Yadda za ku raba yaranku da zama masu ɗari-ɗari a cikin mutane

..

Asalin hoton, Getty Images

Kunya wata dabi'a ce da ke da alaƙa da halin da ke cikin al'ummarmu ta yanzu kuma tana shafar mutane da yawa a duniya.

A makarantu, akwai yara da dama waɗanda ke jin kunyar amsa tambayoyin malamai a aji ko da sun san amsar gudun kada a yi musu dariya, ko tsoron kada su faɗa ba daidai ba, wasu kuma ba sa hulɗa da sauran yara duk saboda kunya.

Duk da haka, ba a mayar da hankali kan irin wannan matsalar ta jin kunya kamar yadda ake mayar da hankali kan sauran matsaloli.

Ana ganin kamar kunyar ba matsala ba ce wadda za ta iya haddasa rashin ci gaban yaro a aji.

Don ƙarin fahimtar irin wannan kunyar, yana da kyau a fahimci cewa kunya kala biyu ce, akwai kunya ta ƙaramin lokaci sai kuma kunya ta dindindin.

Kunya ta karamin lokaci kunya ce da mutum ba ya dadewa yake saurin sabawa da abubuwa, nan da na ta wuce.

Kunya ta dindindin kuma kunya ce wadda ke iya haifar da rashin jin daɗi akai-akai a cikin al'amuran yau da kullum kuma za ta iya kawo cikas ga ci gaban mutum.

Wato idan aka ce mutum na da kunya, hakan na iya tasiri da yanayin tunanin sa da dangantakar sa da zamantakewar sa da ci gaban sa da kuma makomarsa.

Kunya na iya yin tasiri babba ga rayuwar mutane.

..

Asalin hoton, Getty Images

Shin akan haifi mutum da dari-dari ne?

Don taimaka wa mutane masu jin kunya da fargaba, da haɓaka ci gabansu gaba ɗaya, da haɓaka ingancin rayuwarsu, ta hanya mafi kyawu, yana da mahimmanci a fahimci abubuwan da ke faruwa a cikin tunanin su da cikin zuciyar.

Tambayar ita ce: shin jin kunya ko fargaba dabi'a ce ta asali da aka haifi mai kunyar da ita ko kuma daga baya fargaban ke zuwa sakamakon abubuwan da mutum ke fuskanta?

Wannan tambaya ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin masu bincike, wanda ya haifar da mahanga iri-iri.

Wasu daga cikinsu sun danganta jin kunya da fargaba a matsayin wani abu da mutum ke gada daga danginsa, yayin da wasu kuma ke nuna tasirin muhalli ga jin kunya ko fargabar mutum.

Za a iya magance matsalar fargaba ko kunya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma mene ne abubuwan da ya kamata a yi don taimakawa wajen raba yara har da manya da kunya ko fargaba?

Malamai da iyalai za su taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ɗaiɗaikun yara da ke fama da kunya ko fargaba, saboda su ne ke da alhakin ba su tarbiyya, da dabarun da suka dace don fuskantar irin wannan ɗabi'a.

Ga wasu zaɓaɓɓun abubuwan da za a iya yi waɗanda za su iya taimakawa wajen raba yara ko manya da fargaba kuma su iya fuskantar wannan ɗabi'a:

1. Ƙarfafa hulɗa da mu'amalar yaro: Yana da mahimmanci ga yara masu jin kunya su yi hulɗa da sauran yara tun suna ƙanana, abubuwa kamar wasanni na yara na iya taimakawa a wannan batun, wasu iyaye da sunan ba da tarbiyya suna hana yaransu wasa ko hulɗa da sauran yara, hakan na haifar da kunya da fargaba ko a aji ko idan sun fita da yaran.

2. Ƙarfafa ƙima da girmama kai: Mutumin da ba ya ganin kansa da ƙima ko girmama kansa ko kuma ba ya nuna ma kansa so, dole ne ya dinga samun fargaba wajen mu'ammala da sauran mutane, saboda haka yana da kyau tun a gida, tun mutum na ƙarami, a dinga koya masa muhimmancin kansa da girmama kansa, da yadda zai dinga ganin kansa da ƙima, da kuma kada ya dinga ƙasƙanta kansa idan yana wani waje ko tare da abokai.

3. Koya wa yaro kula da yanayin tunaninsa, da fahimtar yadda yake ji a jikinsa da zuciyarsa na ɗaya daga cikin hanyoyin da za a bi wajen raba yaro da fargaba, fahimtar yanayin tunani da yadda mutum ke ji zai sa ya koyi fahimtar sauran mutane wanda hakan zai sa ya san irin hulɗar da zai yi da mutum.

4. A guji yi ma yaro lakabi: Yawancin lokaci, akwai al'adar yi wa mutum lakabi da cewa "ai kunya ne da shi, ba lalle ya iya amsa tambaya ba ko ya iya magana cikin mutane", irin waɗannan kalamai na iya sa yaro ya zama yadda ake masa laƙabi, wanda hakan zai iya shafar halayensa da imaninsa da tunaninsa har ya dinga fargabar magana, ko amsa tambaya ko hulɗa da sauran mutane, saboda haka yana da kyau iyaye da malamai su kiyaye yi wa yaro laƙabi da abu mara kyau.

5. Samar da yanayin rikon amana na iya taimaka wa masu jin kunya su shiga cikin aji ko taro ko yanayi iri-iri.

Wasu daga cikin abubuwan da ke tattare da kunya sun hada da tsoron yin magana a cikin jama'a ko kuma tsoron yin wauta shi ya sa suke guje wa kowane irin mu'amalar zamantakewa. Don haka, dole ne malamai su taimaka ta hanyar ba su damar yin yin magana a aji, amsa tambaya, da nuna masu su ma suna da muhimmanci, da kuma kawar da tunanin sauran yara da suka samu kan raini da sauran hali marasa kyau.

6. Bai wa yara damar fara sadarwa ko tattaunawa, da nuna musu cewa ra'ayinsu yana da muhimmanci, da nuna musu cewa ko saura mutane sun yi musu dariya ba komai.

7. Iyaye da malamai su daina nuna banbanci gaban yara, kar su nuna sun fi son daya kan dayan ko da hakan ne, su daina yaba daya ta hanyar aibanta dayan, yin haka na iya ɓata tunanin yaro da kuma haifar masa da kunya, da tsoro da kuma fargaba.

Waɗannan su ne wasu dabarun da za su iya taimaka wa masu jin kunya ko fargaba su fuskanci matsaloli daban-daban da suka saba fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum.

Saboda haka yana da kyau a fahimci wannan hali na mutum da kuma taimakawa a inda ya kamata, ba wai a yi amfani da damar hakan wajen raina mutum ba ko aibanta shi.

Masu irin wanna dab'i'ar kadai suka san girman wahalar da suke fuskanta wajen koƙarin son su yi hulɗa da mutane, wajen so su amsa tambayoyi a aji da sauran su, amma ba su iyawa saboda da kunya.

A yau ana ɗaukar jin kunya a matsayin ɓacin rai ko kaɗaici ko baƙin ciki, saboda haka ya zama wajibi a bayyana kunya a bainar al’ummarmu da kuma illar da ta ke iya haifarwa ga rayuwar mutane da nufin wayar da kan iyalai da malamai da sauran al’umma gaba daya.

Ta haka ne kawai za a iya biyan bukatunsu a gida da makarantu, da taron jama'a don inganta rayuwar masu jin kunya.