Shin akwai buƙatar tantance masu wa'azi a Kano?

Abba Kabir

Asalin hoton, Kano state Government

Lokacin karatu: Minti 5

Faruwar al'amaura masu alaƙa da addini da yadda suke tayar da tarzoma a Kano na ƙara jefa alamun tambaya dangane da ko akwai bukatar dokokin da za su sa ka idanu kan masu wa'azi a jihar Kano.

A ranar Larabar nan ne dandazon wasu mazauna birnin Kano suka gudanar da zanga-zangar lumana zuwa gidan gwamnati, inda suka kai koke dangane da zargin kalaman "rashin ladabi" ga janibin Annabi Muhammadu SAW.

Wannan dai ba shi karon farko da ake samun irin waɗannan zarge-zarge kan malamai a birnin na Kano, inda har wani lokacin ma ta kan kai ga yin muƙabala ko kuma kaiwa ga kotu.

A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Neja ta ce za ta rinƙa tantance hudubar malamai da limaman coci bisa abin da ta ce ƙoƙarinsu na furta kalaman tunzura al'umma.

Abin tambaya a nan shi ne ko Kano ma na buƙatar irin wannan doka da jihar Neja ta ce za ta yi?

Me ya faru a Kano?

Dandazon masu zanga-zanga

Asalin hoton, Kano State Government

A ranar Laraba ne wasu mazauna birnin Kanon suka yi zanga-zangar lumana game da zargin malamin addini Musulunci, Sheikh Lawan Abubakar Triumph da kausasa kalamai kan Annabi Muhammadu (SAW).

Masu zanga-zangar sun dangana da farfajiyar gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarɓe su tare da yi musu jawabi.

A baya-bayan nan ne aka ga malamin a wani bidiyo yana musanta batun cewa haihuwar Annabi da shayinsa, kamar yadda wasu litattafai suka ruwaito, ba karama ba ce saboda "ana iya haihuwar sauran mutane ma da kaciya".

A cewar malamin, karama na nufin "wani abin al'ajabi da Allah yake bai wa annabawa su kaɗai". Kazalika, malamin ya ce ruwayoyin ba su inganta ba.

..

Asalin hoton, Nigeria Police

Bayanan hoto, Sheikh Lawal Triump lokacin da rundunar ƴansandan jihar Kano ta gayyace shi bisa rakiyar wasu malamai abokansa a watan Yulin 2025.

Martanin Gwamnan Kano

..

Asalin hoton, KNSG

Gwamna Abba ya umarci masu ƙorafin da su kwantar da hankali, inda ya nemi su rubuto masa takardar koke a hukumance ta hannun ofishin sakataren gwamnati.

"In Allah ya yarda za mu ɗauki matakin da bai saɓa wa Shari'a ba," in ji gwamnan.

"Abin da nake so shi ne ku koma ku rubuto wa gwamna takarda, wadda ita ce za a yi amfani da ita daga nan har zuwa ƙotin ƙoli."

Masu ƙorafin sun amince su kai wa gwamnan takardar da ya nema da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Alhamis.

Ko Kano na buƙatar tantance masu wa'azi?

..

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

BBC ta tunɓi wasu malamai guda biyu a birnin na Kano waɗanda duka suka nemi a sakaya sunansu saboda yanayin da ake ciki sakamakon saɓanin fahimta.

"Gaskiya tuntuni ya kamata a ce gwamnati ta yi dokar wa'azi domin tantance me ya kamata da abin da bai kamata mai wa'azi ya yi ba. Ya kamata a ce kawo yanzu akwai dokar da za ta fayyace akan wace mazhaba malaman Kano za su rinƙa koyar da mabiya. Sannan akwai buƙatar tantance irin littafan da ake karatarwa." In ji wani malami a Kano.

Sai dai kuma ɗaya malamin wanda shi ma ya buƙaci da a ɓoye sunansa ya ce yana ganin bai kamata gwamnati ta shigar da kanta harkar malamai ba.

"Ni a tawa fahimtar babu ruwan ƴansiyasa da malanta. Dalilina kuwa shi ne akwai tsoron cewa idan har ƴan gwamnati suka fara shiga harkar to lallai za su saka siyasa a tsarin ta yadda idan malami ba ya siyasar mai mulki zai zama abin hukuntawa. Amma na amince cewa malamai suna sakin baki. Suna rikita fahimtar mabiya." In ji malamin.

Abin da NSCIA ke son a yi kan masu wa'azi

A watan Fabrairun 2025 ne Majalisar Ƙoli kan harkokin Shari'ar Musulunci ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin, Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III, ta nemi a samar da dokokin da za su tantance masu wa'azi a faɗin Najeriya.

Malamai da shugabannin addinin Musulunci a Najeriya, sun ce lokaci ya yi da za a samar da dokoki da suka shafi yadda ake gudanar da wa'azi a faɗin ƙasar.

Bayan kammala taron, Sakatare Janar na Jama'atu Nasrul Islam, Farfesa Khalid Aliyu ya shaida wa BBC cewa lokaci ya yi da dole ne a saka dokokin ƙayyade wa'azi da tafsiri a Najeriya.

"Ka da a mayar da munbarin tafsiri na habaici da zage-zage da ɓatanaci da ɗauko fannonin ilimi masu girma waɗanda ya kamata a karantar da su a zaure a gaban malamai sannan kowane malami ya yi bayani gwargwadon ilimin da Allah ya bashi.

Ƙoƙarin yadda za a rage damuwar kafafen sada zumunta wurin barazanar haɗin kai tsakanin malamai da masu wa'azi, inda jama'a ke kawai yin wa'azi saboda an kafa masa kamera." In ji Farfesa Khalid.

Shi ma Sakatare na Malam Nafi'u Baba-Ahmed "wajibi ne gwamnati ta fito ta yi dokokin da za su tsara yanayin da za a yi wa'azi da tafsiri domin muna ganin yadda wasu mutanen da ke kiran kansu da malamai na fitowa su yi maganganu akan jahilci da sunan wa'azi."

Me kundin tsarin mulki ya ce?

A kwanakin baya BBC ta tuntuɓi Barista Sulaiman Magashi, wani lauya mai zaman kansa a birnin Kano kan buƙatar tantance wa'azi a kundin tsarin mulkin Najeriya.

"Abu ne mai yiwuwa kuma mai fa'ida a ɗauki matakin tsara yadda ya kamata a gudanar da wa'azi domin shi ma fanni ne na wata sana'a wadda shari'ar addinin Musulunci da tsarin ƙasar suka amince a kyautata su."

"Tsarin mulkin Najeriya ƙarƙashin sashe na huɗu na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da ƴancin gudanar da addinin da mutum yake so ciki kuma har da wa'azi wato kira ga addinin da yaɗa shi.

To sai dai kuma wannan ba yana nufin a yi wa'azin ta-ci-barkatai ba ko kuma yadda zai saɓa da tsarin zamantakewar jama'a kamar cin mutumcin wani ko kuma tayar da tarzoma. Saboda haka akwai buƙatar a yi dokokin kyautata wa'azi abu ne da ya dace a yanzu haka." In ji barista Sulaiman Magashi.

Sai dai ya bayyana buƙatar sanya masu-ruwa da tsaki a cikin al'amarin sannan a guji shigar da siyasa a al'amarin ko kuma nuna banbanci wajen umarni da hani.

Lokuta biyu da kalaman malamai suka tunzura jama'ar Kano

Yuli 2025: A watan Yulin shekarar nan ne rundunar ƴansandan Kano suka gayyaci Sheikh Lawal Triumph, bayan ƙoƙarin wasu mutane na halatta jininsa bisa zargin kalaman rashin ladabi ga Annabi Muhammad SAW, zargin da ya musanta. Rikicin ya so ya jefa jihar cikin halin farba bisa rashin tabbas na abin da rikicin ka iya janyowa jihar.

Yuli 2021: A wannan shekarar ce hankali ya tashi a jihar Kano bisa zargin kalaman tunzuri da aka yi wa Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara. Wani ɓangare na malamai a Kano ya zargi Abduljabbar da kalaman ɓatanci ga janibin Annabi Muhammad SAW zarge-zargen da malamin ya musanta, inda ya ce yana kare annabin ne. Wannan al'amari ya janyo har aka yi muƙabala sannna kuma aka kai malamin kotu inda ta yanke masa hukuncin kisa.