Me ya sa Najeriya ta gaza samun gurbi a Gasar Kofin Duniya ta 2026?

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta gaza samun gurbi a Gasar Kofin Duniya ta 2026 da za a buga a ƙasashen Amurka, Mexico da Kanada.
Najeriyar ta yi rashin nasara a hannun DR Congo a wasan cike gurbi na nahiyar Afirka da suka kara ranar Lahadi a ƙasar Moroko.
Hakan na nufin Jamhuriyyar Ɗimokuraɗiyyar Congo za ta wakilci nahiyar Afirka a wasannin cike gurbi tsakani nahiyoyi daban-daban.
Wannan sakamako bai yi wa ƴan ƙasar da dama daɗi ba, inda wasunsu suka riƙa sukar salon wasan da tawagar ke amfani da shi a lokacin manyan wasanninta.
Me ya hana Najeriyar samun gurbi?

Asalin hoton, Super Eagles/X
Kocin Najeriya Eric Chelle ya zargi tawagar DR Congo da yin tsafi, inda a cewarsa ya ga wani daga tawagar yana fesa ruwa a lokacin da ake fara bugun fenareti.
Shin wannan iƙirari nasa na iya zama gaskiya?
Salisu Musa Jegus, mai sharhi kan wasannin ƙwallon ƙafa ya ce iƙirarin kocin Najeriyar ba shi da tshe balle makama.
Masanin wasannin ya zayyano wasu dalilai da yake ganin su suka haifar wa ƙasar gaza samun gurbi, kamar haka:
- Sakaci
Salisu Jegus ya ce abu na farko da ya haifar wa Najeriya matsala shi ne sakaci
''Tun da farkon fara wasannin neman gurbin gasar Najeriya ta yi kuskure'', in ji shi.
Ya ce ya kamata Najeriya ta samu gurbi ka- tsaye ne kamar sauran manyan ƙasashen Afirka, amma ƴan wasan ba su mayar da hankali ba.
- Yawan sauya koci
Sannan Super Eagles ta kuma riƙa sauya masu horarwa, har ya kai ga cewa ta yi amfani da koci huɗu a tsawon lokacin.
''Idan ka duba shi kocin tawagar na yanzu Éric Chelle ba shi ne ya fara jan ragamar tawagar a wasannin neman gurbin ba, kafin shi wasu sun yi aka samu matsala da su aka kore su'', in ji shi.
Ya ce hakan ya taimaka wajen hana an wasan fahimtar junansu, saboda kowwane koci da zubin anwasan da ke son amfani da su.
Saƙon Tinubu ga tawagar

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yaba wa ƴan wasan bisa rawar da ya ce sun taka a wasannin neman gurbin.
Cikin wata sanar da fadarsa ta fitar, Shugaba Tinubu ya yi kira ga ƴanwasan kasar su manta rashin nasarar da suka yi a hannun DR Congo domin mayar da hankali kan gasar Kofin Ƙasashen Afirka da za a Morocco.
''Duk da cewa yana da ciwo tawagarmu ta kasa samun gurbin Gasar Kofin Duniya, karo na biyu a jere, dole ne a yaba da tawagar kan ƙoƙarin da ta yi, musamman cin wasanta na farko a wasannin cike gurbi'', in ji Shugaba Tinubu.
''Abin da ya kamace mu yanzu shi ne kara ƙaimi don tunkarar Gasar Cin Kofin Afirka, dole ne ƴan wasanmu su murmure su manta da wannan rashin nasara'', in ji sanarwar.
Me ya kamata Super Eagles ta yi?

Asalin hoton, Super Eagles/X
Salisu Jegus ya ce tun yanzu ya kamata tawagar ta fara shiri don tunkarar Gasar Kofin Duniya ta 2030.
''Ka ga jiya aka fitar da tawagar, to yau ya kamata ta faran shirin Gasar 2030'', in ji shi.
Ɗanjaridar mai sharhin wasanni ya kuma ce yana da kyau Hukumar Ƙwallon Ƙafar Najeriya ta ɗauki matakin inganta gasanninta na cikin gida.
Ya ƙara da cewa yana da kyau a nemo kamfanoni masu kyau da za su buɗe makarantun horas da yara a faɗin ƙasar domin samar da sabbin ƴan wasa.
''Hakan zai yi tasiri ne kawai idan har babu cin hanci da rashawa da kuma ƙaryar shekaru'', in ji shi.











