler na son barin Real Madrid yayin da yake ci gaba da fama da rashin samun gurbi a tawagar farko, inda rahotanni suka ce AC Milan da Inter na zawarcin ɗan wasan mai shekara 20. (Sport)

Bayern Munich da Real Madrid na son ɗaukar ɗan wasan bayan Manchester United da Portugal Diogo Dalot, mai shekara 25 a bazara. (Teamtalk)

Liverpool na nazarin ɗaukar ɗan wasan bayan Borussia Dortmund ɗan ƙasar Jamus Nico Schlotterbeck, mai shekara 25, wanda suke ganin zai iya maye gurbin Virgil van Dijk na tsawon lokaci. (Bild)

Liverpool da Manchester City da Arsenal ne ke kan gaba a jerin ƙungiyoyin da ke jan hankalin ɗan wasan Sweden Viktor Gyokeres, idan har ɗan wasan mai shekara 26 ya bar Sporting a bazara. (A Bola)

Arsenal ta shige gaban Barcelona a rububin sayen golan Espanyol mai shekara 23 Joan Garcia. (Cadena Ser)

Manchester United za ta iya neman Dusan Vlahovic yayin da Juventus ke shirin rage farashin fam miliyan 35 da ta ƙaƙabawa ɗan wasan na Serbia mai shekara 25. (Givemesport)

Tottenham ta fara tattaunawa da Angel Gomes kan cinikin kyauta idan kwantiragin ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 24 ya ƙare a Lille a ƙarshen kakar wasan bana. (Football Transfers)

Liverpool ta fara sanya ido kan ɗan wasan Bournemouth ɗan ƙasar Hungary Milos Kerkez, mai shekara 21. (Teamtalk)

Leeds ta amince ta sake sayen ɗan wasan tsakiyar Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 29, daga Manchester City, muddin ƙungiyar ta samu ɗaukaka zuwa gasar Premier a kakar wasa mai zuwa. (Teamtalk)

Newcastle na shirin zawarcin dan wasan gaban Ipswich Town Liam Delap, mai shekara 22, yayin da ɗan ƙasar Ingilan ke son ci gaba da zama a gasar Premier. (Football Insider)

Manchester United ce ke kan gaba a jerin ƙungiyoyi da ke zawarcin ɗan wasan bayan Rosario mai shekaru 18 ɗan ƙasar Argentina Juan Gimenez. (Football Insider)