Abu biyar da za a iya sa yara su yi a lokacin hutu maimakon zaman banza

yara 'yan makaranta

Asalin hoton, AFP

Daga Sadiqa Bkeke

BBC Hausa, Abuja

A yayin da makarantun firamare da sakandari ke shiga watan hutu mai tsawo, abin da ke ci wa iyaye tuwo a ƙwarya shi ne yadda ‘ya’yansu za su amfana da wannan hutun ba tare da zama a gida ba su yin komai.

Masana sun bayyana matakan da suka kamata iyaye su dauka a irin wannan lokaci domin ganin ‘ya’yansu sun mori hutun.

Mamu Alhaji Muhammad, mai wata makarantar firamare ce da ke Abuja, kuma ya yi mana bayani a kan abubuwa masu sauki da iyaye za su iya taimaka wa yaransu ba tare da dogon nazari ba.

Daga cikin abubuwan da Mamu Alhaji ya yi nazari a kai su ne:

Manhajar koyon karatu

Akwai wani salon karantarwa ta hanyar manhajoji da ake kira ‘Adaptive Learning System’, inda iyaye za su iya sauke manhajar a wayoyinsu ko kwamfutar hannu da yin rajista. Daya daga cikin manhajojin akwai ‘Youlesson’.

YouLeason: Wata manhaja ce da iyaye za su iya saukewa a wayoyinsu ko a kwamfutar hannu ko kwamfutar tebur.

Sai su yi rajistar yaransu inda za a ba wa ko wane yaro damar koyon darasi daga wurin malami kai-tsaye ta hanyar bidiyo, yaro na kallon malami, malami na kallon yaro.

Kuma iyaye za su iya zama a gefe suna lura da darasin da yaransu ke daukawa.

Mimo: Wannan manhajar na koyar da yara dabarun sarrafa kwamfuta (Computer Coding) ta yadda za su iya kirkiran manhaja da kansu.

Da kuma yadda za su fahimci harshe da kamfuta ke ganewa.

Abubuwan da ba su shafi darussan aji ba

Yara sun dade suna zuwa makaranta, yanzu da ake hutu, akwai bukatar ba su hutu daga abubuwan da suka shafi makaranta da daukar darasi.

Akwai abubuwa da dama da iyaye za su iya yi da yaransu domin shakatawa da kuma kara shakuwa tsakanin iyaye da ‘ya’ya.

Lokacin da yara ke zuwa makarantu, wasu iyayen kuma na zuwa wuraren aiki, wannan wata dama ce da wasu iyayen za su samu domin samun lokaci mai muhimmanci da ‘ya’yansu.

Alhaji Muhammad ya bayyana mana abubuwa da zai iya kara shakuwa tsakinin iyaye da yara ko kuma tsakanin ‘yan uwa. Daga cikinsu akwai:

· Ninkaya

· Ziyartar wurin shakatawa

· Kwallon kafa

· Wasan ‘yar-ɓuya

· Langa

· Carrafke

Ga iyaye masu hazaka kuwa za su iya yin wasan dambe ko kuma wasan doki da yaran nasu.

Skip Karin wasu labaran da za ku so ku karanta and continue readingKarin wasu labaran da za ku so ku karanta

End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta

Aikin gida

Yara kanana wadanda ba su saba da aikin gida ba kan iya jin dadin taya iyayensu aiki yayin da suke cikin hutu.

Iyaye kan iya jawo hankalin ‘ya’yansu kan ayyukan gida kamar su wanke-wanke da shara da goge daɓan gida, ba su damar nuna kwazonsu wajen shirya wurin ajiye tufafinsu ko wurin ajiye takalmansu da sauran su.

Karatu don nishadi

Alhaji Muhammad ya yi mana karin haske kan yadda karatun nishadi ke iya sa yara su amfana da lokacinsu.

Ya ce akwai wata dabara da iyaye za su iya sa yaransu karatu, dabarar ita ce:

Za ku iya samun wani dan lungu cikin gida da za ku ƙayata domin ya ja hankalin yaran, sai ku ba su littafi daya ko biyu da kuma ba su awanni da kuke so su kammala karanta littatafan.

Sannan idan sun gama karatun cikin awannin da kuka ba su, sai ku musu kyauta da zai faranta musu rai.

Mutum-mutumi

Ga iyaye masu hali kuwa, akwai hanyar ilimtar da yara ta mutum-mutumi.

Inda za a samu irin wanda zai koyar da su abubuwan zamani.

Darasi a cikin gida

Kamar yadda kuka sani ko lokacin da yara ke makaranta, ana samo musu malami da zai zo gida don koyar da yara darasin boko ko na addini.

Yanzu da ake cikin hutu ma, iyayen da ke da ilimi za su iya ci gaba da yin haka a cikin gida.

Hakan ma na iya kara shakuwa tsakinin iyaye da yara da kuma koyar da yara ilimin da suke da shi.

Yin haka ma na iya taya iyaye sanin zurfin ilimin yaransu.

Wani rikonin asibitoci na Narayana Health da ke Indiya ta bayyana wasu karin abubuwan da za ku iya yi masu sauki da yara a gidajenku.

Koyon sabon harshe

Bincike ya gano cewa mutanen da ke magana da harshe fiye da daya suna da kaifin tuna abubuwa da kuma basirar magance matsaloli da kuma mayar da hankali kan abu sosai da kuma sauraro da kunnen basira.

Sanin karin harshe zai kasance abu mai amfani ga yara.

Zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa ci gabansu. Koyan sabon harshe ya kasance mai sauki a yanzu saboda yawan hanyoyi da ke bai wa mutum damar koyansa.

Manhajoji da dama suna koyar da harsuna da dama ta hanyar wasan ‘game’ ta yadda yaran za su koya harshen cikin nishadi.

Koya musu girke-girke

yara mai girki

Lokacin hutun makaranta lokoci ne da ya fi dacewa ku koya wa ‘ya’yanku girke-girke masu sauki da za su iya yi.

Hakan zai iya sa wa su kware a fannin girke-girke.

Girka abinci abu ne muhimmi da ko wani yaro ya kamata ya iya.

Za a iya soma da girka abubuwa masu sauki irin su taliya da dangoginsu sannan a koyi yin su shinkafa.

Yara na son koyan sabbin abubuwa, za su kasance cikin annushuwa su ci abincin da suka girka.